Sashe 14
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suhaif na isa kusa da gidan yaga jakar kayanta a yashe a cikin kasa da takalmanta da hijabinta ya durkusa ya tsince ya karkade ya nufi cikin gidan. Ya yi bismillah yayin daya jefa kafarsa a cikin gidan gami dayin sallama a kofar dakin, yaji shiru ba'a amsa ba. Mutanen da suka hango shi a lokacin da yake shiga gidan suka tsaya daga nesa suna kallon ikon Allah suna sauraron abunda zai je ya dawo tsakanin Suhaif da wannan Dodanniya. Dodanniya mana Iman ta zamar musu a garin nan duk a firgice suke.
Ya ji gabansa na faduwa kasancewar dakin da duhu bai hango kowa ba a cikin dakin. Ya sake kwada sallama gami da kara tura kai cikin dakin ya shiga ba'a amsa ba kuma baiga kowa ba. Ya ajiye kayan dake hannunsa ya bude windon dake dakin, nan da nan haske ya gauraye dakin sai ya waiga kowacce kusurwar dakin babu abinda yake hangowa daga kura sai yana a jikin bango. Yayi matukar razana daya hango idanuwan Iman a bayan kyauran dakin tana kallonsa. Ya shaki numfashi yayi ajiyar zuciya da karfi don ganin Iman cikin wannan hali ya tsorata shi. Gashi kanta buyu-buyu babu dan kwali. Daga yadda yaga idanuwanta suna wurwurgawa yasan ba lafiya ta ke ba. Ya dan matso kusa da ita yayi mata sallama, bata amsa ba. Kallonsa take tamkar hoto. Ya nisa ya ce "Ga hijabinki kisa, ga takalminki kisa da jakar kayanki kizo mu tafi wani garin ba anan garin ba. Bata tanka masa ba, ya sake matsowa ya mika mata hijabin ya ce ta karba ta saka ko gezau bata yi ba sai kallonsa take tayi. Yayi magana harya gaji bata amsa masa ba, ya kira sunanta wajen sau ashirin bata amsa masa ba. Daga karshe ya ajiye mata kayan a gefe. Ya ce "Ko yunwa kike ji bari naje in suyo miki kosai da koko.
Ya je ya suyo ya zo ya ajiye mata a gabanta ya koma ya ciko mata ruwa a botiki da kofi ya kawo mata yayi-yayi taci kosai ta sha kokon, tasha ruwa. Idan zata yi alwalla ga ruwa a bokiti taki magana. Yayi da Hausa, yayi da turanci, ya burkuta mata dan abunda ya sani da Larabci da Fulatanci wai ko ta daina jin Hausa abu ya faskara Iman dai kallonsa take. Daga karshe ya fashe da kuka, yayi kuka har ya gaji ya tashi ya taho gida.
Mahaifinsa da Najib sun yi masa tambayar duniyar nan yaya Iman? dan takaici yaki amsa musu, ya kwanta yayi shiru sai shi sai abunda yake damunsa a zuciyarsa. Haka abincinsa na rana ana kawo masa ya dauka ya kai mata na safen nanan ko taba shi bata yi ba, tana nan zaune a bayan kofa inda ya barta. Ya dauke na safe ya ajiye mata na rana ya tafi. Daya kawo na dare sai ya tarar dana rana shima bata ci ba. Abun yayi matukar tayarwa da Suhaif hankali musamman irin duhun dakin daya barota dare yayi. Ita kadai ya shiga wasi-wasi anya kuwa Iman dinsa ce wannan ko kuma ba mutum ba ce daman? Ina son Iman, Iman ina sonki. Karki min haka Iman. Karki koma wata halittar da baza mu iya zama tare ba. Suhaif ya fada a baiyane yayin da yake kwance a dakinsa hawaye yayi masa kawanya. Najib na gefensa sai kawai ya dube shi ya girgiza kai don tausayi.
Haka Suhaif da Iman suka kasance kullum zai kai mata abinci sai uku a rana haka kuma zai dawo ya dauki kayansa ko loma daya bata yi ba. Haka zaiyi maganar duniyar nan baza ta amsa ba. Yanzu kanta a sunkuye yake ko idonta bata dagowa ta kalleshi balle yasa rai zata yi masa magana sun kwana biyu a haka a ran na ukun ne ya shigo gidan da yamma ya tarar da abin al'ajabi. Tun daga bakin kofa ya ga warin takalminta daya da wani abu kuma a jikinsa ja kamar jini. Ya tsaya yana kallon takalmin saiya wuce ya shiga dakin sai yaga warin takalmi a rataye a daure yana lilo ajikin azarar da ke rufin dakin shima jan abu a jiki. Iman na zaune ta juya bayanta wannan karon ta fito daga bayan kofar. Sai Suhaif yaji jikinsa ya dau karkarwa. Muryarsa na rawa ya ce "Iman meke faruwa, me nake gani haka? Kada ki cemun zargin mutane gaskiya be. Ya daka tsawa kamar zararre ya ce "Ki fada min, kimin magana ko ke wacece? Shin ke mutum ce ko ba mutum ba ce? Yau bazan bar dakin nan ba sai kin kasheni na huta. Kina wahalar dani kina tsorata *yan garin nan. Naki yarda a zarge ki, na kasa hakura da sonki. Ki kashe ni na huta da bakin cikin nan, sai ki bar garin ki bar *yan uwana a garinsu. Ko motsi bata yi ba balle ta juyo ta kalle shi. Wannan karon jama'ar dake taruwa suna hangen kofar dakin da Suhaif yake shiga sun fara razana saboda suna jiyo muryarsa da karfi yana fada.
Cikin fushi ya sa hannu ya finciko Iman da karfi ya juya fuskarta. Amma me? Baisan sanda ya ji shi fuk ya fadi kasa ba ya gwara kai da bango. Shin taba ta din da yayi shine ya fadi kasa ko kuwa fuskarta ce ta bashi tsoro ya fadi da kansa don razana? Oho! Fuskar Iman ta razana Suhaif ya sake gwala ido yaga lallai Iman ce duk da fuskarta ta canja zaka iya hango kamanninta. Idota jawur, jan kyalle a wuyanta jan kyalle a gashinta, jajayen kyalle a daure a hannunta da kafafuwanta. Suhaif ya gyara zama cikin fidda rai da sake yin numfashi a duniya ya ce "Iman da gaske ne abin da mutane suke fada kenan? Ta nuna masa kofar fita da hannu alamar ya tashi ya fita da sauri. Suhaif ya mike yana layi kamar zai fadi ga zafin da keyarsa take yi masa inda ya fadi ya doka kai a jikin bango, ya juya zai fita kamar daga sama yaji muryar Iman ta ce "Suhaif! Suhaif!! Suhaif!!! Da karfi ya juyo da sauri ya dubeta. Ta ci gaba da cewa "Ina baka shawara yau kada ka yi bacci ka kwana kana addu'a, ka kwana kana sallah, ka nemi tsari daga makiya, munafikai da shaidanu. Suhaif ya tambayeta cikin mamaki "Kamar yayafa? Ta daka tsawa ta ce "Kada ka bincikeni, kada kaki bin umarnina, kada ka karyata ni, kada ka shagala da barci ka ki yin addu'a idan ba haka ba zaka mutu a daren yau. Ba na son ka mutu don kana da kirki. "Mutuwa? Waye zai kasheni? Ya sake tambaya. Ta yi kara mai tsanani ta ce ya fita ya bata waje. Suhaif ya fice hawaye na zuba a idanuwansa yana nanatawa a zuciyarsa abu kamar wasa ashe da gaske mutane suke. Wannan lamari na Iman ya caja masa kai, har ta kai ta kawo hankalin iyayensa ya tashi sun ga Suhaif kamar mahaukaci yana tafe yana magana. Sai mahaifinsa ya kirawo wani malami bayan sallar isha ya zo yasa Suhaif a gaba yana tofe shi.
Bayan Malamin ya tafi sai Suhaf ya yi alwala ya ce zai je Masallaci acan zai kwana. A'a hauka ta bayyana sai *yan uwa suka dau kuka. A kayi-akayi ya dawo yaki dawowa ya shiga Masallaci yayi ta sallah yana addu'o'i. Cikin gida mata da *yan uwa da ubansa suma addu'a suke yi Suhaif ya tabu. Shi kadai yasan dalilinsa na kwana sallah da lazumi. Sai karfe tara na safe aka samu Suhaif ya fito daga masallaci suka nufo gida da mahaifinsa da Najib suna wani sashi a tsakiya wai dan karya koma Masallacin tunda suna tunanin aljanar Iman ita take kaishi Masallaci sai dariya ta kubuce masa idan ya ga sunyi wani abun. Dan shi da hankalinsa ras suke tunanin bashi da hankali. Idan yayi dariya sai su sake razana sun dauka haukar dariya ce ta kamashi. Sun kusa isa gida sai ga wasu motoci guda uku bus biyu da motar *yan sanda biyu ta zo ta wuce. Wani yaro ne ya rugo yana fadawa abokansa cewar Maigari da jama'arsa ne suka je Dutse suka shaidawa Gwamna abun da yake faruwa game da maganar Iman, cewar a kawo musu agaji annoba ta sauka a garin Doko a zo a fitar musu da ita shine aka ciko motoci biyu da malamai da kuma *yan sanda. Idan bata fito ba za'a saka mata tiyagas ko a kona dakin.
Ai kafin yaron nan ya rufe bakinsa Suhaif ya arta da gudu inda Iman take, Najib da Mahaifin Suhaif binsa suke a guje suna "Jama'a ku tare mana shi. Suhaif ya isa kofar gidan ya iske cin-cirindon mutane da Maigari da *yan fadarsa, ga *yan sanda na kokarin hada tiyagas zasu jefa cikin dakin. Malamai na bin katanga suna tofa addu'a. Amma an rasa mai shiga ciki saboda an riga an fada musu irin bala'in da suke cikin dakin. Suhaif na isa wajen, mutanen gari suka ce "Yauwa ga mai iya shiga wajenta. Suhaif ya ce "Ku dakata zan shiga in fito da ita karku saka mata tiyagas. Kafin su Mahaifinsa su iso Suhaif ya shige dakin sai suma suka tsaya a gefe suna kallon ikon Allah. Ya shiga ya iske Iman zaune tana duban bakin kofa amma jajayen kyallayen nan babu a jikinta. Ya karasa gareta yayi mata sallama bata amsa ba sai ya durkusa a gabanta ya fara mata bayani akan ta fito zasu tafi wani gari. Ta bude baki ta bashi labarin abunda ke faruwa a waje ta ce "Babu garin da zamu tafi. Malamai da *yan sanda ne zasu fita dani daga garin, kaje ka basu labarin bazan fita ba sai dai su kasheni. Mutuwa nake so. Mutumin daya kashe hukuncinsa a kashe shi nafi so a kasheni. Hawaye ya kwararo daga idanuwanta, sai Suhaif ma ya fashe da kuka ya tashi ya fita wajen jama'a ya shaida musu sakonta. Wani Malami daga cikin Malamai ya ce "Kaje ka ce mata ta fito za'a kasheta in har an bincika hukuncin kisa ya hau kanta.