Sashe 4
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 10 min read
Ba su Naja'at kadai ba har su Goggo da Babansu nan da nan suka ji Iman ta shiga ransu saboda wadannan kyawawan dabi'unta. Inda tafi burge Babansu shine tunda Iman tazo gidan nan ya huta da bugun kofar dakin su Naja'at da asuba, kafin yazo ya tashesu sai ya tarar Iman ta tashesu tuntuni har sunyi sallah. Haka kuma take zama ta bude alkur'ani tayi ta kwarara karatun alkur'ani da kira'arta da muryarta mai dadi har garin Allah Ya waye. Dole su Naja'at suka fara koyi da ita. Goggo kuwa Iman ta kara shiga ranta saboda rashin son jikinta akwai aiki ko an hanata bata hanuwa. Kafin su ankara ta gama aikin gidan kakaf, har aikin da basa yi kullum Iman ta kirkiro shi kamar cire yana, da wankin bandaki kullum. Su Naja'at masu son jiki sunyi farin ciki da zuwan Iman gidan nan saboda hutawarsu kawai suke yi. Ko Goggo ta korosu ta ce su zo su taya Iman aiki sai ita Iman ta hana su ta ce su bari kawai zata yi. Ko kuma idan tana gudun kada Goggo tayi musu fada sai ta ce su sami waje su zauna su dinga yi mata hira tana aikin. Nan da nan suka ji sun shaku da Iman. Matsalar daya ce wacce take kawo musu illa wajen kara shakuwa da juna ita ce Hausa bata ishi Iman ba. Tana so ta fadi wani abu da yawa da yaren Hausa bata sanshi ba, haka idan suka fada bata cika ganewa ba. Harshenta yafi kama da na Fulani, wani lokacin kaji kamar Larabci ne yafi yawa a bakinta, Hausa dai kadan-kadan take yi. To inda Allah Ya tarfawa wannan matsalar tasu ta bambamcin yare ruwan sanyi shine da ga baya sai Iman ta fuskanci Goggo tanajin fulatanci, itama ashe fulatanci ne yarenta sai suka fara yarawa. Sannan sai suke turanci tsakaninta da Zubaida da Naja'atu da Suhaif. Babansu kuma daya fuskanci tana jin larabci sai shima suke yarawa, duk da bazai iya doguwar hira da ita ba sosai da Larabci bai kware ba. To fa yare ake zubawa a gidan nan kala-kala.
Suhaif yayi-yayi Iman ta saki jiki dashi su saba su dinga hira abu ya faskara taki yarda su saba. Kunya ce da ita sosai, daga gaisuwa babu abinda take kara ce masa sai dai idan yayi mata tambaya ta amsa, ta mike ta shige daki. Saboda ita nema ya fara zama da kannensa yana hira idan yazo ya same su suna hira, amma dif zaiji Iman ta dauke wuta ta daina zuba labari ta hau gyara nayafi tana tura gashi cikin dankwali. Idan ta sunkuyar da kai kasa ba zata kara dagowa ta kalleshi ba, balle suyi hira.
Bayan zuwan Iman da wata guda ta nuna sha'awarta ta shiga makarantar Islamiyyar su Naja'at da Zubaida. Bayan sun shaidawa shugaban makarantar cewa zasu kawo sabuwar daliba ya ce su biya mata kudin wata sai ta fara zuwa. Iman da Zubaida da Naja'at suna tashi da sassafe suyi aikin gida suyi wanka duk da ba kayan makaranta (uniform) suke sawa ba sai su saka manyan hijabansu wani lokacin Iman takan saka katuwar (nikaf) ta rufe fuskarta, su dauki jakar littattafansu su tafi. Ajinsu daya kasancewar nan ne ajin manya wadanda suka yi nisa, sun sauke alkur'ani tuntuni hadda ake koya musu. Da aka gwada Iman don asan wanne aji za'a saka ta sai suka ga Iman harta wuce *yan manyan ajin saboda tayi nisa sosai a hadda. Haka a fannin hadisai da zauransu. Tunda babu aji na sama dana su Naja'at sai suka sakata a ajinsu. Iman bata wasa da karatunta akwai hazaka a gida da makaranta koda yaushe ka ganta da littafinta a hannu tana karantawa idan bata da aiki. Haka take kara koyowa Zubaida da Naja'at inda suka kakare. Goggo ma ba'a barta a baya ba, ta yarda da hankali da nutsuwar Iman don haka take zama da Iman tana koya mata karatun kur'ani.
Yau Alhamis babu makaranta bayan duk sun tashi da asuba sunyi salla, kamar yadda *yan makaranta suka saba sai kowacce ta zauna akan abin sallarta ta bude kur'aninta tana karantawa har saida gari ya washe. Naja'at da Zubaida suka gyara shinfida suka sake kwantawa suka bude wani sabon barcin da basa samu suyi saboda makaranta. Iman ta mike ta fito tsakar gida don ta gaishe da Baba da Goggo sai taji tsit babu kowa da alama dai sun koma barci. Ta juya zata koma dakinta sai taji karar bude kofa. Tana jiyowa sai taga Baba ne ya fito daga daki dauke da wata bakar leda a hannunsa. Ya yi wanka ya yi kwalliya yana ta kamshin turare. Tayi sauri ta durkusa har kasa ta gaisheshi cikin harshen larabci. Ya amsa mata cike da fara'a ya shaida mata yau Kano zaije sai gobe zai dawo idan su Naja'at sun tashi ta fada musu ya wuce. Ta amsa masa da to, sannan tayi mas fatan Allah Ya kiyaye hanya. Ya fita ita kuma ta koma daki ta cire hijab da doguwar riga baka dake jikinta ta daura wani tsohon zaninta wanda ta mayar da shi na aikin gida ta sanya wata yaloluwar riga fara (tea shirt) ta daura dankwali ta fito tsakar gida don fara aikin gida. Tsakar gida kaca-kaca saboda sunsha hirar dare anci gyada ansha rake duk an zubar a tsakar gida. Kwanukan da aka cicci tuwo ne a watse a tsakar gida. Wasu a kicin, wasu kuma an kaisu wajen wanke-wanke kusa da rijiya. Iman sarki tsafta, ta tsaya kawai tana kallon tsakar gidan saboda mamaki da takaicin daya dameta a zuciya tana fadin "Daman haka muka yi da tsakar gidan nan jiya da daddare a duhu ban share ba, yanzu a dattin nan muka kwana? Ga babban abun kunya a haka Baba ya fito yaga tsakar gidan nan, zaice bamu da amfani a gidan. Tama rasa ta ina zata fara, wanke-wanken zata fara ko shara? Sai ta tsayar da shawarar ta hada kayan wanke-wanke ta fara share tsakar gida da kicin. Haka kuwa tayi ta share gidan ral a binka da Siminti ya fita yayi tas ko tsinke bata bari ba ta tattara ta kwashe. Sannan ta dauko kujera da omo bayan ta jawo ruwa a rijiya ta zauna ta fara wanke kwanukan da suka bushe da tuwo miyar kuka.
Suhaif ne ya dawo daga rakiyar mahaifinsa, ya rakashi har bakin titi ya hau mota sannan ya dawo gida. Yana sako kai cikkin gidan saiya ga Iman a zaune tana wanke-wanke kanta a sunkuye a kasa bata ganshi ba, kuma karan kwanukan da take wankewa basu barta taji motsin shigowarsa ba. Ya tabbata Iman bata zaci zai shigo a dai-dai wannan lokacin ba kuma bata zaci yana kallonta ba data ruga daki ta saki hijabinta. Ba zata zauna da damammiyar rigar nan a gabansa ba, saboda bata bude ko wutsiyar gashinta a gaban wani namiji. Iman ta san addininta, tasan darajar ta *ya mace gata da kunya.
Daya tabbatar bata ganshi ba sai bai bari ta ganshi ba yaja da baya a hankali ya koma. Wani dan karamin wundo ya tsaya yana lekenta domin yana kokonto ko ba ita ba ce bama. Saboda shi har yanzu baima kare mata kallo ba balle ya santa sosai, tsakaninsa da ita ya ganta a lullube cikin hijabi ta durkusar da kai ta gaishe shi, wani lokaci ma fuskarta a rufe da nikaf kafarta da safa. Yasan fara ce amma bai dauka tas-tas kamar haka ba. Ya kurawa fuskarta ido yana kallon hancin dodar, ga wani lumshasshen ido mai dauke da far tas da bakar kwayar ido dara-dara. Gashin girarta mau taushi a kwance dodar bakinkirin. Bakinta karami dai dai ita ga lobawar kumatu ko magana take balle tayi murmushi ko dariya. Ga wata *yar siriritar wushirya a tsakiyar fararen hakoranta. Fatar jikinta abar kallo ce farinta mai kyau tas da ita kama daga fuskarta har tafin kafarta jawur da ita. Suhaif ya shiga tunani a zuciyarsa "Anya kuwa wannan ba *yar Larabawa ba ce? Kai dole ruwa biyu ce ko uwarta ko ubanta a sami balarabe. Tana da tsananin kyau wadda ko a mata sai sun tsaya sun kalleta sun kara kallonta balle namiji. Suhaif ya nisa ya ce a zuciyarsa "Lallai dole ki boye wannan kyawun naki saboda mu anan kasar bakake zaki zame mana tamkar wata zinariya abar kallo abar sha'awa wanda kowa yake fafutukar tara kudi ya mallaka domin zinare abun ado ne ga mata, kadara ce ga da namiji shiyasa kowa yake son ya mallakeshi. Allah Ka bani Iman, Allah Ka sani inason Iman tun ranar dana fara ganinta har cikin raina.
Dankwalin kanta ne ya sulmiye zai fadi duk da hannunta da bakin tukunya tayi kokarin sa bayan hannu ta dafe dankwalin don kada ya fadi abun ya ci tura, kasancewar yana da santsi sai ya sulale yayi kasa yayin da idanuwan Suhaif ya dira akan wani lallausan gashi dogo baki wulik. Ya sake murtsike idanuwansa yana kallo. Gashi ne dai Suhaif ba karya idanuwanka suke nuna maka ba. Ta lunkube gashin ta tufke bai san iyakar sa ba amma ko ba'a fada masa ba yasan zai tabo gadon bayanta. Gashin kanta bashi da alaka dana bakar fata daga gani wannan tsatson jajaye ce. Suhaif ya fada a ransa "Dolo Iman ta hada jini da farar fata ko Uwa ko Uba, amma bari mu saba zan binciketa a hankali.
Ko da ta mike tsaye ta dauki kayan data wanke tana mikawa kicin sai Suhaif ya bi kira da dirin jikinta da kallo. Wai!! Allah Yayi halittarsa ance mutum tara yake bai cika goma ba ko ta ina aka ragu wannan? Mai madaidaicin tsawo ce. Ta fi kiba daga kugu daga sama siririya. Kafarta abar kallo ce saboda anyi mata shape mai kyau wanda shi ya taimaka wajen kara dirar jikinta. Tea shirt din dake jikinta bata da kauri don haka ta sake fito da cikar kirjinta. Ya ja dogon numfashi ya shafa kirjinsa ya fada a bayyane "Allah Ka bani wacce nake gani yanzu, kasa ta soni kamar yadda nake sonta. Bayan ta gama kwashe kayan wanke-wanken sai ta zo ta wanke bakin dake hannunta da ruwan kyau da omo. Sannan ta dauki dankwalinta dake kasa a cikin ruwa ta kade ta daure kanta, ta dauko tsintsiya da ruwa da omo ta fara wanke wajen.
Yaji zuciyarsa ta hau dukan uku-uku saboda ya sake sarkewa da son abunda ba lallai bane ya samu sai ya shiga tausayin kansa kamar ya rushe da kuka. Yasa hannayensa biyu a aljihu ya jingina goshinsa a jikin bango ya runtse idanuwansa yana zulumi da takaicin ta yaya ma zai saba da Iman balle ya sami soyayyarta? Yarinyar da ko hada ido sau daya bata yarda su yi, zaman minti uku bata yarda suyi, magana jimla biyar basu taba yi ba. To yaya zaiyi? Yana tambayar zuciyarsa yana tambayar kansa. Motsi ya ji a bayansa ya juyo da sauri, sai yaga Iman ce dauke da tsintsiya a hannunta daya hannun kuma dauke da abun kwashe shara da kanzo a ciki tazo zata zuba a abun zuba sharar dake ajiye a zauren. Saboda tsananin firgita Iman ta zubar da abubuwan dake hannunta. Ya sake zare wadannan manyan idanuwansa ya kalleta sai taji wani abu yarr a cikin jikinta, taji kamar a tsirara take, hankalinta ya tashi yau wanda take tsananin kunya da jin nauyinsa ya ganta a haka. Ta fisgo dankwalin kan ta tana so ta rufe jikinta sai taji ta tuje gashinta ya zubo a fuskarta da bayanta yaraf, ta fara ja da baya. Yana kallonta ya durkusa a hankali ya dauki tsintsiyar da abun kwasar sharar ya fara tattara kanzon data zubar a gabansa. Sai gabanta ya fadi tana gudun ko tayi laifi ta zubar da kanzo yana kwashewa ta hau in ina ta ce "I'm sorry. Ya sakar mata wani lallausan murmushi ya girgiza kai ya ce "ba mishkila, tafi kawai. Abunda ya bashi mamaki sai yaga tayi masa murmushi ta duka ta ce "Thank you ta sunkuyar da kai kasa ta juya ta tafi. Ya ajiye tsintsiya da abun kwasar shara yazo ya jingina ajikin kofa yana kallon yalo-yalon gashin nan nata har sai da ta shige daki sannan ya dawo ya kwashe kanzon daya zube ya shiga dakinsa ya kwanta tamkar bashi da sauran laka a jikinsa. Babu abinda yake hangowa a idanuwansa da zuciyarsa sai Iman.
Tun daga wannan rana Iman ta sake kara jin kunyar Suhaif sai kara gudunsa take, haduwa tayi musu wuya sai wasan *yar buya in dai ba kure musu tayi ba bata yarda ta tsaya su gaisa. Abun yana damun Suhaif babu yadda zaiyi ya hanata wannan hali, kuma duk gidan shi kadai take yiwa haka duk sauran ta saki jiki dasu rai-rai yake jiyo hirarta amma a gabansa sai tayi shiru, a hankali sai ta zame ta gudu daki shi kuwa a zuciyarsa ya saba da ita don tunaninta da sonta ya zame masa abokinsa na yau da kullum, tana zuciyarsa koda yaushe yana tunaninta, son kuma karuwa yake yi.