← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 80

Sashe 27

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

YARENA ADDININA....CIGABAN LABARIN..., Jikin fadila ya fara sanyi ta dubeni cike da nadama
tace 'pretty ban fahimcekiba. "na nisa nace ina
mamakin yadda yar musulma zata iya buda jikinta
tayi zina nasan ko batada ilimin QUR'ANI sosai
duk inda take duk abunda take tasan Allah yana
kallonta. Ina sha'awar musulmai domin sun san darajar mata sai dai mace ta wulakanta kanta
domin addini yazo musu da cewar mace ta killace
kanta a gidan mijinta. Idan ya kama zata fita
unguwa ta suturce jikinta, hijab har kasa mace
musulma bata tsayawa da maza atiti kotaje gidan
wani suyi shakiyanci kota yarda wani da namiji ya taba jikinta ko su tafa hannu. Duk inda zata shiga
ita kadai ta saka tsoron Allah a zuciyarta Allah na
ganinta don Haka mijinta baya fargaba hartaje
inda zataje tadawo shiyasa nake sha'awar
addininku fadila. Amma ke kin zubar da duk
wannan gatan, don duk wanda Allah yayishi musulmi dan musulmai ba karamar kyauta Allah
yayi masa ba kuma Allah yaso shi da rahamarsa.
Bai kamata ki zubar da wannan baiwar ba fadila."
sainaga idonta ya cicciko da hawaye, ta zauna
tayi shiru tana tunani. Naci gaba da cewa "kina
musulma fadila ban taba ganinki kintashi kinyi sallah ba saboda karki batawa wani arne rai
Gibrel da kawayenki su Ngozi kin shiga cikin arna
gaba da baya kin bar addininki. Ga sabon Allah
da kike ciki tsantsa. Cinki da shanki da suturarki
duk haramun ne. Ga uwa-uba hakkin iyayenki,
kin fadamun aure za'ayi miki kikace bakya son mijin kika kai musun Gibrel suka ce czaki aureshi
ba kika hado kayanki kika biyo shi ku kazo kuke
holewarku? Iyayenki duk inda suke suna chan
suna tunaninki, kin dauki alhakinsu kin rusa duk
tarbiyar dasuka yimiki fadila. Kece mutum ta uku
da zan fada mata wani boyayyan sirri; daga hamma huzaifa sai mamarsa saikuma keda zan
fada miki yanzu. Fadila ni musulma ce, kuma
nakarbi musulunci a boye duk ranar da
mahaifiyata taji ina sallah zata yankani ne kawai."
fadila ta zazzaro ido tana mamaki. Naci gaba dayi
mata bayani, nace "butar nan da nake dauka in shiga ginin chan salla nake shiga in buya inyi.
Hijabina da abun sallata da carbina duk suna ciki
aboye banaso kowa yasan ni musulma ce shiyasa
nake mamakinki, karfi da yaji kinbar addininki
addinin tsafta da gaskiya. Kiji tsoron Allah fadila,
ki saka aranki duk inda kike Allah yana ganinki, akwai mutuwa, akwai hisabi, akwai wuta da
aljanna.
Kafin in rufe bakina fadila ta rushe da kuka ta
rungemeni tsam-tsam, nima kukan nakeyi. Cikin
kuka fadila tace mun "ban taba tunanin akwai
wa'azin da zaisa inyi nadama ba, inji na tsani abunda nake sai yau. Pretty kin fimu wayo ashe,
nake miki kallon wawuya?" dakyar na lallashi
fadila na mayar da ita wajen zamanta tazauna.
Nadauko muciya nafara tuka tuwona. Tambayoyi
fadila take mun wai yanzu yaya nake gani?
Inbata shawarar yadda zata canja rayuwarta. Shawarar dana bata nace ta tuba ga Allah shita
sabawa kuma Allah mai rahama ne, mai jinkai zai
karbi tuban wanda ya tuba. Sannan tabar zinar da
take, ta hada kayanta ta koma gidansu ta nemi
gafarar iyayenta, ta rike salla ta shiga islamiya
tanemi ilimin QUR'ANI da hadisi tayi addu'a Allah yafito mata da miji nagari musulmi tayi aure ta
hayayyafa ta bawa ya'yanta tarbiyar addinin
musulunci. Ta tambayeni toni kuma akan kaina
yazanyi da rayuwata tunda na fada mata
mahaifina musulmi ne amma mahaifiyata ba
musulma bace. Gashina musulunta a boye,? Nayi shiru ina tunani nikaina bansan yazanyi ba. Ina
fargabar komawa gida tunda karatu aka turoni
banyi karatun ba, kuma yadda zanje in zauna a
gidan da sabon addinina. Na faiyace fadila labarin
da bata saniba na game da rayuwata, na shaida
mata wani dan makwabcinmu shine ya cusawa zuciyata tsoron Allah. Shine ya musuluntar dani.
Abunda yafito daga bakinta shine ki auri hamma
huzaifa mana shine mai sonki zai kula dake ya
kuma kara koya miki addimin." najuyo da sauri
na dubeta can na tambayeta. "tayaya zan
aureshi? Kuma yaya akayi tasan inason huzaifa." tayi murmushi tace ai karshen so yana miki kema
kuma haka daman ginshinkin so shakuwa kin
shaku da huzaifa fiye da iyayenki. Huzaifa yana
burgeki saboda addininsa da halayensa shi yaja
ra'ayinki zuwa musulunci kawai ya daukeki kuyi
tafiyaku wani garin kuyi aurenku tunda mahaifiyarki ba zata yarda ba." zance fadila haka
yake babu namijin da naji ina so nake sha'awarsa
a matsayin mijina irin hamma huzaifa amma
nasawa raina bazai yuwu ba. Nayiwa fadila
bayani hamma huzaifa yanada tarbiya yana yiwa
iyayensa biyayya bazai yarda ya daukeni mu gudu wani gari muyi aureba. Na dai cewa fadila ta
tayani da addu'a amma rayuwata tana cikin wani
hali don haka nema nake sha'warta domin
uwarta da ubanta dukka musulmai ne kuma
musulmi zasu aura mata, bahaushe YARENSU DA
ADDINNISU daya. fadila ta tausayamin sosai kuka nake tamkar
idona zai fita naji na tsani rayuwata, naji haushin
mahaifina daya auro mahaifiyata wacce addinin
suba daya ba suka sakani a cikin rudani. Fadila
tayi nadama ta gamsu da shawarwarina ta shaida
min in Allah yaso ko..

Surayya Abubakar
Surayya Abubakar

________________ YARENA ADDININA.
___CI GABAN LABARI part 2

Nan da nan na nemi yawun bakina da makogarona na rasa sun bushe kamas don tashin hankali, sai zuciyata ta lalubo min addu'ar da Huzaifa yake karantawa a duk lokacin da bala'i ya tunkaroshi. Naji kafata ba zata iya daukar jikina ba da dan Jaririn dake hannuna sai nima na sulale na zauna kamar yadda tashin hankalin ganina yasa Mahaifiyata ta sulale ta zauna. Karkarwa suke suna nuna Jaririn dake hannuna, nima hannuna na karkarwa idanuna na zuba tamkar ruwa a famfo ina nuna gagarumin tashin hankali da nake hange a tare dasu.
Mahaifina yayi karfin hali yasa hannu ya tashi Mahaifiyata tsaye yana goge mata hawayen daya wanke mata fuska. Ya ja hannunta da kyar suke jefa kafafuwansu suka shiga gida suka barni a nan zaune cikin kasa turmus. Na kalli gabas na juya yamma, na kalli kudu na juya arewa, na kalli sama, na kalli kasa gaba daya duniyar tayi min zafi ji nake kamar ba a duniyar nake ba, dama a dau raina. Hankalina ya gushe, kaina ya dau zafi gumi ya keto min hade da hawaye mai radadi na rasa inda zan nufa inji sanyi a raina. Babu mai lallashina, babu wanda zanwa bayani ya gane halin da nake ciki bani da sauran gata sai Allah. Shi kadai nake ambato, kowa ya watse ya barni. Na kurawa Jaririn da ke hannuna ido ina kallonsa, sai tsala kuka yake har da hawaye kamar yadda nake hawaye, na fashe da kuka na rungumeshi tsam ina tausayin kaina amma na fi tausayin Jaririn, shi da baisan komai ba na rayuwa.
Tabita naji ta tabani na dago da sauri na kalleta itama hawaye take, ta rungumeni da dan Jaririn dake hannuna mu duka ukun kuka muke. Ta mika hannu ta karbeshi tasa hannu ta tasheni tsaye tana karkademin jikina, tace inzo mu shiga gida. Na girgiza kai, na sharbe hawaye nace "Mama Tabita ba zan iya shiga gidan nan ba da sunan in ci gaba da rayuwa. Tabita ta ce "Rufkatu me kike nufi da baza ki shiga gidanku kici gaba da rayuwa ciki ba? Ga Mahaifiyarki ga Mahaifinki su basu koreki ba, ke zaki kori kanki. Ina zakije ki zauna wanda yafi nan gidanku ga ki da dan Jariri. Na sake rushewa da kuka na ce "Ni ba zancan dan Jariri bane ya daga min hankali. Mama Tabita bakya ganin yadda Mahaifina ya zama? Tabita ta bude baki tana mamakina can tace "Na dauka babban farin cikinki ne yanzu hankalinki zai kwanta binciken da kika dade kina yi akan addinai kala-kala, me yasa kowa da abinda yake bautawa ba'a bautawa abu daya Mahaifanki suna bin addinai daban-dabam, yanzu Mahaifiyarki da Mahaifinki da ke da kannanki kun zama abu daya kuke bautawa. Allah Yasa Baban wannan yaron shima ya zama yana bautawa abun da kuke bautawa. Tasa hannu ta dafa kafadata ta ce "Zo mu shiga gida in kintsaki ke da danki daga ganinku kunsha wuya.
Na fisge kafadata naki tafiya na tsaya cak na rasa abun yi, jin zuciyata nake tamkar ana kwankwatsamin don takaici, wani jiri ne yake daukata yake shirin ya yar dani kasa. Tabita na lallashina bana fahimtar abunda take fada. Ukuba tayi ukuba, tashin hankali yayi tashin hankali na zura da gudu gidan su Hamma Huzaifa inje in tambaye shi, ya akayi yana raye ya bari haka ta faru da Mahaifina. Sai Mahaifiyarsa ta ce min ai a lokacin dana ganshi dinann a bakin mota kayansa ake zubawa a mota tafiya zaiyi Saudia. Jami'ar koyan addinin Musulunci ta Madina ya tafi karo ilimim addinin na tsawan shekaru hudu. Ta dauko min wasikar daya bari a bani. Na bude na karanta, ashe Hamma Huzaifa yana tsananin sona bai fadamin ba sai a wasika. Na sulale na zauna a tsakiyar dakin su Maman Huzaifa ina ta sharbar kuka. Maman Huzaifa tayi ta bani baki ta ce "In kwantar da hankalina in daina kuka duk abun daya samu bawa jarrabawa ce daga Allah. Na ji dan sanyi a raina dana samu mai lallashina mai nuna min akwai Allah. Na share hawayena da gefen mayafina nayi ajiyar zuciya. Mama ta matso kusa dani ta ce "Fatima, Huzaifa ya shigo dazu yana hawaye ya shaida mun dalilin hawayensa ke ya gani da dan Jariri kin haihu. Yayi tsananin bakin ciki da bacin rai da kika watsar da duk abubuwan da ya koya miki tun kina yarinya, yace mun tunda yake bai taba ganin yarinyar da take da matukar hankali da tunani da sanin ya kamata kamarki ba, ya shaku dake yana kuma godewa Allah da Allah Yasa kika Musulunta ta sanadiyyar sa, yasan kuma ba karamin riko zaki yiwa addininki ba. Amma hankalinsa yayi mummunan tashi da yaga abun da bai taba zata ba a gareki. Nasan duk inda yake yanzu yana can yana tunani da bacin rai. Da kyar na lallashe shi ya tashi ya tafi shi da direba za'a kaishi filin jirgi.
Chapter 27 · 0% Book details