← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 80

Sashe 15

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suhaif kuka yake haikan ya koma cikin dakin da Iman take ya shaida mata ta fito sun ce zasu kasheta. Wannan karon murmushi ta yi. Suhaif ya dauko mata hijabinta ya ce ta saka saboda akwai maza da yawa a waje. Iman ta girgiza kai ta ce "Ni da za'a kasheni maye abun saka hijabi? Ba zan saka ba. Suhaif ya girgiza kai don tausayi ya cukuikuye hijabin ya dauko mata jakar kayanta da takalmanta. Iman ta mike, tafiyarta da kamanninta sun dawo dai-dai ta dubi Suhaif ta ce "Har yanzu ni Musulma ce idan aka kashe ni aimin wanka, a yimin sallah, a yi min sutura irin ta addinin Musulunci ina son Musulunci. Sai hawaye ya zubo daga idanuwansu su duka "Suhaif ya ce "To naji amma ki saka hijabinki sai kifi kama da Musulma sai su yadda muyi miki Sallah. Ta karba ta saka hijabin suka fito. Jama'a sunyi mamakin Iman sanye da hijabinta a nutse yadda take da, *yan sanda da Malamai sai jikinsu yayi sanyi suna fadin yarinya nutsattsiya haka ace mata mayya? Watakila ma bakin ciki ne yayi mata yawa ta shiga wannan hali. A gindin katuwar bishiya aka shimfida tabarmi da kujeru aka ce ta zauna za'ayi hira da ita ayi mata tambayoyi kafin a kasheta din. Iman taki zama ta ce ita dai kawai a kasheta babu hirar da za'ayi ta gaji da duniyar.
Malamai suka ce babu yadda za'ayi su kasheta basu ji wa da wa ta kashe ba, don sai wanda ya kashe wani sannan a kashe shi. Da kyar Suhaif ya lallasheta ta zauna akan wata tabarma Suhaif ya ajiye jakar kayanta yazo ya zauna a kusa da ita. Mutanen gari mata da maza suka dinga diddukowa, a ciki harda Goggo dasu Naja'at. Kuka kawai Iman take ta kasa magana. Anyi mata tambaya kala-kala tayi guda ASHIRIN DA HUDU taki amsawa tamkar da GANGAR JIKINTA ake magana Ruhinta baya wajen. Ba karamin yi da baki aka yi ba kafin Iman ta bude baki ta fara magana.
LABARIN IMAN...........

Wash gaskiya na gaji da shige da fice dan ganin na kawo muki labarin nan.

clap 4 me.... Kunsan na cika jarumi da har nabi bayan Suhaif na ambalo muku abin daya faru tsakanin su. Su wa'e ko Oho. Lolx...

Reedwan Suraj Isma'il

>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN

_LABARIN IMAN_

Ta ce "Makasudin shigata wannan mummunan hali na dangantashi da Iyayena. Su suka jamin wannan bakar rayuwa. Tun kin maganar Allah da abinda Annabi ya zo dashi sai bata, sai kuma kuncin rayuwar duniya da lahira.

Mahaifina mutumin Gombe ne bafillatani ne gaba da baya kallo daya zaka yi masa kaga kamannin Fulani. Fari ne tas dogo sosai sunan Mahaifina Lamin kuma shine babba a gidansu sai kannensa mata guda biyu Hajara da Gambo, mahaifinsu ya rasu tun suna kanana Mahaifiyarsa ce kawai take kula da su sunanta Fatima. Sun sha wuyar rayuwa kasancewar duk dangin mahaifinsu basa kulasu, sun bar Mahaifiyarsu da wahalarsu. Ta jajirce sai sunyi karatu musamman mahaifina ganin shine babba namiji babu abunda zata masa irin ta bashi ilimi gara ma matan dake su aure zasu yi shine ya kamata yayi karatu ya sami babban aiki ya riketa ya rike kannensa. Ta sayar da shanunsu ba adadi da gona don Lamin ya sami ilimi. Allah cikin ikonSa ya gama sakandiren dai-dai lokacin yayi nisa a karatun alkur'ani gashi da hazaka a duka bangarorin biyu. Ya sami admission a Jami'ar dake Bauchi wato ATBU suka bashi Engineering course din masu kwazo da kokari. Haj. Fatima Mahaifiyarsa ta hada masa duk abunda zai bukata na makaranta ya tafi.

Mahaifiyata kuwa sunanta Patrica ba Musulma bace. Mahaifiyarta Inyamurace mutanen Onisha, Mahaifinta kuwa bature ne jar fata. Yazo nan ya ganta suka yi aure daga karshe ya tafi da matarsa can kasarsu Maziko acan Allah Ya basu haihuwa suka haifi Mahaifiyata Patrica. Ai dole tayi kyau don ta biyo Mahaifinta sak farinsa da gashinsa da hancinsa, idanuwanta ne irin na Mahaifiyarta dara-dara duk da Mahaifiyar ma farar Inyamura ce tas amma farin Patrica kana gani kasan na farar fata ne. Mahaifiyata na shekara uku Mahaifinta ya rasu. Cikin dare Mahaifiyarta ta saceta suka gudo Nigeria don taga alama dangin mijinta na kokarin kwace mata *yarta.
Mahaifiyata na da shekara tara Mahaifiyarta ta rasu a garin Onisha sai kaninta ya dauketa mai suna Uncle Sunday. Aiki ya kaishi garin Jalingo wato Taraba State nan Mahaifiyata tayi karatun sakandire dinta ta samu admission ita ma a nan ATBU Bauchi inda Mahaifina yake suka bata courst din Architecture wato zane da tsara gine-gine. A lokacin Mahaifina yana shekara ta uku wato lebel 3 Mahaifiyata ta shiga label 1.

Allah cikin ikonSa tun sanda Mahifina yasa ido akan Patrica yaji duniya babu wacce yake so sai ita. A hankali suka saba musamman a lokacin Jarabawa wajen karatunsu daya, kasancewarsu su duka masu nacin karatu ne har yake koya mata abun da bata sani ba. Bayan sun saba sai ya fito mata da bukatarsa cewar yana sonta kuma da aure. Abunda ta fara nuna masa ya za'ayi yace zai aureta bayan YARENSU da ADDININSU ba daya bane? Ta nuna masa tayi zurfi a addininta, uwa-uba kawunta murikinta babban mukami yake dashi a wajen bautarsu sune masu bin kauyuka suna kira azo cikin addininsu. Ta ce tayi nisan da babu wani abu da zaisa ta canza addininta. Mahaifina ya nuna duk wannan mai sauki ne shima bazai bar Musulunci ba ya dawo addininta ba, don shima yayi nisa a addininsa amma zasu iya aure kowa yayi addininsa. Ta nuna masa wannan abu ba mai yiwuwa bane ya bar maganar kawai. Yaran da zasu haifa fa ai zasu iya shiga addininsa. Yayi mata alkawari duk yaran da zasu haifa ya yarda subi addininta idan sun ga shi suke so. Tambayar da tayi masa ita ce "Ka yarda da *ya*yanka su bi ADDININA kai kaki yarda ka bi ADDININA meye dalilinka nayin haka? Ya kasa amsa mata wannan tambayar. Amsar ita ce idonsa ya rufe yaga wacce yake so baya tunanin rayuwar *ya*yansa yadda zata kasance nan gaba. Wanne irin bacin ran Mahaifiyarsa da danginsa zasu shiga idan suka ji ya auri wacce ba Musulma ba?
Patrica a kullum tana nunawa Lamin bata son wannan soyayyar tasu domin abune mai wuya musamman idan aka koma bangaren Iyaye. Iyayensa da nata ba zasu yarda ba don haka su hakura su auri wadanda YARENSU DA ADDININSU yake daya. Amma Lamin ya makale shi dai yaji ya gani ba gudu ba ja da baya. Tayi masa wulakancin da ko kare bazai dauka ba don yaji haushi ya rabu da ita, duk da tana tsananin sonsa itama amma tana tunanin gara su hakura domin ita babu mutanen da ta ki jini irin Musulmai da addinin Musulunci. Lamin ya gama karatunsa ya tafi bautar kasa ya bar Patrica a ATBU ita bata gama ba. Allah cikin ikonSa aka turashi Jalingo garin su Patrica acan yake bautar kasarsa. Lokaci-lokaci yake zuwa ya gaishe da kawunta marikinta ya shaida masa shi abokin Patrica ne a makaranta. Wani weekend Patrica tazo gida ta iske Lamin da kawunta har sun saba hira suke haikan. Tayi matukar mamaki ya aka yi Lamin ya nemo gidansu harya shisshigewa kawunta haka suka saba? Bayan ya gama bautar kasarsa ma saiya nemi aiki a garin saboda abar kaunarsa Patrica. Duk inda take yana biye da ita, duk sanda ya shiga Gombe garinsu sai ya karasa Bauchi wajenta haka idan aka yi hutu ta dawo jalingo Lamin yana Jalingo kullum saiya zo gidansu Patrica.
Abun ya fara bata tsoro don kawunta ya fara fuskantar akwai soyayya a tsakaninsu ba kawance bane. Tasan abune marar yiwuwa tunda tun tana yarinya yake yi mata fada tasan kawayen da za tayi a makaranta ban da Musulmai domin zama da Musulmai zasu dinga saka mata wata akida har wataran taji tana son addinin Musulunci. Amma me? Sai taga kawunta da kansa yake nuna mata ta kula Lamin tabar wulakanta shi, don yaro ne mai hankali da nutsuwa. In har yace zai aureta ta yarda ta aure shi.
Patrica ta tsorata da maganar kawunta. Ya za'ayi da bakinsa zaice ta auri musulmi. Ya fada mata manufarsa ita ce watarana zasu iya jan hankalin Lamin ya shigo addininsu. Tunda ya nace yana matukar sonta kamar ransa, har ya yarda *ya*yansa su bi addininta shima zai iya canjawa. Patrica ta yarda da zancen kawunta daman kuma tana matukar son Laman sai ta sakarwa Lamin fuska suka yi ta tafka soyayyarsu. Aka tsayar da lokacin aure da zarar ta gama karatunta sai tayi bautar kasa a dakin mijinta.
Chapter 15 · 0% Book details