Sashe 50
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 6 min read
na bashi kudin jirgi? Baba ya fada yayin da mamaki ya kamashi, Baba ya juya ya nufi gida da sauri ya shiga dakin su Najib shi ai zai san inda Suhaif din ya tafi, tunda bakinsu daya. Najib yayi dai-dai akan gadonsa yana shakar bacci bai san ma inda yake ba, sai da Baba yayi ta dukan hannunsa sanna ya farka. "Ina Suhaif? Baba ya tambayeshi. "Gashi can a gadonsa yana bacci. Najib ya fada cikin magagin bacci. Baba ya ce "Kai bude idonka. Ina Suhaif din yake? Ba ga gadon nasa babu kowa akai ba. Sai Najib ya tashi ya zauna yana murtsike ido yana soshe-soshe ya ce "To ban san inda ya tafi ba. Baba ya fusata ya fara fada yana cewa "Na fara gajiya da irin wannan rashin jin naku, kamar wasu kanana. To idan baku gyara halin nan naku ba zan cire hannuna akan ku kowannenku yaje ya nemo aikinsa. Yanzu yanzun nan daga Lagos aka yi min waya yau ake neman su Suhaif, tun jiya ya kamata yaje ya kwana acan yau litinin za'a tantancesu amma ya shiga mota ya tafi yawonsa kawai. Najib ya yunkura zai tashi sai yaji ya dafa wata takarda a gefensa, ya dauko ya bude yana karantawa sai mamaki ya kamashi gami da fargaba. Baba ya dube shi ya ce "Me aka rubuta? Najib yayi shiru can ya ce "Suhaif ne ya bar wasika ya ce ace maka ba zai iya aiki ba saboda tsananin damuwar da take damunsa ko ya fara aikin ma zasu gaji su kore shi. Don haka ya je nemo maganin damuwarsa shine ya tafi garin su Iman nemanta. Yadda ku kasan ruwan zafi ake watsa masa haka Baba yake jin labarin da Najib yake bashi. Sai ya hau balokoko yana fada, ya fito daga dakin ya nufi dakin matarsa itama ya hada da ita cewa yake laifin ta ne, ita ta sakarwa yaran suke abunda suka ga dama. Naja'at da Zubaida suma suka fito Mama ta kasa bawa mijinta hakuri saboda ransa yayi matukar baci. Suhaif dai ya kama hanya sai tafiya yake haikan ya tafi neman abar kaunarsa, ya bar *yan gida da shan fada ko ruwan shayi ya gagaresu kurba a safiyar yau, yau dai laifin wani ya shafi wani. Suhaif ya isa Jalingo da magaruba, baiyi wata-wata ba ya zabi hotel din da yake so ya biya aka bashi daki, bayan anyi masa odar abinci yaci yasha, sanna yayi sallah yayi wanka ya kwanta amma tunani da murna sun hanashi bacci. Murnar ita ce yau gashi a garin su Iman dan haka yana da 50% din tabbacin ganinta. Tunanin kuwa shine ta ina zai fara nemanta? Gari kamar Jalingo ace an zo neman mutumin da ba'a san inda yake ba. Shi ba attajiri ba, ba dan siyasa ba wanda da zarar an fadi sunansa kowa ya sanshi. Allah gani gareKa. Suhaif ya fada lokacin da yake ta juyi akan gado. Washe gari da sassafe Suhaif ya shirya ya fito neman abunda ya zo nema, da farko cewa yayi a nuna masa G.R.A. An kaishi G.R.A sunfi a kirga amma Allah baisa ya ci sa'ar ganin gidan su Iman ba. Ya yi kwatancenta, ya nuna hotonta, ya fadi sunayenta da ake kiranta dasu kakaf amma bai sami wanda ya santa ba. Har dare ya yi sanna ya koma dakinsa na Hotel ya kwanta, cike da bakin ciki. Haka washe gari ma da sassafe ya fita, amma yau wajen bauta ya nema ya dinga zazzagawa yana fadar sunan Mahaifiyarta da Mahaifinta basu sansu ba. Washe gari kuma ya nemi asibitoci yana tambayar Dr. Hani ko Allah zaisa yaga Dr. Hani ko a lokacin daya zukewa yaron Iman abu daga hancinsa ya rubuta adreshinta, bai samu inda Dr. Hani yake ba, anan ma har dare. Washe gari kuma kauyukan Mumuyawa ya yini, anan ne kuwa yafi shan wuyar banza. Ba sa jin yarensa, baya jin nasu, basu fahimci kalma daya ba daga cikin abubawan da yake tambayarsu. Sai suka zamar dashi a bin kallo, wasu kuwa ganin ya tunkaro su a mota sai su zura da gudu. Dole ya hakura ya dawo dakinsa na Hotel cike da takaici da dacin bakin ciki. Bai hakura ba sai ya shirya washegari ya nufi kasuwanni ko Allah zaisa yaga Iman, nan ma ya yini yana kallon masu saye da sayarwa babu Iman babu mai kamarta. Ranar da ya cika sati guda a Jalingo ya saduda ya hakura ya hada kayansa a jakarsa ya biya masu Hotel ya fito ya nufi hanyar Kano. Hawaye sharaf-sharafa fuskarsa saboda bacin rai gashi a garin su Iman amma ya rasa inda take. Ya iso Kano da misalin karfe shidda na yamma saboda irin gudun da yake zurawa don bacin rai, bai damu da ko motar zata fadi ba, ko yayi karo da wasu motocin, ya fitar da rai da son ci gaba da rayuwar duniya. Mai gadi yana bude masa get ya kutsa ya shigo cikin gida a fusace. Yaga *yan gida kakaf har da *yan Doko suna zazzaune a farfajiyar gidan, daga dukkan alamu tafiyarsa ta tayar musu da hankali, da rashin dawowarsa kwana da kwanaki. Ya je inda ake ajiye motoci yayi parkin ya dauko jakar kayansa ya rataya ya nufo inda suke ransa a bace yake kamar yadda yaga rayukan iyayensa a bace har da masu wurgo masa harara. Ya karaso inda suke ya duka ya gaishesu, babu wanda ya amsa masa, sai Naja'at da Zubaida ne suka yi masa sannu da zuwa Najib ma dauke kai yayi baya ma kallon inda yake. Shima sai ya share, zai wuce cikin gida, Mahaifinsa Baba na Doko ya daka masa tsawa ya ce "Kai sha-sha-sha ina zaka je ne? Da wo nan kayi mana bayanin daga ina kake, suhaif ya dawo ya tsaya yayi shiru bai ce komai ba. Baba na Kano ya ce da Suhaif "Zo nan gabana, Suhaif ya zo ya durkusa, suka fara masa fada su duka hudun wato har da Goggo da Mama, har ma baya gane abun da suke fada domin carin yayi masa yawa. Naja'at da Zubaida suka tashi suka shiga gida suka labe, saboda kada a gama masa fada ya huce a kansu, gannin wata uwar harara da yake jeho musu. Najib ma yake tsoma baki a fadan. Suhaif ya zabura ya ce "Dalla Malam ka rufe mana baki ka bar wadanda suka isa suyi min fadan ba kai ba, Najib ya ce "Ai gaskiya ake fada maka, gashi nan akan Iman ka rasa aikinka, wata kilama baka ganta ba. Baba na Kano ya ce "Ni dai ka kunyata ni, abokina ne manajan na rokeshi arziki ya daukeka aiki, ya kukuta ya soka ka amma shine ka gudu a ranar da ake nemanku. Baba na Doko ya ce da Suhaif "To kar ka shiga cikin gidan nan ka koma inda ka fito kaje can ta baka aikin tunda ka rasa wancan aikin da aka sha wuyar nemar maka, babu gidan wanda zaka je ka kwanta ana ciyar da kai. Suhaif ya ce "Kuyi hakuri dan Allah, nasan nayi laifi ku yafe min, Baba na Doko ya ce "Babu zancen hakuri wallahi sai kabar gidan nan yau, kuma kar ka je Doko, Suhaif ya mike ya saba jakarsa ya nufi wajen motarsa ya shiga.