Sashe 2
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 9 min read
Reedwan Suraj Isma'il
YARENA ADDININA
CI GABAN LABARIN
Suhaif na isa gida ya iske mahaifinsa Alh. Hayatu suna kofar gida a zaune shida wani bako yazo neman na cefane. Bayan ya gaishe su sai ya sami waje ya zauna a gefensu. Baba yace da Suhaif ya shiga ya aunowa wannan bawan Allah gero kwano uku Suhaif ya je ya auno ya kawo. Mahaifinsa ya hadawa mutumin da kudi dari biyu ya bashi, Mutumin yana ta godiya ya dauka ya tafi. Alh. Hayatu ya dubi Suhaif ya ce "Yaya na ganka duk kayi sanyi kalau kamar marar lafiya? Suhaif yayi murmushi ya ce "Lafiyata kalau Baba, sai dai ina tausayin yadda nan gaba talakawa zasu ci gaba da rayuwa a kasar nan. Yanzu Allah ne kadai Yasan yawan magidantan da suke cikin halin rashi ga iyali da yawa haka suke kwana da yunwa sabo da babu, sun buga ko ina basu samowa iyali komai ba, su kuma ba musakai ba ballantana suyi bara. Taimakon irin wadannan yana lada tunda baza su iya yawon bara ba, su kuwa musakai zasu iya bara a basu.
Alh. Hayat ya girgiza kai don tausayi ya ce "Hakane Suhaif, kasar nan sai addu'a, talaka yana wahala Allah Ya canja mana wannan rayuwa. Suhaif ya ce "Amin Baba, amma kaga da za'a sami iri-irinka, masu hali su dinga taimakawa marasa hali da kan musulmai ya hadu, sun so junansu musulmai, da masu yin bara sun rage bara. Abu ne mai wahala kaga wanda wanda ba Musulmi ba yana bara duk yawancin masu bara Hausawa ne kuma Musulmi kaga bama kishin YARENMU DA ADDINIMU. Amma sai kaga mai kudi ya tara abincin da zai iya ciyar da iyalinsa har tsawon shekaru, makwabcinsa kuwa bashi da ko kwayar shinkafa. Alh. Hayat ya yi murmushi ya ce rufin asiri dai Alhamdulillahi tunda duk shekara ina samun amfanin gona wanda zai isheni in ciyar da iyalina har wata shekarar, amma nima wataran na cefane sai mun harhada da mahaifiyarka da kai kanka dan abinda ka samo a Kano. Daman mutum ba zai ga Allah yayi masa wata baiwa ba sai ya dubi wanda yafi, amma muddin yana duban na sama dashi wanda suka fishi ba zai godewa Allah ba. Yanzu me yasa na dage na hakikance na ce sai kayi digiri? Duk garin nan waye ya taba wani karatu me zurfi kamarka? Ai dan a sami ilimi a garin wanda wataran in Allah Yasa ka zama wani kusa a gwamnati ka tuna da *yan garinku ka zo ka taimakemu. Dan haka abunda nake so da kai shine kaga ka gama karatunka na digiri kuma ka fito da sakamako mai kyau (First class). Bautar kasa ya rage muku kuje kuyi shikenan ka samu aiki ka fara. Duk garin da aka kai ka bautar kasa kaje babu komai dan ina jiyo ka rannan kana hira da dan uwanka Najib kana cewa idan ba Kaduna ba ko Kano aka kai ka babu in da zaka je kai baza kaje Kudu ba. Suhaif yayi murmushi ya ce "Baba ba kudun ne bana so ba, saboda bana so in shiga cikin mutanen da Yarena, addinina ya bambanta da nasu, kaga ko a B.U.K bana zama dasu a daki daya saboda bana sonsu suma basa son Bahaushe Musulmi. Baba kawai ka taya ni da addu'a Allah Yasa a kaini arewa. Alh. Hayatu ya ce "Zan taya ka da addu'a amma fa kai ka fada mun cewar *yan Kudu arewa ake turosu, *yan arewa kuma a kai su kudu sai dai idan mutum yayi sa'a. Ni dai ina baka shawara karka dauki wannan sanadiyyar raunana karatunka kace baza ka je bautar kasa ba dan an tura ka kudu. Ina da kyakkyawan zato a kanka Suhaif ka rike karatunka ka nemi aiki ka taimaki al'ummar garin nan, naga kana son taimako kana kishin Yarenka da Addininka.
Suhaif ya gyara zama ya ce "Baba ai barewa ba zata yi gudu danta yayi rarrafe ba, abunda duk kaga ina yi a wajenka nake koyi kamar son taimakawa mabukata da kishin YARE da ADDINI. Alh, Hayat yayi dariya ya ce "Ai shi yasa ake son iyaye su zamana masu kyakkyawar dabi'a don duk abinda suke yi shi *ya*yansu suke kwaikwaya, Allah yayi maka albarka ya taimakemu baki daya. Suhaif ya ce "Amin Baba, yanzu ma daga gidan Hajja nake naje gaisheta. To ina fitowa kofar gidan sai naga *yar Hajja da kwayenta a kofar gida suna sayar da goro da kwai. Suka nuna min wata yarinya bakuwa ce bata san kowa a garin nan ba tana kuka tana neman taimako bata san inda zata je bama. Da nayi mata tambayoyi sai ta ce ita marainiya ce bata da uwa bata da uba ita kadai kuma suka haifa. Danginta kakaf bata sansu ba Nigeria ma bata taba zuwa ba, a Makka aka haifeta shine aka kamota don bata da takardar zaman kasar ba tare da tasan inda zata je ba. Baba idan kaga yarinyar sai kayi mata kuka abun tausayi, shine na kaita gidan Hajja na ce su bata abinci ta kwana gobe inji shawarar da zaku yanke. Alh. Hayat yai shiru can ya ce "Suhaif waye ya ce maka ana irin wannan gangancin? Da daddaren nan ka tsinci yarinya ka dauke ta ka kaita gidan tsohuwa kace ta kwana, ba ka kaita gidan me gari ba shima idan yaga bazai iya riketa ba a kaita wajen hukuma su riketa. Bakasan duniya ta lalace ba, ka taimaki mutum shi kuma ya cuceka. Yanzu idan ka bibiya ma yarinyar karya take yi. Ko aure aka yi mata bata san mijin ta gudo. Suhaif ya ce "Baba ba haka bane duk wannan tambayoyin Hajja tayi mata nima nayi mata ta rantse ba auren dole aka yi mata ba. Kuma yarinyar kintsattsiyar yarinya ce Baba, ko daga maganarta zaka san yaran Hausa bai ishetaba, Baba Musulma ce tana neman taimako mu taimaketa mana. Yanzu idan muka kyaleta tayi gaba zata iya fadawa wani hannu a cuceta a matsayinta na mace budurwa akwai hatsari. Daga jin Hausarta zaka san ba girman nan ba ce. Alh. Hayat yayi shiru can ya nisa ya ce "Suhaif tunda kace haka na amince kaje ka taho da yarinyar nan gidan yanzu, don ba za'a bar tsohuwa ta kwana da wacce ba'a san asalinta ba, duniyar nan a bar tsoro ce. Ni kuma zan shiga gida in sanarwa Mahaifiyarka da kannanka kafin ku karaso.
Suhaif har zaiyi magana ya ce a bari sai gobe, sai yayi shiru ya amsawa mahaifinsa da "To madalla Allah Ya kara arziki da wadata. Ya tashi ya nufi gidan kakarsa, Babansa kuma ya shiga cikin gida.
Suhaif yayi sallama a gidan Hajja ya tarar da Iman ta gama cin tuwo tana wanke hannu, Hajja kuwa tana kishingide akan shinfidarta. Tana jin muryar Suhaif sai tayi zunbur ta tashi zaune ta ce "Muryar wa nake ji kamar Babangida, daman baka tafi ba ko dawowa kayi baka gama tsokanar daka saba bane? Suhaif yayi dariya yazo ya zauna a kusa da ita ya fara koro mata bayanai kamar yadda suka yi da Babansa a hankali suke maganar ba tare da sun bari Iman taji ba. "Zancen banza yarinya mai hankali da nutsuwa har na fara jin dadin zama da ita shine kake so ka dauke mun ita? Gata wayayyiya tafi *yar Hajja wayo ko talla suka je ba zata ajiye kayan tallar ba ta hau wasa da kawaye kamar yadda *yar Hajja take yimin. Suhaif ya kwashe da dariya ya ce "Ai ba'a yayin dorawa *yan mata talla yanzu Hajja, yayin karatun boko ake yi. Kinga Iman bata yi kama da *yan talla ba da mai ilimi take kama. Anyi-anyi kibar dorawa *yar hajja talla kinki, taci makarantar kwana anan Garki babu nisa kinki yarda a kaita ai lokaci zan samu inzo in sace ta in kaita makarantar dole ta zauna tayi karatu. Takaici ya hana Hajja yin magana saita gyara filo ta kwanta. Suhaif ya juya dubi ya dubi Iman wacce ta takure a gefe kan tabarmar da tayi sallah tana jan carbinta yayi murmushi ya ce "Iman ki dauko kayanki kizo mu tafi can giddanmu su Baba suna so su ganki ku gaisa. "Bata kara ko sakon daya ba ta tashi cikin ladabi gami da amsa masa ta nufi dakin da ta ajiye jakar kayanta ta fito. Suhaif ya mike tsaye yana yiwa Kakarsa sallama, kamar yadda ya sani daman baza ta amsa ba saboda tana jin haushin dauke Iman kuma yayi mata maganar makarantar *yar Hajja wacce da zarar yayi mata in ranta yayi dubu sai ya baci. Iman ma tazo ta durkusa a gaban Hajja tayi mata sallama gami da yin godiya, Hajja ta amsa dakyar. Suhaif fuskarsa cike da murmushi ya shige gaba Iman na biye da shi suka fice. Sun danyi nisa Suhaif ya juya ya kalli Iman ya ce "Af kawo jakar kayan in taya ki rikewa. Ta sunkuyar da kai kasa ta ce "Ka barshi nagode zan rike babu komai. Suhaif ya sake mika hannu ya ce ta bashi ya rike mata. Sannan ta mika masa jakar suka ci gaba da tafiya.
Suna isa gidan a tsakar gida suka iske Baban Suhaif da Babarsa. Bayan sunyi sallama sun amsa musu sai suka shigo Suhaif ya dubi Babansa ya ce "Ga Iman din na taho da ita. Iman tazo ta durkusa a gabansu ta gaishesu suka amsa dukkansu. Mahaifiyar Suhaif ta ce da Iman ta dawo gefen tabarma tazo ta zauna. Iman tayi godiya cikin ladabi ta zo ta zauna a kusa da mahaifiyar Suhaif. Suhaif ma ya sami waje ya zauna. Alh. Hayat yayi gyaran murya ya dubi Iman ya ce "Yarinta ki fada mana gaskiyar dalilin da yasa kika bar garinku, karki boye mana idan kina so ki zauna damu anan baza mu kore ki ba sai mu zauna tare. Kuka ne amsar tambayar da yayi mata, tayi kuka har ta godewa Allah, su duka lallashinta suke yi, dakyar ta tsagaita da kukan. Cikin shesshekar kuka ta ce "Duk abunda na fadawa Suhaif shine gaskiyata ban boye muku ba, ina neman alfarma ku yi min sutura ku taimake ni in zauna daku babu inda na sani, babu wanda na sani. Tausayinta ya rufe su Goggo mahaifiyar Suhaif har hawaye take yi ta ce "Iman yi shiru daina kuka zamu rike ki tamkar *yarmu ta cikinmu. Goggo ta kwallawa Naja'atu da Zubaida kira suka fito daga dakinsu suka zo suka sami waje suka zauna. Alh. Hayat ya shaida musu ga *yar uwa kuma kawa tazo zata zauna dasu, ya shaida musu marainiya ce tana neman taimako don haka kada su wareta su riketa tamkar *yar uwarsu jinin su domin haramun ne cusgunawa maraya. Sun dauki alkawarin cewa zasu zauna da Iman lafiya tamkar *yar uwarsu. Daga karshe Goggo ta ce su dauki jakar kayanta su tafi da ita dakinsu suyi mata shimfida kusa da shimfidarsu. Farin ciki mara misaltuwa ya rufe Iman ta sake durkusawa ta yiwa su Alh. Hayat godiya. Naja'atu ce ta dauki jakar kayan Iman na biye dasu har cikin daki suka yi mata shimfida ta kwanta. Daga karshe Suhaif ya yiwa Mahaifansa sai da safe ya tashi ya nufi shagonsa dake zauren kofar gidan. Bayan Alh. Hayat da Goggo sun taba hira suma suka shiga dakinsu suka kwana.