← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 80

Sashe 34

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tunanina da Micheal yaji zancen kotu zai fadi gaskiyar abunda ya faru, cewar bani ya yiwa ciki ba kawata ce kuma ta mutu a garin haihuwa na dauki yaron. Sai naji Micheal ya kaikaice ya narkar da murya yana bada hakuri wai haka Allah Yayi, ya san bai kyauta ba da yayi sanadiyyar hanani karatu. Amma son da yake min ne ya ja haka, yanzu ya zo ne ya ga dansa ya kuma kawo masa kayan haihuwa kuma a radawa dan suna kuma in da za'a yadda a bari ya aure ni don mu rungumi dan mu. Kuma ya dau alkawarin zai rike ni da dana amana cikin wadata da kulawa kuma zai dau nauyin karatuna tun daga degree har sama da haka idan ina so kuma a kowacce kasa kuma ko nawa za'a kashe. Tashi daya kalaman mayaudari Micheal ya sanyaya zuciyoyin Mahaifana, suka ji lallai Micheal ya dace abi shawararsa. Shine kadai mafita tunda ga da waye kuma zai aure ni da dan wani, gara ubansa. Daman babban takaicin shine karatuna dana rasa amma yanzu gashi na samu mai nemomin makarantar fiye da ta da, ai shikenan. Mahaifiyata ta gyara zama ta ce masa "Micheal meye addininka? Ko da ya fada mata, taji addininsu daya sai suka hau dogon kwatance. Daga karshe sai ta gane Mahaifiyar Micheal mai bi ce sosai itama, shugabar wani babban wajan bauta ne a Bauchi. Tun Mahaifiyata tana ATBU nan take zuwa bauta duk ranar bauta. Zata iya tuna Micheal lokacin yana yaro karami. Lallai Micheal ya fito daga gidan manyan mutane, ga arziki ga addini. Farin ciki ya rufe Mahaifiyata daman ita babban burinta taga na auri miji wanda ba Musulmi ba domin ta kula dani bana son addininta. Huldata da Hamma Huzaifa ma bata so, saboda ta fuskanci akwai ranar da zata ji wani labari na game da aure a tsakaninmu domin shakuwar da kaunar junanmu tayi yawa. Ashe ita wannan Jaririn gaba ta kaita wai gobarar Titi a Jos.

Hmmm ku huta da karatu anan
Wanda ba su ga farkon na biyu ba su shiga wajen "Show More" yayi kasa zai gani

Reedwan Suraj Isma'il

________________ YARENA ADDININA.
___CI GABAN LABARI

Mahaifina baiyi magana ba daga dukkan alamu wannan labarin auren baiyi masa dadi ba. Baiyi niyyar aurar da ni yanzu ba nayi kankanta a lokacin shekaruna goma sha biyar. Amma yaya zaiyi na dauko goyo? Gara in tafi can da dan mu karata. Mahaifiyata na cikin farin ciki ta kwallawa Tabita kira ta ce "Ta kawo musu ruwa da lemo. Micheal ya cewa abokinsa ya je mota ya dauko akwatina da kwalayen da yayi mana shopping.
Matukar bacin rai ya darsu a raina bansan sanda zuciya ta fito dani falon ba na tsaya a tsakiyar falon gaban Micheal da Mahaifana na ce "Micheal karya yake yi bani ya yiwa ciki ba kawata ce. Don haka bazan aure shi ba. Mamaki marar misaltuwa zaka iya gani a fuskokinsu su duka. Mahaifiyata ta daka min tsawa ta ce in tafi in basu waje kar in yiwa mutane rashin kunya. Wana dauka kananan yara? Ai ana ganin Jaririn anga ubansa. Ita kawar tawa bata da hannun rike dan sai ni zan rike mata? Mahaifina ya ce to ai wannan maganar bata sauraro ba ce ya akayi na bar makaranta na shiga gari? Har kuma ina musu ina cewa ban haihu ba. Babu yadda za'ayi in dauko dan wata in tinkaro gidanmu da shi da sunan dan kawa. Micheal ya hau rantse-rantse har da sa hannu a aljihu ya dauko wasu hotunanmu daya ni da shi, daya kuma ni da shi da abokinsa, don ya iya munafunci bai dauko na ni da shi da su Harriet ba. Takaici yasa na nufi gidan Mama Tabita da gudu ina rusa kuka. Babu yadda zata yi da ni sai lallashi ta ce min inyi hakuri. Bubby kanina ya shigo ya iskemu cikin wannan hali ya dube ni duban tausayi ya ce "Aunty Rufkatu ki daina kuka kiyi hakuri, Mummy ta ce ki kawo Jaririn babansa zai ganshi. Tabita ta miko hannu zata kwance shi daga bayana na fisge na ce "Bazan bayar ba, Mama Tabita Micheal mugu ne baya tsoron Allah, shi yayi sanadiyyar mutuwar Mahaifiyar yaron nan yanzu kuma dan zai kashe, daman ya fada sai ya kashe dan duk ranar da aka ce dan sa ne. Bubby ya bude baki yana kallona cike da mamaki. "Kamar yaya Micheal yayi sanadiyyar mutuwar Mahaifiyar dan, ba kece mahaifiyarsa ba? Ya tambaye ni. Na sake rusa kuka na ce "Bani ba ce Bubby yayi wuf ya fice ya nufi gida yana zuwa ya tarar da Micheal da Mahaifanmu a falo a inda ya barsu, ya dubi Micheal ya dubi Mahaifiyarmu da ta aika shi ya ce "Ta ce ba zata bada yaron ba Micheal mugu ne shi ya kashe Mahaifiyar yaron ya ce sai ya kashe yaron shima. Nan fa aka hau kallon-kallo, Micheal ya hau zare guru-gurun idanuwansa tamkar bai gane abunda nake nufi ba sharri nake masa. Mahaifina cike da mamaki ya ce "Wai meke faruwa ne, me yake damun Fatima ne take magana kamar tababbiya? Micheal fada mana gaskiya me take nufi? Mamaki marar misaltuwa zaka iya gani a idon Micheal ya ce shima bai san me Pretty take nufi ba, shi dai abinda ya sani shi ne yayi mata ciki, ciki yayi wata tara, da hannunsa ya kaita asibiti ta haihu yana shirin ya siyo musu kayan haihuwa ya kawota gida, ta gudo tazo tana nunawa kamar bata sanshi ba yanzu. Mahaifiyata ta fusata ta mike ta nufi inda muke tana fada tana cewa "Na zamar dasu kamar wasu yara kanana yaushe aka haifeni da zan musu wayo in nuna ma bani na haifi yaron ba, don haka duk ranar da na kara duban kwayar idanuwansu na ce ba nice Mahaifiyar yaron nan ba saita fasa min baki. Ta tunkaro inda nake tsaye a fusace, a zatona ma dukana zata yi saina rufe fuskata da hannuna Tabita ma jikinta ya dau rawa ta taso tana bata hakuri sai na ji ta fisge goyon daga bayana ta tafi da yaron wajen Micheal. Na sulale na zauna a kasa don takaici da radadin da zuciyata take yi. Tabita na bani baki akan kar in damu kar in sake yin musu akan bani na haifeshe ba in barsu haka. Na ce "Mama Tabita zancen aure fa suke yi, wai tunda ga da a tsakani zai aureni mu rike danmu. Tabita ta ce "To ai babu komai ki aure shi Rufkatu, yaro ne mai hankali mai kyau kuma, kin fada mun yadda yake matukar sonki tun farko ma ke yake so ba Harrier ba zai rikeki sosai tunda yana sonki. Na girgiza kai hawaye bai daina zuba ba nace "Ba zan iya auran Micheal ba Mama Tabita Micheal dan iska ne, macuci ne, bashi da tausayi ko kadan, dan fashi ne, duniya yasa a gaba babu addinin da yake yi. Haka Tabita ta tsaya a kaina tana kallona tamkar sassakakken gunkin da take bautawa, daga dukkan alamu ta fara zargina da yiwa Micheal kazafi saboda kiyayyar da nake yi masa.
A can falo suka yiwa jaririn adddu'a irin tasu, suka sakawa yaron suna Citibin. Micheal ya dauko Camara ya daddauki yaron a hotuna kala-kala, ya dauki Mahaifiyata da Mahaifina da Jaririn a hoto, sannan abokinsa ya dauki Micheal da dansa sannan ya dauki Micheal da dansa da Mahaifana a hoto. Daga karshe suka yi addu'a, Micheal yayi musu sallama akan da zarar yaje gida zai sanar da Mahaifiyarsa ya gano inda Pretty take da Jaririnta dan hankalinta ya tashi daya sanar mata Pretty ta gudu kuma baisan garinsu ba. Ya ci gaba da zuba musu karya ya ce itace tace lallai-lallai yaje ya nemo Pretty duk inda take. Yanzu kuwa zata fi kowa jin dadi idan taji labarin ya ganta ita da Jaririn suna cikin koshin lafiya. Kuma zai daukota su zo taga yaron sai ayi zancen aure. Mahaifiyata taji dadi kwarai saboda zata hada zuriya ko kuma ma in ce ta hada zuriya da babbar Malamarta a wajan bauta, mai tsananin yiwa addininsu hidima da dukiyarta da jikinta wato Mahaifiyar Micheal. Dari bisa dari taji aurena da Micheal ya kwanta mata a zuciya. Mahaifina kuwa ba yabo ba fallasa, ba haka yaso ba wai kanin miji yafi mijin kyau. Bashi da zabi tunda matarsa sai yadda tayi dashi, jikinsa yayi sanyi kalau dan yasan ba'a yin haka a addininsa na da, mace ta haihu a titi ba tare da anyi mata aure ba. Mahaifiyata ta kwallawa Tabita kira tazo ta dauki dan Jaririn da lubgin kayan da Mahaifinsa ya sayo mana kala-kala ta ce a kawo min. Nayi farin ciki da kayan Jarirai *yan waje dan daman yana fama da rashin kaya, bayansu kuwa duk sauran basu burgeni ba. Leshinan da atanfofin basu isheni kallo ba, saidai madarar Jarirai suma ya burgeni da yayi tunani ya siyo, dan kuwa yasan yaron ba uwa gareshi ba balle yasha nono.
Haka na kasance kukan dare daban, na rana daban, na yamma daban. Ko gidanmu bana son shiga ina nan nane da Mama Tabita, ita kadai ta rage mun mai kwantar mun da hankali ta bani hakuri idan ina kuka, ta tausaya mun halinda nake ciki. Na kanyi kuka na musamman idan na tuna babban rashin da nayi na Hamma Huzaifa, ina tsananin jin takaicin ya tafi da bakin cikina a ransa, na ganina da jariri ba tare da na wayar masa da kai ba cewar ba dana bane, kuma fadan da yake mun, naji fadan ban taba aikata zina ba. Huzaifa ne abokin hirata mai kokarin amsa min tambayoyi, mai kaifin basirar yanke mun kyakkyawan hukuncin duk wata matsala data dameni. Allah baya barin wani dan wani. Ya daukemun Huzaifa.
Chapter 34 · 0% Book details