Sashe 6
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari ranar Juma'a su Iman basu da makaranta don haka su Zubaida baccinsu kawai suke yi har karfe takwas na safe babu kowa a tsakar gidan. Iman a kwance take juyi kawai take ko itama ta samu ta danyi baccin safe yau taji yadda masu iya baccin safe suke ji don ita bata iya komawa bacci ba, bata san yaya suke ji masu yinsa ba. Ta duba agogo taga takwas ta dan gota sai ta mike ta cire *yar yaloluwar rigar baccin dake jikinta ta saka kayan da ta mayar da shi na aiki. Ta fito tsakar gida duk da ta share tsakar gidan da daddare tas yake babu datti amma ai ba za'a rasa kura ba. Sai ta shiga hado kayan wanke-wanke. Bayan ta wanke tas ta kawar da kayan saita share wajen ta kwashe kanzo da gayan tuwon da aka ci aka rage. Ta nufi zaure inda abun zuba shara yake. Akan wani dan dakali dake kofar gidan ta hango kafafuwan Suhaif bata hango gangar jikin ba amma ta jiyo dogon tsakin da yake ta ja da alama yana cikin damuwa, damuwar tasa ba zata rasa nasaba da zancen tafiyarsa bautar kasa ba, an tura shi garin da baya so kuma mahaifinsa ya ce dole yaje. Ta taho a hankali ta leka inda yake zaune ta ganshi ya dukar da kansa kasa ya rike kai da hannu biyu yana girgiza kai saboda tsananin damuwar da yake ciki. Iman ta ji tausayinsa ya kamata, ba don tana kunyarsa ba data bashi hakuri ya daina damuwa da yawa amma baza ta iya tsayawa tayi magana ba. Ta juya a hankali ta shige cikin gida taje ta karasa wanke wajen da tayi wanke-wanke ta koma daki ta zauna sai taji ta kasa zaman, ta tashi ta fito tsakar gida ta tsaya taji ta rasa sukuni lallai wani abu yana damunta a zuciya. Ta rasa meke yi mata dadi a ranta kuma yanzun nan abin ya fara nukurkusar zuciyarta don kalau ta tashi a safiyar yau zuciyarta cike da farin ciki. Can ta tuna ashe halin da Suhaif yake ciki ne ya shafeta itama ta kasa sukuni. Sai ta shiga mamakin kanta da kanta. Yaya haka? Meye wannan? Yaya na shiga damuwa don Suhaif yana cikin damuwa? Inji zuciyarta. Sai wata zuciyar tace "Ai ya kamata ki taya Suhaif duk halin da yake ciki ko farin ciki ko bakin ciki. Ki tuna fa shine ya taimakeki a lokacin da kike neman taimako, kin shigo kasar da baki san kowa ba gaba da baya. Ya tsaya tsayin daka sai da ya ga kin sami wajen zama daram sannan hankalinsa ya kwanta. Ya kamata a ce kin taya shi bakin ciki, sai ta koma daki ta kwanta tayi shiru a kan *yar katifarta. Can a cikin zuciyarta taji ance "Gaba daya wannan ba mafita bace kinzo kin kwanta ranki ya baci shi wanda kike dominsa bai san me kike yi ba kuma ko da ya sani babu abinda zai kara masa kije ki tare shi ki bashi hakuri ki gaya masa kalaman kwantar da hankali ki bashi misali da hadisai in da Annabi ya fada mana mu bi maganar iyayen mu kuma yarda da kaddara. Sai Iman tayi zunbur ta tashi zaune tayi shiru tana tambayar kanta da kanta tayaya zata iya tarar Suhaif tayi masa magana har tayi masa kalaman da zai gamsu ya kwantar da hankalinsa bayan kunyarsa take matukar ji, kwarjini yake yi mata sosai. Sai taji ranta ba zai yiwu ta tare shi don baza ta iya ba, to amma tana tunanin me zai hana ta rubuta masa wasika ta kai masa. "Hakaa kuwa za'ayi. Ta fada a bayyane. Ta tashi cak daga kan katifarta ta dauko jakar makarantar islamiyya dake rataye a jikin kusar dake manne a bangon dakin, ta dawo ta zauna akan katifarta ta bude jakar ta dauko littafi da biro, ta ciro takarda ta fara tsantsarawa Suhaif wasika cikin harshen turanci don shi tafi iyawa fiye da Hausa sai kuma fulatanci yarenta wanda shi tafi ji amma ai shi wanda zata yi dominsa baya ji. Da farko ta gaishe shi, gaisuwa irin ta addinin musulunci da kuma girmamawa. Sai ta nuna masa irin halin damuwar data shiga sanadiyyar ta ganshi yana cikin damuwa to amma ya bar damun kansa saboda abun bana damuwa ba ne in har zai barwa Allah zabinSa. Ta kara da cewa ya bi maganar mahaifinsa ya yi biyayya a gare shi hakika idan yayi haka zaiga budi a rayuwarsa. A ko ina yake ya sawa ransa Allah Yana tare dashi, kudu da arewa duk daya ne Allah yana ganin ko ina. Kada ya damu mutum yakan so abunda ba shine alheri a gare shi ba sai Allah Ya zabar masa abunda zai ji baya so kuma ya zama shine alheri a gareshi. Yayi hakuri yaje tayi alkawari zata zamanto mai yin addu'a a gare shi, insha Allah zaije lafiya ya dawo lafiya. Ta jawo wasu ayoyi a cikin littafi mai tsarki ta fassara taja hadisai tayi masa misali dasu. Ta kara yi masa nasiha daya kwantar da hankalinsa kada ya damu. Data gama rubutawa tsaf sai ta linke ta jawo zirmikeken hijabinta ta saka ta fito. Ta leka kofar gida ta hango Suhaif yana nan a zaune inda ta barshi sai ta tsaya tayi cak tana tunanin yaya za'ayi ta bashi wasikar. Mummunar faduwar gaba ce ta afko mata yayin da ta ga Suhaif a gabanta ba tare da ta ji motsin tafiyarsa ba. Shi ma yayi kicibus da ita, sai yayi kasake yana kallon ta bai zata zai ganta a nan ba, ya yi matukar mamaki da sassafen nan "Ina Iman za ta je, yau Juma'a kuma babu makaranta, bayan makaranta kuma babu inda Iman take zuwa? Wasu lokutan ne ma takan raka su Naja'at su je su gaishe da Hajja Kakarsu. Ta durkusa ta gaishe shi ya amsa ya ci gaba da kallon ta a zuciyarsa cike da alamomin tambaya. Ya ga Iman dai a tsaye ba ta shige gida ba, ba ta kuma fita waje ba, kanta a sunkuye a kasa. Ya ce "Iman unguwa za ki ne? Ta girgiza kai ta ce "A'a. Ya ce "Kawai kin leko kofar gida ne? Sai ta yi murmushi ta dora takardar da ke hannunta a kan wundon da ke kusa da inda suke tsaye ta juya ta shige cikin gida. Suhaif ya bita da kallo yana cewa: "Wasikar tawa ce ko kuma wani zan kai wa? Ba ta iya juyowa ta bashi amsa ba saboda kunya. Ya yi ta mamakin irin wannan kunya ta Iman, amma babu mamaki kunyar Fulani ta wuce haka. Sai ya sa hannu ya dauki wasikar da mamaki da kuma zumudi, wani bangaren cike da fargaba, Allah Ya sa ya ga abin da yake fita a cikin wasikar, ma'ana, Allah Ya sa ita ma ta fahimci son da yake yi mata, ita ma a ce tana yi masa. Ya shiga dakinsa ya sa makulli ya rufe ya zauna a kan wata tsohuwar kujerar da ke dakin. Ya yi bismillah sannan ya bude wasikar ya fara karantawa Suhaif ya tsinci kansa da tsananin farin cikin abin da ta fada kana kallon fuskarsa za ka iya ganin farin cikin da ya lullube masa zuciya, daman Hausawa sun ce. Labarin zuciya a tambayi fuska. Nan da nan ya ji mugun bakin cikin da tsananin damuwar da ke addabar zuciyarsa sun ware. Ya gamsu kwarai da bayanan Iman. Ya ji ya sake son ta fiye da son da yake yi mata a da. Ya maimaita karanta wasikar nan fiye da sau goma saboda ta yi masa dadi. Murna yau ba za ta misaltu ba a zuciyarsa. Can ya dau biro da takarda ya fara rubuta amsar wasikar. Bayan ya yi mata sallama irin ta addinin Musulunci sai ya nuna mata jin dadinsa da ta kula da halin da yake ciki har ta damu ta dauki biro da takarda ta rubuta wasika ta yi masa nasiha. Ya yi godiya sannan daga karshe ya yi mata alkawari zai yi amfani da shawarwarin da ta ba shi zai kuma bi abin da mahaifinsa yake so sannan shi ma ya yi mata alkawarin zai zamo mai yi mata addu'a a ko yaushe Allah Ya ba ta miji na gari mai tsananin son ta, saboda haka shi ma kuma yana rokarta a cikin addu'ar da ta yi alkawari za ta dinga yi masa ta ce Ubangiji ya ba shi wata yarinya da yake tsananin so da bege. Ya sa yarinyar ta san halin da yake ciki ita ma ta so shi, saboda wacce yake so din ba ta san yana yi ba. Ya bayyana mata cewar wannan dalili yana daya daga cikin dalilan da ya sa ba ya son tafiyar. Da ya gama rubutawa sai ya nade wasikar ya ajiye biron, ya dade a zaune yana tunanin a inda zai gan ta ita kadai ya bata wannan wasika. Ya dubi agogo ya ga karfe tara daidai, sai ya ji a jikinsa ai *yan gidan ma ba su tashi daga barci ba, tunda sukan kai karfe goma suna barci. Yayi zumbur ya fito tsakar gida ya tarar babu kowa, sai yaji motsin kwanuka a kicin, ya nufi kicin sai ya tarar da Iman ce take damun koko. Tana dagowa ta ga Suhaif suka hada ido sai dukkansu suka sakarwa junansu wani sanyayyen murmushi. Ta yi sauri ta sunkuyar da kanta kasa bata yarda sun kara hada ido ba. Ta ajiye ludayin da take juya kokon tayi sauri ta saka hijabin data cire ta dora akan cinyarta. Suhaif yayi murmushi ya jefa mata wasikar kan cinyarta ya ce "Ina daki ina jiran amsa nasan baza ki iya kwankwasa min kofa in fito in karba ba to sai ki dora akan wundon da kika ajiye mun dazu. "Bata ce masa komai ba kanta a durkushe a kasa tana ta murmushi. Ya dakko kofi a kwando ya mika mata. Ya ce "Zuba min kokon. Ta karba ta zuba masa ya karba ya tafi. Zumudin karanta me Suhaif ya rubuta bai barta ta gama juye kokon a kwanukan sha ba sai kawai ta rufe da faifai ta mike ta shiga daki. Ta tabbatar su Naja'at har yanzu barci suke haikan