← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 80

Sashe 63

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidan Najib a Badawa Layout yake, suka dunguma sai gidan Najib. Naja'at tayi mamakin ganin Iman murna ta kamata suka rungume juna. Daga karshe Naja'at ta damu har taso a gane damuwarta da taji labarin Iman zata auri Hamma Huzaifa tana tausayawa dan Uwanta Suhaif tana tunanin halin da zai shiga. An jera musu abinci kala-kala sunci sun sha sun koshi. Bayan sunyi sallar la'asar sai Suhaif yayi musu sallama ya ce zai tafi Doko yanzu haka yana yi musu fatan alheri sai ya zo Jalingo daurin aure kenan. Najib, Naja'at Huzaifa da Iman suka raka shi har bakin mota ya shiga shi kadai zai tafi ba tare da direba ba. Ko kadan baya garajen duban gefen da Iman take ita kuwa babu abunda take sai satar kallonsa, ko tantama babu tana so tayi masa magana amma babu dama dan haka maganar da tayi masa ta karshe shine ya gaishe mata da Goggo, Baba, Hajja da *yar Hajja. Ta ce ya cewa Goggo dan Allah ko kowa bazai zo bikinta ba ita ta zo. Suhaif ya amsa mata da "To zan fada musu yaja mota ya tafi yayin da hawaye ya zubo a idanuwansa, Iman ma haka amma sai tayi sauri ta shige gida.
Misalin karfe biyar na yamma Najib da Huzaifa suka shirya fita gidajen *yan uwa da abokan Huzaifa. Iman da Naja'at suma suka ce zasu je NNDC quater sharada gidan Zubaida su kai mata nata katin. Don haka gidan ma rufeshi aka yi tunda babu kowa. Najib da Huzaifa a motar Suhaif wacce suka zo da ita suka fita. Naja'at, Zainab da Iman da yara su kuma suka fita a ta Najib tunda tafi girma. Naja'at ke tukawa suka nufi Sharada.
Sun iske Zubaida itama shigowarta kenan ko fitowa daga mota bata yi ba, daga gidansu take Hadeja Road. Daman tana da labarin Iman ta zo. Ta tare su da sauri cike da mamakin ganin Iman. Itama Iman tayi mamakin ganin Zubaida saboda yadda tayi uwar kiba haka. Iman ta rungumeta suka gaisa ta ce "Zubaida me kike ci kika yi kiba, nima in ci, ina mamakin kibar Naja'at ashe ita ba kiba tayi ba akan ki. Zubaida ta kyalkyale da dariya ta ce "Ke dai kina nan yadda kike Iman dama ni ce, kamar kara dawowa yarinya kika yi, kin zama *yar siririya kin dada fari da kyau, kiyi zamanki a haka ni ai bana son kiba. Oh! Iman sai naga katin aurenki da Hamma Huzaifa ya aka yi? Naja'at ta ce "To uwar tambaya ai sai ki kaimu cikin gidan mu zauna sai ayi labarin, ga bakuwa da yaranta suna tsaye. Sannan Zubaida ta ce "Lah ashe da wata ban kula ba, wannan balarabiyar fa? Iman ta ce "Matar Hamma Huzaifa ce da yaransa. Zubaida ta gaisheta da turanci, Iman ta ce "Ai bata jin kowanne yare sai larabci, *ya*yanta ne suke jin fulatanci da turanci. Iman ta fassarawa Zainab abun da Zubaida take cewa wato sannu da zuwa. Zainab tayi murmushi ta mikawa Zubaida hannu suka gaisa. Zubaida tayi gaba suna biye da ita har cikin gida tana cewa "Ku shigo ku zauna, ashe yau akwai labari kala-kala. Ga Iman ga Hamma Huzaifa sannan ga matarsa balarabiya, ga kuma Yayana Suhaif wai ya za muyi? Naja'at ta ce "Ai kuwa baza ki sha labarin komai ba dan kuwa Iman bata iya surutu ba. Katin biki kawai zamu baki mu tafi a gidana suka sauka.

Suhaif da Iyayensa zaune suke a dandasheshen gidan da Suhaif yasa aka rushe gidansu na da aka mayar dashi na zamani. Ya zuba musu kaya na alfarma na zamani, idan ka shiga gidan baza ka taba zata a Doko kake ba, sai ka fito kofar gida. Goggo ta dube shi taga a hautsine yake kamar wani abu yana damunsa. Ta ce "Baban gida kamar kasha wuya a Umarar nan, naga ka rame duka ka hautsine kamar ba kai ba. Shi yasa na ce ka bari muje da Azumi, kace ta Mauludi tafi rashin cikowa. Mahaifinsa ya ce "Da gaske ne ai ta Maulud tafi rashin jama'a. Wane irin wuya zai sha kamar wani wanda ya je babu guzuri? Goggo ta ce "Allah ganinsa nayi kamar ba shi ba.
Suhaif yayi ajiyar zuciya ya ce "Babu wata wuya da muka sha kawai dai yanayin rayuwar ce haka.
Suka dauki lokaci mai tsawo suna hira sai Suhaif ya bude wata *yar jaka a kusa dashi ya zaro katina guda biyu ya mikawa Baba daya, Goggo daya. Baba ya iya karatun Hausa, Goggo kuwa babu ko ABCD ta jujjuya katin ta ce "Shegantaka zaka yi mun, ka fada min da baki ko katin meye. Ko auren aka dauro daga Makka bamu sani ba, ka samu wata ne? Suhaif yayi murmushi ya ce "Baba ya karanto da karfi kiji. Baba ya ce "Daurin auren Huzaifa Ahmad Jalingo da Fatima Lamin Jalingo. Su duka suka hada baki "Wacece Fatima? Suhaif ya yi ajiyar zuciya ya ce "Katin daurin auren Hamma Huzaifa da Iman ne. Sai Goggo ta dau salati mai hade da kuka kamar an fada mata mutuwa. Baba ya cabki kunnan Suhaif yana ja yana fada cewa yake "Shin na fada maka ko ban fada maka ba? Na ce ka hakura ka auri wata, ko ban fada ba? Daman banda hauka a ina ka taba jiran mutumin da baisan ana jiransa ba. Nan sai suka dinga yiwa Suhaif nasihohi kala-kala cewar kada ya sake ya ce zai tsangwami kansa ya shiga damuwa, ya dauka haka shine yafi alkhairi, ya nemi wata ya aura. Shi kuma ya rokesu su yiwa Allah suyi masa alfarma su shirya aje bikin nan dasu saboda Iman ta zama *yar gida. Goggo bata musa ba, ta ce zata je harma da *yar gudunmawarta, Iman ai *yarta ce. Baba ne yake dujewa da kyar Suhaif ya lallasheshi gami da yi masa alkawari da zarar sun je bikin Iman sun dawo a watan shima zasu ji nasa auran. Yayi musu alkawari ya yadda da kaddara zai nemi wata ya aura. Sunji dadi sosai sun yi masa addu'a Allah Ya yi masa albarka ya musanya masa da ta gari. Suhaif ya dauki jakar kayansa ya nufi dakinsa hawaye ne ke zuba sharr-sharr daga idanuwansa. Ya kwanta yana tunani haka kuma yake kuka, saboda ya kasa bacci ya kasa daina son Iman har yanzu. Sai ya tashi cikin dare ya yi ta sallah, ya yi azumi ya roki Allah Ya kawo masa karshen damuwar nan da ta haddasu a zuciyarsa ta Iman shekara da shekaru.
Washe gari Iman, Huzaifa matarsa da *ya*yansa suka shirya suka fito dan kama hanyar tafiya Yola. Najib da matarsa Naja'at suka musu rakiya har filin jirgi. Najib ne ya biya musu kudin tikitinsu duka, Huzaifa yayi-yayi ya bari ya biya ko rabi ne. Najib yaki ya ce shima bashi ya biya ba, tun jiya Suhaif ya bashi ya ce ya biya musu. Suka yi ta godiya suka shiga jirgi suka tafi, sannan Naja'at da Najib suka dawo gidansu.

Ana jibi daurin auren Iman da Hamma Huzaifa. Suhaif ya yi waya Abuja aka kawo masa wasu sababbin motocinsa fil-fil a ledarsu guda uku da ya shigo dasu daga GERMANY. Motocin duka ukun irinsu daya, kalar fentinsu daya bakake kirar zamani wadanda ake yayinsu a lokacin. Ana gobe daurin aure kuma da sassafe suka shirya a daura dasu. Idan da wuri aka daura su juyo a ranar idan kuma an samu African time su sake kwana. *Yan Doko sun hallara a Kano gidan Baba na Kano, Najib da Naja'at sun iso da sassafe sai Zubaida da mijinta Muslim da *yan tagwayenta da mai renonsu Lantana suma sun iso akan lokaci. Ana shirya yadda za'ayi tafiyar, wannan ya ce a shiga babbar mota daya tafi, wancan ya ce araba a shiga kananan motoci a jeru a tafi da direbobi. Suhaif ya ce dalilin da yasa ya aika Abuja aka kawo masa sababbin motocin nan iri daya guda uku, sai dan su tafi dasu zai fi tsari, kuma suna da saurin tafiya, gasu da tudu dan haka nisan nan bazaisa su gajiba. Yana so idan sun tashi dawowa suje filin jirgin Yola su dawo ta jirgi. Babansu ya ce "Ban gane muje a mota ba mu dawo a jirgi waye zai dawo da motocin, direbobin? Idan haka ne mu tafi a jirgi mana. Suhaif ya ce "A'a so nake in bawa amarya kyautar daya, angon ma kyautar daya sai in tuko dayar in dawo ni da wanda baya son hawan jirgi. Baba na Doko ya zabura ya ce "A'a Suhaif har kyautar motoci biyu zaka yi? Haba-haba sunyi yawa irin wadannan motoci masu tsada galla-galla dasu a ledarsu. Baba na Kano ya dakatar da Baba na Doko ya ce "Kyaleshi karka hanashi alheri. Suhaif mai kyauta ne, kuma duk wanda harkarsa ta taso Suhaif yana yi. Da dai ace bai wadata gida bane zai wadata na dawa shine zamu hanashi, ai abun farin cikinmu ne har muka samu yayi hakuri ya dangana, har zai halacci wajen bikin har ma ya dauko kyauta ya basu yayi musu fatan alkhairi. Suhaif hakan da kayi yayi, Allah Ya saka da alkhairi kaci gaba da hakuri da dangana Allah Zai saka maka da alkahirin sa.

Mota daya Muslim ne yake tukawa, Zubaida agaba. Kujerun baya kuwa mai aikin Zubaida ce da *yan tagwayenta. Daya motar kuwa Najib ne yake tukawa, Naja'at a gaba, Mama da Goggo a baya. Sai daya motar Suhaif yake tukawa Baba na Kano a gaba, baya kuma Baba na Doko shi kadai. Suka yi addu'o'i sannan suka kama hanya. A jere suke tafiya, suka nufi garin Jalingo. Jalingo Ja garin Baba, shiga da kaya ka fito da gammo. Inji masu kirari.

Nima sai na dana kirarinmu.
KANO TA DABO TUMBIN GIWA KO DAME KAZO MUN FIKA
Ko da musu ne????????????????

Reedwan Suraj Isma'il

>>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Chapter 63 · 0% Book details