Sashe 71
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read
da matsayi da take jina a zuciyarta. Ga kuma matata kawarta. Na nuna mata duk abubuwan data zano bai haramta aure tsakaninmu ba. Ta amince daga baya, tun a waya muka shaidawa Iyayenmu, babu wanda bai yarda ba a cikinsu Mun hadu da Suhaif da Najib a satin da zamu taho daurin aurenmu. Bani da masaniya akwai tsohuwar soyayya a tsakaninsu, na dai kula Najib ya fi Suhaif fara'a da son hira. Sai na zata halittarsa ce haka, sai ban damu ba. Muka dunguma muka taho Abuja, to a ranar na fara sanin halin da ake ciki. Zan shigo kenan cikin falon da Najib da Fatima suke zaune sai na ji suna hira Najib yana shaida mata damuwar da Suhaif ya ke ciki a sanadiyyar sonta. Itama tana kuka tana fadar halaccin da Suhaif yayi mata. Abunda ya fi dagamun hankali shine da aka ce yaki aure saboda jiranta, kuma ba zai yi aure ba har abada idan ya rasata. Ban nuna musu naji hirarsu ba, a mota hanyarmu ta zuwa Kano nake tambayarta yadda suke da Suhaif ta bani labari tas zamanta a garin Doko, da taimakon da Suhaif yayi mata har da yadda suka yi da matsafan da suke cutarta. Amma bata ambaci kalmar soyayya da take tsakaninsu ba saboda kada in sani raina ya baci. Na ci gaba da kula da Suhaif da halin damuwa da yake ciki, tun daga Kano har zuwasu daurin auran nan. Tuntuni nake tunani ko na bar masa ita tunda yana tsananin sonta? Sai na shiga kokonto ina zulumi domin ina sonta nima, idan na bar masa ita kuma zan cutu. Naci gaba da addu'ar Allah Ya zaba mana abunda yafi alkhairi kuma duk sanda zan kwanta barci sai nayi istahara Allah Yasa inji zabi mafi alheri da yafi kwantamin a zuciyata. Jiya da daddare ana hira sai Suhaif ya tashi ya fito, Fatima ta biyo shi, ni ma sai na biyosu. Na ji duk abunda suka fada, yana kuka tana kuka har Suhaif ya ce tayi masa addu'a idan ya mutu. Ya roketa kada ta bari in san ciwon son ta ne ya kashe shi. Dukkanmu nan Musulmai ne, duk Musulmu ya san Hadisin Annabi da ya ce "Imanin dayanku ba zai cika ba har sai ya sowa dan Uwansa abunda ya sowa kansa. Ina son Fatima, Suhaif ya na son Iman fiye da ni, har yana kokarin haramtawa kansa aure gaba daya a rayuwarsa, yana kokarin rasa ransa saboda sonta. Itama tana sona amma kuma tana kukan rabuwa da shi tana tausayinsa, zata dauwama cikin tausayinsa musamman idan ya rasa rayuwarsa a kanta. Nayi koyi da hali, dabi'a, kirki da karamci irin na mutanen Madina. Yadda suka yiwa Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da yayi Hijira daga Makka zuwa Madina shi da Sahabbansa. Mutanen Madina da murna suka tare shi, su raba gidajensu suka basu rabi, wasu su saki matansu suka aura musu. Don haka ko da ace na auri Fatima zan iya sakinta in bawa Suhaif ya aura. Idan na auri Fatima na so kaina da yawa saboda ina da mata guda daya, shi kuma Suhaif ba shi da ko guda daya, yana cikin ukuba da tashin hankali ya rasata, ni kuma ina cikin walwala da jin dadi zan aureta. Sai naga bazan iya yiwa dan uwana Musulmi haka ba. Na yanke hukuncin na barwa Suhaif Fatima ya aura ni na hakura. Alla Ya dubi zuciyata Ya san dan shi nayi, sai Ya yaye mun damuwa da bakin ciki. Yanzu haka ni da Ubangiji ne kadai nasan dadin da farin cikin daya rufe min zuciya. Gaba daya suka dauki kabbara, Iyayen Suhaif, Mahaifansa Huzaifa, Mahaifan Iman suka dinga shi masa albarka. Hawaye ke zuba a idanuwansu su dukka harda Huzaifa. Suhaif ya rungume Huzaifa ya kasa magana sai hawaye kawai ke zuba. Iman ta rungume Mahaifiyarta su dukka kuka suke. Mahaifiyayar Iman ta share hawaye ta ce "Lallai sai yanzu na sake gaskatawa, na sake rungumar addinin Musulunci da karfina, zuciyata, da dukiyata gaba daya. Hakika Musulunci addini ne mai salama, addini ne mai girma, addinine mai karamci. Ya koyawa Musulmai son junan su, su hana kansu su bawa dan uwansu, a taba Musulmi daya suji kaman su duka aka taba. Suna da kishin addininsu, na kara gane gaskiya, gaskiya ce, na kuma gane addinin gaskiya. Allah Ya sanar dani hakan ta hanyar *yata ta cikina. Tun da cikinta kafin na haifeta ina mafarkan da suke min nuni da hakan zata faru nan gaba, sai na ki ganewa. Bayan na haifeta sai naga fassarar mafarkaina Musulma na Haifa, mai kira zuwa ga addinin Musulunci, duk naki yarda da gangan na danne sai daga baya naga da gaske Malama na haifa a cikina kuma tana kira zuwa ga gaskiya sai na yarda na bita. Na godewa Allah, Huzaifa na gode, Allah Zai saka maka sakayya da gidan Aljanna dalilin wannan abunda kayi. Huzaifa ya amsa da "Amin na gode Mummy. Mahaifiyar Huzaifa sai yanzu tayi magana ta ce "Huzaifa dana, na yarda da kai dari bisa dari. Nasan tausayinka, kana kaunar *yan uwanka da ma sauran Musulmi gaba daya. Nasan zaka iya haka, zaka iya abunda yafi haka. Mutane suna ta mamaki amma ni dana haifeka banyi mamaki ba. Tunda na sanka fiye da kowa, nasan halinka Allah Yayi maka albarka, Allah Ya saka maka da Aljannah. Hawaye a idon Huzaifa ya amsa da "Amin Fetal" yadda suke kiranta kenan.