← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 80

Sashe 11

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iman ta gama alwala sai ta zauna tayi shiru tana tunanin irin farin cikin da taji na ganin Suhaif abun baya misaltuwa. Ya ajiye jakar kayansa ya dauki dabino guda daya a kayan shan ruwa da aka jere a tsakar gida yaci. Ya gaishe da Babansa da Gwaggo. Naja'at da Zubaida suka gaishe shi. Ya karasa wajen rijiya ya dubi Iman yayi murmushi ya ce "Iman ba gaisuwa? Maganarsa ce ta dawo da ita daga tunanin data tsunduma. Tayi murmushi ta ce "Ina jira ku gama gaisawa ne sai in gaisheka. Ta gaishe shi ta dauki buta da sauri ta cika masa ta durkusa ta mika masa sannan ta wuce daki ta tayar da ikamar sallah. Bayan kowa yayi sallah aka zauna aka sha ruwa tare a tsakar gida. Gwaggo kwananta daban. Iman, Naja'at da Zubaida kwano daya suke ci. Baba da Suhaif tare suke ci, ana ci ana hira. Suhaif ya ce "Wannan sallar me aka fi yayi ne? Naja'atu tayi farat ta ce "Yaya Suhaif ai mu wannan sallar munfi kowa chabawa kayan sallarmu kala biyar ne tsadaddu. Dadi ya rufe Suhaif daman ya lura Iman bata da wasu hadaddun kaya na kwalliya duk da dai shigar dogon hijab tafi yi. Amma ai tana sako riga da zani masu kyau a ciki idan ta cire hijabin ana gani. Ya ce "Haba! Dakko in gani, lallai ku *yan gata ne kayan sallar kala biyar? Naja'atu ta tashi ta shiga dakin Gwaggo ta dauko wata katuwar leda a shake da kaya ta zazzage akan tabarmar da Suhaif ya ke. Dai dai lokacin da aka kawo musu wutar lantarki dan da sai fitilar kwai. Suhaif ya ce lallai *yan Nepa ma sun san zanyi kallon kayan sallah shi yasa suka kawo wuta. Sai gaba daya suka kyalkyale da dariya. Suhaif da Naja'atu suka fara warware kaya. Naja'at ta ware kala uku-uku guda biyu ta ce wannan kala uku-ukun ni da Zubaida Baba na Kano yayi mana. "Ta ware wata atamfa Nichem guda biyu iri daya ta ce "Wannan Hajja Kakarmu tayi min ni da Zubaida. Sannan ta ware wata atamfa Code Boire ta ce "Wannan mu uku Baban nan gidan yayi mana ni da Zubaida da Iman. Suhaif ya ce "Kala daya na gani na Iman ina nata na wajen Baban Kano kala uku da kala daya wanda Hajja tayi muku? Naja'atu tayi shiru can ta ce "Mu biyu suka yiwa banda Iman. Iman ta sunkuyar da kai kasa, Baba da Gwaggo ma sai kunyar Iman ta rufesu. Suhaif yaji ransa ya hau tafasa don bakin ciki. Ya dubi *yan matan ya ce "Ku tashi ku shiga daki, ku bamu waje muna magana. Naja'at ta tashi ta hada kayan sallarsu ta nufi dakin Gwaggo inda suka ajiye, Zubaida da Iman suka kwashi kwanukan abincinsu suka shiga dakinsu. Suhaif ya ce "Haba Baba, haba Gwaggo yanzu *yan marainiyar Iman din nan baza'a riketa tamkar *ya ba? Wa take dashi a duniya yanzu wanda ya wuce ku? Baba ya dakatar dashi ya ce "Kai tsaya Malam kafin kayi mana wa'azi sai ka tambaya. Shin a cikin kayan da aka nuna maka baka ga kala dayan dana yi musu su duka ukun ba? To abunda Allah Ya horemun kenan ban ware Iman ba. Bani da hujjar da zan aikawa Usman Baban su Zubaida in ce suyi kayan sallah da wata bakuwa. Aka bibiyama bai san da ita ba. Dan duk zuwan da yake yi yana ganinta su gai gasa bai taba tambayar wacece wannan ba dan bai kawo aka wai a gidan ake rikonta ba. Gwaggo ta ce "Hajja kuwa su uku ta sayawa atamfa na dauka da Iman ashe dayar ta *yar Hajja ce tayi musu iri daya. Na yi magana ta ce min bata yi niyya ba baza ta dinka da Iman ba. Ya zanyi mata? Suhaif ya tashi daga cin abincin, bacin rai yasa ya fita daga ransa. Ya leka dakin da suke zaune ya kwallawa Naja'atu kira ta fito. Ya ce ta dakko masa *yan kwalayen kayansa guda hudu da ba'a yi da Iman ba. Ta je ta dauko da sauri ta kawo masa ya karba, ya dauki jakar kayansa ya wuce dakinsa. Naja'atu taje gurin Gwaggo tana tambayarta "Me zaiyi da *yan kwalayen? Gwaggo ta ce "Watakila sayo mata zaiyi. Baba yayi dariya ya ce "Ina yaga kudi? Zai je dai ya kara gani. Washe gari da sassafe Suhaif yayi sallama yace zaije Kano. Bai dawo ba sai ana gobe Sallah. A daki ya sami Gwaggo ita da Zubaida, Naja'atu da Iman an aike su. Bayan sun gaisa saiya zazzago kayan ledar da hannnunsa. Saiga kayan mata a dinke irin nasu Naja'atu kala hudu. Sak irin na su, dinkin wannan ma yafi nasu kyau da tsada. Surfani ne tsadadden gaske. Zubaida ta ce "Kai wadannan dinkunan na waye? Sun yi kyau gaskiya. Suhaif yayi murmushi ya ce "Da gaske sun yi kyau? Zubaida ta ce "Wallahi sunyi kyau sosai daman irinsu nafi so Mama tasa aka yi mana wadancan. Na waye wadannan din? Suhaif ya ce "Na Iman ne. Kamar an watsa mata wuta haka ta zabura ta wurgar dana hannunta ta tsuke fuska ta hau harare-harare. Zaka iya ganin bakin cikinta a baiyane. Gwaggo ta yi murmushi ta ce "Allah Ya saka maka, kaga yanzu sai su fito dukkansu ukun kayansu iri daya. Amma fa ka iya rigima Babangida ina ka samo kudi haka? Ince dai kai ka sami kayan sallar kai? Suhaif ya mike ya fita yana cewa "Idan tazo ki bata ni ai ba yaro bane, ba sai na saka kayan sallah ba. Da Iman ta dawo aka nuna mata kayan sai ta fashe da kukan murna. Su Naja'atu da Zubaida kuma yanzu suka tabbatar da abunda suke zargi Yayansu son Iman yake don haka sun dasa tsanar Iman a ransu, sai harararta suke. A boye Iman ta rubuta wasikar godiya mai dauke da kalaman so da kauna ta turawa Suhaif daki. Dolen su Naja'at suka saka kaya iri daya da Iman ranar Sallah saboda tsoron Suhaif. Da niyyarsu duk ranar da ta sa wannan su kuma sai su ki saka irinsa sai su saka wani. Amma babu yadda za su yi kayansu iri daya ranar sallah haka duk inda za su je tare suke zuwa, amma fa suna raina kansu idan suka jera. Iman ta yi kyau sosai, kyawun da duk garin babu wanda idan ya kalle ta ba zai sake juyowa ya sake duban ta ba. Dolensu suke jerawa da ita saboda Suhaif ya ce, su je tare, sai dai Zubaida ta sha yarwa Iman bakar magana a hanya, ita kuma sai ta yi shiru ba zata rama ba, babu wanda zata fadawa kuma. Suhaif ya kashewa Iman kudin kayan sallarsa kakaf har da neman ciko ya yi a wajen Najib. Haka yayi sallar babu sabon kaya, nasa ya wanke ya goge ya sa ya je Idi ya dawo ya ci tuwon sallah ya kwanta a daki yana karanta wasikun Iman shi ne babban farin cikinsa a yau ranar sallah. Ya ba wa kannensa sababbin kudi da ya canjo daga Kano. A takaice hoton Iman yake so yadda ta yi kyau da sallar nan ya fake da wai su hadu su dau hoto su uku su kawo masa. Bayan Sallah da kwana uku aka ce su Suhaif su koma Ogun, idan ya tafi ba zai dawo ba sai sun gama. Suhaif ya tafi ya bar Iman a gida duk *yan matan sun tsaneta, biyayya take yi musu tun karfi, amma komai ta yi sai a ce ta yi laifi, sai ta yi sauri ta ba su hakuri don ta zauna lafiya da kowa. Kwanci tashi babu wuya a wajen Allah, su Suhaif sun kammala bautar kasarsu. Allah cikin ikonSa sai ga Suhaif yana bakin cikin rabuwa da *yan Ogun saboda ya saba da su, mutane ne masu kirki. Sun yi masa mutunci ya saba dasu su ma haka. Bayan dinbin kyaututtukan da suka dinga ba shi, sun dauki hotuna saboda tarihi, dukkansu ba a son ransu suka rabu ba. Suhaif ya dawo gida ya iske su Iman lafiya kalau. Kamar yadda Iman ta saba tafiya makaranta da wuri, haka yau ma ta tashi da wuri ta gama aikin gida ta yi wanka ta sa hijabinta ta dauki jakar makaranta ta yi wa Gwaggo sallama, ta nufi makaranta ba tare da ta jira su Naja'atu ba, don sai fitowarta ma suka shiga wanka. A wajen wata mai kosai ta hango Suhaif da wani abokinsa suna saya. Yana hango Iman ya nufo inda take cike da fara'a yana cewa "Ka ga masu himmar makaranta, har zaki tafi? Iman tayi murmushi ta ce "Ai kuwa yau ma ban fito da wuri ba, tara fa har ta gota, wata rana kafin tara na je. Ta gaishe shi, gami da *yar harara ta ce "Kosai ma ka zo saya ko? Tuwon gidan namu ba za ka ci ba, shi ke nan, na yi fushi ma mu ma mun daina dafawa da kai, tunda ba ka son namu babu dadi ka fi son na sayarwa. Suhaif ya bude baki yana salati fadi ya ke: "Yi hakuri wallahi ba ni zan ci kosan nan ba, ni kosai bai dame ni ba. Tunda nake da ke kin taba gani na ci abincin wani gida? Ai sai naki balle kuma abincin sayarwa. Iman ta yi murmushi gami da yi masa wani sunkuyayyan kallo ta ce "Yau na ga ikon Allah ga ka a gaban mai kosai tun daga nesa naga ka mika mata kudi kana jira a zubo maka, kuma har da rantsuwa ba ci zaka yi ba, me za ka yi dashi sadaka? Su duka suka kwashe da dariya ya ce "Kin cika mantuwa, dazu kina damun koko na ce ki cika min kwanon sha mu biyu za mu sha, na shaida miki yau Najib zai zo daga Kano takanas don ya zo ya ganki, ku gaisa. Saboda bai taba jin na yi budurwa ba, sai kuma yaga na kwana ina bashi labarin ki da na je Kano, sai ya ce bari ya zo takanas ya ga wannan mai rabon. Dariya ce ta kubce musu su dukkansu. Iman ta maimaita "Lallai kuwa ya zo ya ga wannan mai rabon Suhaif ya ce
Chapter 11 · 0% Book details