← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 80

Sashe 78

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 4 min read

Micheal ta ce "Ibarahim yanzu tunda ka dogara da Allah, ka yarda shi kadai ne mai iko, mai bayarwa, mai hanawa. Bari ka gani ma tun daga yanzu. Iman ta tashi ta fita ta je lungun data boye Muhammad ta kamo masa hannunsa suka zo wajen Micheal. Micheal ya kurawa yaro ido, yaro ya kurawa Micheal ido. Micheal ya ce a ransa "Ya aka yi wannan yaron yake kama dani? Cike da mamaki Micheal ya dubi Iman ta ce "Waye wannan yaron? Iman ta ce "Dan Harriet ne kuma danka ne bai mutu ba. Micheal ya dora hannu aka ya fasa kuka share-share da hawaye. Jikinsa ya dau karkarwa yana yiwa Iman godiya ya ce "Yadda na zama dana ba zai iya taba ni ba dana rungume shi naji sanyi a raina. Ni kadai na rage a duniya yanzu Pretty bani da Uwa ba Uba, babu dangi. Ashe ina da da a raye? Na gode Pretty. Iman ta ce "Ka godewa Allah. Iman ta dubi Muhammad ta ce yaje ya gaishe da babansa, Muhammad ya yatsune fuska ya ce "Wannan ne Babana? A'a ga Babana nan. Ya nuna Ibrahim, dakyar suka kamashi suka kaishi wajen Micheal. Micheal ya shafa kansa yana kuka. Micheal makale da sandarsa biyu ya rako su bakin mota suna ta bashi baki da shawarwarin yadda zai gudanar da rayuwarsa. Da yadda zai aiwatar da addininsa. Iman ta dubi Mansur wanda har yanzu yana shafa wuyansa inda yasha shaka. Ta ce "Mansur yi hakuri, ka taimakeni ka taimaki rayuwar Micheal, kaga kai Musulmi ne. Micheal ya Musulunta, ka shiryu shima ya shiryu ya daina fashi ka zama abokinsa don rayuwa baza tayi dadi ba mutum daya bashi da kowa babu mai zuwa wajensa. Ka koya masa wankan shiga Musulunci, sai ka koya masa alwala da sallah. Idan kaima baka iya ba ka kaishi a koya masa ko kuma zan baku kudi a dauki Malami ya dinga koya masa. Zan baku kudi ku gyara kanku da muhallinku. Ta juya ta kalli Micheal ta ce "Ka yi min alkawari baza ka kara shan giya ba, fashi, neman mata, balle ka datsewa mutane kafa ko kisa. Kamin alkawari baza ka bar Musulunci ba kuma zaka rike addininka duk abunda Musulmai suke yi kamar salla, azumi, da hakuri zaka yi. Sannan kamin alkawari kudin da zan baka zaka gyara gidanka da jikinka da kuma abinci mai kyau. Micheal yayi murmushi ya gyada kai ya ce "Nayi alkawari zan yi duk yadda kika ce, ko bayan idonki ne. Iman da Suhaif suka shiga mota suka yi shawarar nawa ya dace a bashi. Kudi mai dumbin yawa suka bawa Micheal ya bude baki yana mamaki sai juya damin-damin kudin yake yana godiya. Iman ta ce "Ka sayi wayar hannu zan baka lambar mijina idan ka hada wayar sai ka kiramu. Ya amsa mata da "To zan saya. Mansir ma ya hau murza hannu don har kaikayi hannunsa ya fara yi tun kafin nasa kudin ya shiga hannunsa. Iman ta mika masa nasa duk da na Micheal yafi yawa amma yayi murna bai taba zata zai sami haka ba. Shima yayi mata alkawari zai tsaya tsayin daka ya ga ya taimaki Macheal akan komai ma ba addini kawai ba. Mansur ya shiga mota su Iman ma suka shiga suka tafi. Micheal yana daga musu hannu har suka tafi. Gidan Fadila Mansur zai nunawa Iman. Suka isa bakin get din gidan, lallai kuwa attajiri Fadila take aure. Iman ta ce su jira bari ta shiga ciki ta gani. Iman na shiga falon gidan ta tarar da Fadila a zaune a falo tana da tsohon ciki, ga karamin yaro zaune akan cinyarta da samari guda biyu suna zazzaune dukkansu suna kallon talabijin. Fadila ta amsa sallama gami da dago ido tana kallon mai shigowa. Fadila ta zabura ta sauke yaron dake cinyarta ta mike tsaye cike da mamaki ta tambaya "Wa nake gani kamar Pretty? Iman ta ce "Ni ce Fadila. Suka rungume juna saboda murna. Fadila ta kama hannun Iman ta ce "Zo ki zauna kawata Allah mai iko, ba dan ikon Allah ba da koda kudina ina zan nemeki? Iman ta ce "Kafin na zauna bari na shigo da baki a waje, mai gidana ne da wasu guda biyu. Fadila ta ce da samarin nan "Bishir jeka waje ka shigo da baki maza ka kaisu falon Babanku ka nuna musu bandaki. Iman ta ce "Sai ka shigo min da karamin yaron nan. Bishir ya amsa da "To Aunty, ya fita waje. Fadila ta ce "Kafin mu gaisa bari nasa masu aiki su harhado muku abinci. Bayan shigar Fadila kicin ba dadewa ta dawo wajen bakuwarta. Iman ta ce "Sallah nake so in fara yi. Fadila ta ce "To bari mu shiga daki. Suka dunguma zuwa katafaren dakin barcin Fadila, Fadila ta dubi Muhammad ta ce "Pretty danki ne wannan kuwa? Kai bayan rabuwarmu bai ci ki haifi wannan ba. Iman ta ce "Bari inyi salla zaki sha labaru. Kafin Iman ta idar da salla masu aikin Fadila sun jere musu abinci kala-kala da abun sha. Haka suma su Suhaif an kai musu nasu.
Chapter 78 · 0% Book details