Sashe 40
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
RANAR SALLAH !!!
Ranar da muka kwana goma, ranar ne ake sauke azumi, ranar ne kuma ranar Sallah. Bayan Sallar Idi sai naga matan da muke tare suna harhada kayansu suna shirin tafiya. Na tambayi Maman Amina ina zasu tafi naga suna hada kaya? Sai ta sanar mun ai yau kowa zai tafi gidansa tunda azumi ya kare. Gabana ya fadi, hankalina ya tashi bani da inda zan nufa, sai jikina yayi sanyi. Maman Amina ta lura da halin da na shiga yanzun nan, sai ta fara mun tambayoyi taji ra'ayina. Ta ce min "Yau nima zan je gidan Iyayena ayi bikin sallah dani sai sati na sama in koma Jalingo. Ke fa Fatima wacce unguwa zaki tafi ne? Hawaye mai yawa ya zubo nace bani da kowa, ban san Kano ba, ban taba zuwa ba bani da dangin uwa babu na uba. Sai na rushe da kuka na fada kan cinyarta ina cewa "Maman Amina ki taimakeni.
Hankalinta ya tashi, tana lallashina idonta ya cika da kwalla ta ce min, "Fatima yi shiru kada jama'a su taru kinga sun fara tambayata meya sameki zan taimakeki kamar *yar cikina, Fatima Allah ne Ya hadamu. Naji dadin maganarta sai hankalina ya fara kwanciya ta share mun hawaye ta ce "Zaki yarda ki bini gidanmu na nan Kano idan sati ya zagayo zan koma Jalingo mu tafi tare, ki zauna tare da ni da marayun *ya*yana su Amina? Nan fa daya ai bani ba komawa Jalingo, nayi shiru. Can naji ta sake ce wa "Zabi zan baki, ko kuwa kinfi son in nemar miki gidan aiki anan garin? Nayi sauri na ce "Eh ki samar min gidan aiki anan garin saboda inason garin akwai addini. Tayi murmushi ta ce "Jalingo ma akwai Musulunci sai dai kice akwai yare daban-daban da wasu addinai, ba kamar Kano ba Hausawa ne kuma Musulmai ne dukkansu. Mu duka mu kayi dariya. Wadanda muka saba suna ta zuwa inda muke muna zaune acikin Masallaci suna yi mana sallama, muna musu fatan alheri da fatan Allah Ya hadamu a wata shekarar.
Muma muka tashi muka hada kayanmu Maman Amina tayiwa *yan tawagar da muka taho tare sallama cewar ita ta tafi cikin gari sai wani satin zata je Jalingo su kuwa yau zasu koma Jalingo nima nayi musu sallama muka fito. Bana barin Maman Amina ta dauki tsinke idan muna tare dan haka da jakar kayana dana kayanta na dauka muka fito get din makarantar BUK. Naga ta tsayar da tasi ta ce masa TUKUR ROAD zai kaimu. Su kayi ciniki muka shiga. Muna tafiya a hanya take sanar dani zata kaini gidan aiki ne da farko sannan ta dawo cikin gari kusa da gidan Sarkin Kano nan ne unguwar gidan Iyayenta. Ta ci gaba da yi mun bayani, ta ce gidan da zata kaini bama Hausawa bane balle ayi gutsiri tsoma da kananan maganganu. Larabawa ne, larabawan Egypt. Mace da Mijinta sai dansu guda daya. In har zan zage in yi musu aiki ba ha'inci in kular musu da dan karamin yaronsu to lallai zasu rikeni tamkar *yarsu, zanji dadi in huta, gida ne tamkar aljannar duniya. Kamar yadda ta karanci halina dan zaman da muka yi tasan babu matsala halina yana da kyau zamu dai-daita, don haka ne ma taga ya dace ta kaini can. Tana bani labarin yadda suka saba da balarabiyar, Baban Maman Amina ne ya taba yi musu aikin gadi, waccan shekarar baban ya rasu. Dan haka *yan gidansu kakaf sun saba, kuma har yau har gobe kusan su suke ciyar da gidansu Maman Amina. Kayan abinci buhu-buhu suke kaiwa gidansu, kudin cefane, kwancen kayansu na sawa da zakka. Shi yasa itama duk sanda tazo garin alkawari ne tazo ta gaishesu, duk sanda taje sai taji Balarabiyar tana jajen *yar aiki bata jin dadin yadda basa iya kula da danta. Danta guda daya, ga kuma yadda take ji dashi, shekaru goma da aure sai yanzu suka samu haihuwa.
Na tambayi Maman Amina sun kauro Nigeria kenan baza su koma kasarsu ba? Ta ce mun zaiyi wuya su koma gaba daya suna dadewa ma basu je ganin gida ba. Duk harkar samun kudinsu da kasuwancin su suna nan Kano. Mijin dan kasuwa ne, matar ma ta bubbude super market da Nursiry ana karatu. Dai-dai lokacin Maman Amina ta cewa mai tasi "Nan zamu sauka. Na bude baki ina kallon kerarren gidan da ban taba arangama da irinsa ba a ido biyu. Ta biya shi kudinsa muka dunguma kofar gidan, kafin mai gadi ya bude get sai da ya liko ta windo ransa a bace zaiyi mana wulakanci ko da yaga Maman Amina ya ganeta sai ya washe baki ya ce "Sannunku da zuwa" da sauri ya wangale get muka shiga riki-riki da jakunkuna a hannuna. Muka tsaya suka gaisa da buzun mai gadin sannan muka wuce cikin gidan bayan mun keto ta lambuna da swimming pool ga ruwa yana bulbulowa ta cikin wasu duwatsu suna bawa grass carper ruwa da fulawowi. Abun tamkar a film ba a ido biyu ba. A Nigeria dai ban taba ganin irin ginin nan ba, sai dai a waje lokacin da muka je da Iyayena.
Mun iske balarabiyar matar a katafaren falonta na alfarma tana kallon talabijin tashar Makka ce ana sallar azahar, ta burgeni matuka ganinta sanye da hijabi tana jan carbi a hannunta. Ta amsa sallamarmu, sai ta taso da fara'a da sauri ta tari Maman Amina gami da rungumeta ta sunbaci kumatunta, ina gefe ina kallon sabon salon gaisuwar da ban taba gani ba ina kuma sauraron yaren da ban taba jiba a sarari wato da larabci suke magana. Ban san me suke cewa ba naga Maman Amina tana magana tana nuna ni da alama dai gabatar dani take. Sai naga sun tuntsire da dariya dukkansu, Maman Amina ta juyo inda nake tsugunne ta ce mun "Na mata bayani ta ce kamar kuwa nasan tana tsakiyar neman mai raino. Ta ce kinyi mata dari bisa dari, kinga ko bata nan danta zai ganki kamar ita saboda kema kinyi kama dasu Larabawa, wai kamarku daya anya ke ba balarabiya ba ce? Sai nima nayi dariya, suna Magana Maman Amina tana fassara mun. Matar ta zano dokokin gidan, da abun da zanyi da wanda zan kiyaye. Tana ta maimaita mun in kular mata danta sosai shine burinta. Sannan nawa zata dinga biyana a wata? Nayi caraf na ce "Bana bukatar ko kwabo fata na su rikeni amana kuma su sani a makarantar Islamiyya har in sauke alkur'ani shine burina.
Da Maman Amina ta fada mata abinda nace sai ta bude baki tana mamaki. Tace in matso kusa da ita ta mikamin hannu muka gaisa tana larabci tana shafamun kai, Maman Amina na fassara mun abunda take cewa, bata taba ganin yarinya mai hankali wacce ta rike maraicinta ba irina, nayi tunani mai kyau kudi bai kai ilimi muhimmanci ba. Tayi alkawari zata kaini Makarantar Islamiyyar da take yi, ta *yan kasar su ce larabawa ne ziryan a makarantar. Da yamma ake zuwa Makarantar kullum banda alhamis da juma'a ranar asabar da lahadi ayi da safe. Akwai ajujuwan yara, manya tsofaffi, maza da mata, ana biyan kudi da yawa saboda kwararrun Malamai, tayi alkawari zata biya mun har in sauke kur'ani. Naji dadi sosai nayi ta godiya sai ta fada min sunanta Naila, sunan mijinta Abdul-Samad danta kuwa Abdul-Malik. Ta tambayeni sunana na ce mata sunana Fatima, sai ta rike kai ta ce babban suna ne a wajenta ba zata iya kiran sunan ba. Sunan Mahaifiyarta ne kuma sunan uwar mijinta ne zata dinga kirana da IMAN to daga nan na samo asalin suna Iman.
Anan gidan na zauna tare da Mummy Naila zaman jin dadi da kwanciyar hankali. Idan kuka ga dakina a gidan tamkar dakin *yar shugaban kasa da ban dakina a ciki. Na saba da danta Abdul-Malik shima ya saba dani har yakan ki zuwa wajen Mahaifiyarsa da Mahaifinsa sai ni kawai. Aikina shi ne kula da Abdul-Malik kawai dan haka na zage ba rana ba dare ina kula da shi matuka ko Mahaifiyarsa sai haka. Shekarunsa biyu kacal a lokacin amma dakinsa daban shima an zuba masa kayan wasan yara kala-kala ba ya iya rabuwa dani, ko Mahaifiyarsa ta ce in kai shi dakinsa ya kwanta to fa da tsakar dare zan tashi in je in dauko shi dakina mu kwana tare ko ni in kwanta a dakinsa. Na kan rungumeshi inyi kuka idan na tuna da dan Jaririna. Haka idan ina masa wanka ko shirya shi, ko ina masa wasa sai dan Harriet ya fado min ina tunanin halin da yake ciki yanzu, inji dama ace shine Abdul-Malik muke tare haka cikin jin dadi, wadata da kulawa mai yawa.
Kamar yadda na cika mata alkawari da na dauka na kula da danta, itama ta cika min alkawari ta saka ni a makaranta mai dunbin kwararrun Malamai. A kaimu a mota a dauko mu a mota duk ranar da baza ta samu damar zuwa ba ni da Abdul-Malik ake kaiwa direba ya jira har a tashe mu. An bude ajin kananan yara kamar *yan shekara biyu zuwa hudu anan ajin aka saka Abdul-Malik shima, tun yana kuka ina lallashinsa har ya saba. Ina jin dadin rayuwata sosai amma Mummy Naila ta fini jin dadi, bata da fargabar bar mun danta ko ina zata je. Tana matukar sona da kula dani, babu abunda na rasa, babu wani abu ko wani daki da tayimun katangar shigarsa, komai nake so zanci, ko ina zan shiga a gidan. Ta yarda da gaskiyata. A kwai kuku mai dafa abinci akwai Liliyan me share-share da goge-goge, a kawai Lantana mai wanke-wanke. Isa mai yanke fulawa. Isyaku da Kasim masu wanki da guga, ga masu gadi da masu sharar farfajiyar gidan ba adadi. Dukkansu girma suke bani, rissina mun suke suna kirana da Madam nima, dan su a tinaninsu jinin masu gidance banyi musu kama da *yar aiki ba. Na kara yin fari kal, nayi kiba, nayi fes na samu gyara ga sutura kala-kala, duk da ma nayi kwalliyar zurmikeken hijab nake sawa.