← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 80

Sashe 19

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tace "An kaini wajen bautarsu anyi min addu'o'i, cikin lallami shugabansu yayi min nasiha ya cusa mun ra'ayin son addininsu shine addinin gaskiya. Sai kaina ya sake cunkushewa na sake dabarbarcewa tunanina ya hautsine na kasa tantance addinin gaskiya.
Haka kuwa akayi mahaifiyata ta samo min makarantar da ake koyar da addininsu dake Enugu. Raina baya son kudu nasha kuka Mahaifina bai so ba amma Mahaifiyata ta ce saina je. Hamma Huzaifa ma yasha bacin rai, kawayena Mumuyawa sunsha kuka zamu rabu haka aka kaini garin Enugu.
Nasha bakar wuya a makarantar saboda yadda nake jayayya da Malamai a duk sanda aka zo darasi akan addininsu, ana fara wa'azi duk sanda suka fadi wani abu sabanin yadda Hamma Huzaifa ya fadamun saina tashi na karyata Malamin a aji. Ince Malam ba haka bane baka fada dai-dai ba, Allah baShi da uwa baShi da uba baShi da da ko jika. Sai suyi ta mamakina tun suna bani amsa a hankali suna kawomin hujjoji daga littafinsu amma bana dandara ko gobe Malami yazo aji ya fadi wani abu sabanin abunda Hamma Huzaifa ya fadamun zan tashi in karyata shi. To sai suka shiga dukana kamar Allah ne ya aikosu har da farfasamun jiki. Dalibai ma suka tsane ni. Seniors su kayi ta dukana suna zagina a hostel wai daman banyi kama da su ba watakila ni ba bafillatana bace dama balarabiya ce nazo in yada addinin Musulunci. Takai ta kawo duk an tsane ni duk da haka ban canja ra'ayina ba sai dai idan ba'a shiga ajinmu ba an fadi wata kalmar da bata yimin ba akan addini sai na musa. Malamai suka ga zasu kasheni saboda duka kuma baisa na daina ba, sai aka kaini kara wajen shugaban makaranta aka zauna meeting. Aka kirani ofishin suka zagayeni dukkansu tambayar da suka yi min shine "meye addinina? Na ce musu ban sani ba. Suka sake tambayata meye yarena? Nan ma bansan yarena ba, na dinga zano musu yare kala-kala da nake ji. Suka bugawa Mamana waya aka shaida mata tazo ta dauki *yarta don wannan makarantar koyar addininsu ce, *yar kuma ba irin addinin take ba Musulma ce. Mummyna ta fashe da kuka don takaici tace ba Musulma ba ce. Suka ce sun tambayeni yarena shima nace ban sani ba na zano musu yare iri-iri sufa sun kasa gane wannan wanne irin abu ne? Ta ba su hakuri ta ce kuma za ta zo karshen sati. Mummy ta zo makarantar ta ba wa Malamai da shugaban makarantar hakuri ta yi musu bayanin cewar Mahaifina ne Musulmi yake hure mun kunne da addininsa shi ne ma ta ga gara ta kawoni makarantar koyon addininta. Ta ce ni yarinya ce mai kaifin basira dukan da suke yi mini ba zai sa in canja ra'ayina ba, amma in har za su zaunar da ni cikin hikima da dabaru su karanto min addininsu a hankali, to tabbas zan rike a zuciyata sai in sawa zuciyata son abun. Ta zayyano musu yadda zasu bini har ta ce zata dinga biyan wani kudi na musamman ga Malamin da zai dinga ware lokaci yana yi min darasi na musamman ni kadai a kan yadda zan fahimci addinin sosai wato (extra Lesson). Ta kira ni gefe cikin dabara ta dinga lallaba ni tana yimini wa'azi har naji zuciyata ta fara karkata ga addininsu.
Na tsayar da hankalina a waje daya na sa karatu a gaba na yarda da abin da suka cusa min a zuciya. Ta kai ta kawo idan aka yi jarabawa akan addinin na fi duk *yan ajin cinyewa. Mahaifiyata tana jin dadi sosai, hankalinta ya kwanta. Idan na fara zayyano mata abin da yake kwakwalwata wanda aka koyamin a makaranta na game da addininta, mamaki yana rufeta tamkar na haddace littafin a kaina sai ta yi murna.
Mun gama shekarar farko har mun shiga shekara ta biyu a makarantar. Wata rana ranar Asabar da rana a makarantarmu na fito daga hostel zan tafi hall karbar abinci, na zo wucewa ta dakin seniors sai wata daliba *yar aji shida ta kirawo ni ta ba ni wata roba ta ce in karbo mata abinci daga hall. Na durkusa na karba don girmamawa don muna matukar tsoron *yan ajin gaba damu. Musamman ni da na yi kaurin suna a makarantar sun tsane ni ana min zargin ko ma ba addinin nake yi ba, na tafi hall sai na tarar teba aka yi da miyar danyar kubewa dama ni duk ranar da aka yi teba ba na ci, sai na karbi wacce aka aiko ni na fito, na kusa karasowa dakin sai na hango ta ta bude wata katuwar lokar da ke kusa da gadonta. Lokar cike take da kayan makulashe kai ka ce katafaren kanti ake shirin budewa. Biskit kala-kala, alewa, cingam, madara, milo, corn flakes, da dai sauransu.
Senior ta kalle ni ta yi murmushi da taga ina kallon kayan lokar, na mika mata robar teba na juya zan tafi sai ta kirani na dawo. Ta dauko leda ta dinga damko biskit da alewa kala-kala tana zubawa a ledar ta cika ta taf ta mika min, na kalle ta cike da mamaki na tambaya. "Wa zan kaiwa? Sai ta yi murmushi ta ce "Na ki ne, ki je ki ci ke yarinya ce mai hankali, ga shi ba ki da kiwa. Na yi murmushi, farin ciki ya rufeni, sai na duka na yi mata godiya na fito daga dakin. Ta fito har bakin kofar dakin tana dagamin hannu, ni ma ina daga mata. Duk waigowar da zan yi sai na ganta a tsaye a inda take tana dagamin hannu, har sai da na shiga dakinmu, ina ma da biskit kala-kala a akwatina, amma ba ni da irin wadannan tsadaddun, alewa kuwa ba ni da ita don *yar kadan mamana ta saya min, ta ce na cika shan zaki ida na ga alewa ko biskit ko abinci bana ci sai shan alewa.
Don haka tuni na shanye alawowin a kwana kadan. Na haye kan gadona na lankwashe kafa na bude ledata cike da farin ciki don yau na huta da cin abinci tunda na sami alewa da biskit. Na dauko wata katuwar alewa wacce aka yi ta da cakudadden bonbita da madara, daga gani zata yi dadi. Tun kafin in kai bakina har yawuna ya fara tsinkewa. Ledar alewar kadai abar kallo ce da sha'awa tun kafin ka bude. Nakai ledar bakina zan cisga in yaga sai na dakata cak ina tunani. Abunda ya fado mun a raina nasihohin da labarun da wasu Malamai da prefect suke bamu a Makarantar kasancewarmu kanana, sababbain suwa bamu san abunda yake faruwa a makarantar ba.
Chapter 19 · 0% Book details