← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 80

Sashe 20

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ansha ja mana kunne akan mu guji cin abun wacce bamu sani ba, saboda akwai dalibai da suke kungiyar matsafa a makarantar, suna nan jifge guda har sun kafa kungiyarsu suna kuma jan *yan uwansu dalibai cikin kungiyoyinsu a boye. Wadannan daliban ba'asan ko su waye ba kuma babu wata shaida da zaka gani a jikinsu kace sune wadannan balle ka gujesu. Amma dai koda yaushe ana samun wadanda aka tsafe, wasu a sume, wasu kuma an kawar da hankalinsu sai dai a mayar dasu gida don basa iya tuna abunda ya faru.
Duk yadda suka boye kansu amma ansan wasu daga cikin daliban ana korarsu amma koda ankori iri-irinsu sai kaga sun sake yaduwa fiye da da. Kullum a tsorae muke musamman da daddare, anan ana tsoron fitar dare saboda aljanu, acan kuma haka ake tsoron fitar dare saboda matsafa. Idan kaga yarinya ta kwanta bacci anzo an tasheta bata tashi ba, a girgizata, a dauko ruwa a sharara mata bata farka ba. Daga karshe a dauko reza a tsattsaga jikinta ko motsi baza tayi ba. To *yar kungiyar ce kuma gangar jikinta ce anan ruhinta ya tafi wajensu. Sai sanda kurwarta ta dawo sai tayi firgigit ta tashi taji tsumu-tsumu cikin ruwa taji radadi wajen da aka tsaga mata. Duk a gabanmu muke ganin irin haka dan haka kusan kowa bai yarda da kowa ba, ko kawa ba'a cika yi ba kuma ba maicin abun wani. Sai dai in tuntuni kasan mutum. Wala gidanku daya ko *yan uwa ko gari guda, ko kun zauna kun saba ka karanci mutum ka yarda dashi.
Sai na mayar da alewar hannuna cikin leda na daure ledar na jefa ledar na jefa kan akwatina na fasa sha. Ga bakar yunwa ina ji amma wani barci mai nauyi na ba gaira ba dalili ya ruftomin ko idona bana iya budewa, tun ina jingine akan filo harna mike na kwanta akan gado nayi ta barci mai nauyi. Bazan iya fasalta yadda naji ba kamar a mafarki, kamar a ido biyu naga wasu irin mutane sun zagaye gadona mata da maza, manya magidanta ba dalibai bane, da kuma daliban har da uniform irin namu. Sannan *yan kananan yara *yan primary duk suna ta dariya da karfi mai tsoratarwa. Babbansu wani tsoho tukuf cikan harshen turanci ya ce mun "Rufkatu sannu da zuwa cikinmu, yanzu kin zama mu mun zama ke. Zamu yi miki arziki, farin jini, mu kara miki kyau da kwarjini da ilimi zaki ji dadin rayuwarki. Amma kada ki bi ko wanne addini domin bama son addu'a kowacce iri ce. Sai naji na ce "Bana sanku kuma bazan shiga cikinku ba. Ya jawo wata budurwar yarinya gabansa ya ce mata bude idonki ta ganki. Sai budurwar ta yaye wani gyale da ta rufe idonta sai naga wannan senior ce da ta bani biskit da alewa dazu. Sai ta ce "To meya sa kika ci alewa da biskit dina, ki biyani. Saina nuna mata kan akwati na ce gasu can ban ci ba, dauki kayanki. "Suka kwashe da dariyar mugunta suka ce "Rufkatu aikin gama ya gama ki bamu uwarki ko ubanki mu kashe. Na firgita amma na rasa addu'ar da zanyi a cikin addinina na kasa tuno addu'a daya da zanyi dan babu addini daya dana tsayar har in koyi addu'ar neman tsarin makiya da akeyi, sai na fara kwalla kara mai firgitarwa. Babbansu yasa hannuna ya kama gashina ya dinga cukurkudawa ina ihu kamar raina zai fita. Ni dai na bude ido naga *yan dakinmu gaba daya a kaina ana tambayata ihun me nake yi. Ban iya basu amsa ba naci gaba da ihu kamar zan tsaga kunnuwansu don a firgice nake ba zan iya tuna abunda ya faru ba ga tsananin ciwo da jujjuyawar da kaina yake mun. Dalibai suka dunga zazzagamun addu'a, ban daina ba sai aka je staff quarters aka kira malamai suma suka zo suka fara tasu. Saina daina ihun na fara wani bacci mai kama da mutuwa. Kwanana daya da yini daya a gadon asibiti ana karamun ruwa ban farka ba. Aka nemi wayar gidanmu ba'a samu ba a lokacin an rufe layin. Sai aka daukeni aka kaini wurin addu'a a garinmu ana ta cigiyar Iyayena. Nan da nan Mahaifiyata taji labari ta garzaya wurin taga ni din ce kuwa. Sai ta fashe da kuka, ganina cikin wannan hali . Ta tambayesu meya sameni suka bata labarin abunda ya faru. Sai tasan wannan ciwon nawa bana asibiti bane. Saita daukeni ta tafi dani wajen bautarsu. Nan fa suka dukufa da yi min addu'a ba kakkautawa ba dare ba raba ga karin ruwa ana yimin saboda bana ci bana sha a sume nake kawai a kwance kamar gawa numfashi kawai nake yi da an binneni, har tsawon kwananki biyar a haka a kwance. Mahaifina da yaga haka shima ya hado Malamai musulmai suka hadu har Hamma Huzaifa duk suka dauki Alkur'ani suka yi ta saukewa a kofar gidanmu. Ana yanka ana sadaka, addu'a bata faduwa kasa saina farka na bude idona.

Iman ta fashe da kuka haka *yan wajen sai hawaye ya dinga zubo musu. Sai girgiza kai suke dan tausayi. Ta jima tana kuka kafin taci gaba tace.

Nasha wuya, nasha wuya a wannan lokacin domin sai dai ban kwanta barci ba na dinga ganin wadannan mutane suna firgitani. Daga karshe Mamana ta hakura da makarantar aka dawo dani ta jeka-ka-dawo a nan jalingo ina zuwa ina dawowa gida a hankali-ahankali kuma ana yimin addu'a daga dukkan bangaran uwata da ubana, Hamma Huzaifa har rubutun kur'ani yake min yana kirana a boye yana bani ina sha yace kada in fadawa Mahaifiyata. Sannan nabar ganinsu a mafarki na dawo hayyacina kamar da. Naci gaba da harkokina kamar kowa kuma ina jin dadin sabuwar makarantar ta jeka ka dawo. Amma naci gaba da bincike akan addinai kuma ina zuwa wajen kawayena Mumuyawa kullum bayan na dawo daga makaranta, haka ban daina zuwa dakin bautar mai aikinmu ba Tabita ina ganin yadda ake bautarta ina yi mata tambayoyi. Kuma dolen-dolena in bi Mahaifiyata wajen bautarta duk ranar yin bauta. Musamman yadda Mahaifiyata ta sami karin girma ada aka bata mukami saboda saninta, da kwazo a bin addininta. Dukiyarta, jinin jikinta da duk lokacinta duk ta sadaukarwa addininta. Ta kai ta kawo duk ranar bauta bayan an tashi daga wajen bauta su Mahaifiyata suna shiga motoci su shiga kauyuka da burane suna wa'azi suna kira zuwa ga addininsu.
Na fara zama budurwa na kara wayo da hankali. Ina zama da Hamma Huzaifa a kofar gidansu lokaci-lokaci da yamma idan na dawo daga makaranta naga Mummy bata nan, kuma idan bana son zuwa wajen kawayena da abokaina Mumuyawa. Shi daman Hamma Huzaifa kullum da yamma idan yana gari bai koma makaranta ba a kofar gidansu yake shimfida darduma ya zauna yana karatun kur'ani, a lokacin yana karatu a FUTY jami'ar dake Yola. Sai inzo in zauna in yi ta sauraronsa domin karatun yana yimin dadi kuma ina sha'awa in koya. Idan ya shafa addu'a sai mu shiga hirar duniya a hankali sai mu gangaro hirar da muka saba ta addini. Na ce "Hamma Huzaifa ka bani addu'ar kariya idan abun tsoro ya tunkaroni. Sai ya koyamun ayatul kursiyyu, falaki da nasi, duk da nasha wuya kafin in koya amma na nace dakyar na koya da sudin goshi kuma na dauki lokaci mai tsawo kafin na iya sosai.
Watarana ina aji hudu na secondry ni da kawayena mun fito daga get din makaranta an tashi zamu gida saina ji dik mutum ya diro a gabana ina tafiya na tsaya cak sai naga wannan budurwar data bani alewa da biskit amma a suffar abun tsoro tazo mun, farata zaka-zaka da hakora. Ta mika hannu zata tabani na tsorata na fadi kasa ina karkarwa, sai Allah Yasa na tuno da addu'ar da Hamma Huzaifa ya koya mun saina fara karanto ayatul kursiyyu ta kasa tabani saita bace. Wadanda muke tafiya basu ganta ba ni kadai na ganta sunga kawai na fadi kasa ina karkarwa har sun wuce suka dawo suka tashe ni muka tafi. A lokacin na sake sakawa raina ina son Musulunci addinin gaskiya ne. Na ci gaba da bincike da koyon abubuwa a cikin addinin a wajen Hamma Huzaifa ko kannensa idan baya nan. Ko kuma kawayena Musulmai. Watarana in shiga library makaranta bangaren littattafan addinin musulunci in buya inyi ta karantawa. Ina da kokari a makaranta sosai don haka ina S.S 2 na zana jarabawar S.S.C.E tare da *yan S.S 3 kuma na cinye dukka. Mahaifana sunyi murna sosai, ba tare da bata lokaci ba Mahaifina ya samarmin addimission a ATBU yace can zanje idan naje Yola bazan yi karatun kirkiba saboda akwai *yan Jalingo da yawa kuma kusa da gida ne gara nesa. Da farko na damu sosai kawayena Harriet da Janet suka ce kar in damu dukkansu jami'ar ATBU zasu tafi saimu hadu kawai a can, sannan naji hankalina ya kwanta. An bani course din da Mahaifiyata ta karanta achetecture naji dadi Iyayena ma sunji dadi. Kafin inje registration saida Mahaifiyata da Mahaifina dani muka je London da China yawan shakatawa kamar yadda koda yaushe suke yimin alkawari idan na gama secondry naci jarabawata zasu kaini kasashen waje. Munyi sati hudu acan sannan muka dawo. Alokacin har naso in makara saboda an koma makaranta har an kusa rufe rigistration.
Chapter 20 · 0% Book details