Sashe 49
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
A falon Baba suka hadu ana ta hira, wasa da dariya ga Mahaifiyar Najib itama tana taya su godiya. Ta ce "Baban Najib sauran *yan matan Naja'at da Zubaida gashi suma kwanan nan zasu fara zuwa B.U.K kamata yayi suma a saya musu *yar karamar mota irin ta *yan mata koda guda daya ce su biyu a daukar musu direba ya koya musu. Bai musa mata ba sai ya ce "Suma na aika Germany a cikin motocin da za'a auno min za'a taho dasu Civic kowacce tata daban saboda idan ma aure suka yi su tafi da kayansu gidan mijinsu. Gaba daya falon ya hargitse da murna. Suhaif ya sake dukawa yayi godiya ya tashi ya nufi dakinsa, yana murmushi a baiyane kada a gane labarin da yake zuciyarsa. Hakika Suhaif yaji dadi sosai da wannan abun arzikin da Baba na Kano ya birgesu shi da *yan uwansa, amma babu wacce ta fado masa sai Iman dama da ita zasu ci arzikin nan tare, yaji a ransa dama Iman tana nan su shiga motar tare, a zahirin gaskiya yaji baya son motar nan tun da ba Iman. Sai ya ji kuka ya kamashi ya kulle kansa a daki ya sha kukansa shi kadai yayi ya gaji. Bayan Doko daya tuka yaje ya nuna musu ya dawo babu inda yake hawa motar yaje kullum yana gida a kwance a daki. Ba kamar Najib ba ai shi tun ranar da aka danka masa mukullin motar idan ya fita da safe sai da yamma zai dawo ya ci abinci, yayi wanka, ya canja kaya ya sake fita sai karfe goma na dare kuma. Har yawon Najib ya fara damun Mamarsa tana masa fada tana masa misali da dan uwansa Suhaif baya fita ko ina kullum yana gida. Don an saya maka mota cewa akayi ka fita yawo da abokai? Sannan Najib ya fara dan zama a gida. Shi dai Suhaif ya zama tamkar mutum-mutumi a gidan bashi da tunani, bashi da abun yi sai ina zaiga Iman? Dama ya ganta, ko a wanne hali take ciki yanzu, yaya za ta kasance da Iyayenta? Aikinsa kenan tunaninta. Suhaif na kwance kan gadonsa, daya daga cikin masu aikin gidan ta kwankwasa masa kofa ta ce da shi ya zo Baba na kiransa. Ya tashi ya nufi falon Baba ya iske shi shi kadai bayan sun gaisa ya tambaya "Ina Najib? Suhaif ya ce "Baya nan, Baba ya gyara zama ya shaidawa Suhaif cewar Naja'at da Zubaida sun sami admission a B.U.K. Zubaida ta sami Geography, Naja'at kuma Biochemistry. Suhaif ya yi murmushi gami da yi musu addu'ar fatan alkhairi da sa'ar farawa da gamawa lafiya. Sai Iman ta fado masa arai saboda su uku suke tare, gashi su biyu zasu fara Jami'a ya yiwa Iman sha'awar dama da ita. Jikinsa yayi sanyi idonsa ya ciko da kwalla amma bai bari Baba ya gane ba. Baba ya ci gaba da cewa "Don haka ka shirya kaje Doko ka dauko su Naja'at domin an ce min har an fara bayar da admission letter. Suhaif ya amsa da "To Allah Ya kaimu goben, sai Baba ya sake cewa "Ga wani sabon albishir din, na so ace kai da Najib kuna tare ku bani goran albishir. Suhaif ya tattara hankalinsa gaba daya yana sauraran abinda Baba zai fada cike da zumudi, babu abinda yake fata irin dama ya ce masa Iman ta dawo Doko. Amma sai ya tuna ashe Baba na Kano bai san Iman ba, sai dai Mama ta bashi labarin abubuwam da suka faru, da yake bashi da son labari a nan ya watsar bai sake tayar da maganar ba. Baba ya katse masa tunani ya ce "Kun sami aiki kai da Najib. Kai a Nigerian Port Authority Lagus, Najib kuma a Union Bank Kano Branch. Suhaif ya kurawa Baba ido yana kallonsa tamkar hoto. Wani tunani ne ya fado masa, yana tuna ranar da Iman ta hada masa takardunsa na neman aikin a wani file. Da hannunta ta rubuta masa takardar neman aiki da Baba ya ce su rubuta, ita kuma da kanta ta zaba masa inda zai zaba. Har Iman tana tsokanarsa tana cewa "Idan suka daukeka aiki a NPA kafin shekara ka zama mai kudin gaske, zaka yi mana wahalar gani sai mun cike form. Yau ga aikin ya fito amma Iman bata nan. "Kai lafiya, meke faruwa? Ka zama kamar gunki, tunanin me kake? Baba ya tambaya. Suhaif ya sunkuyar da kai kasa yayi shiru ya kasa magana, "Suhaif wai me yake damun ka ne, kwana biyu naga alamar akwai abinda yake damunka har ya shafi walwalarka baka son shiga mutane kullum kana kwance a daki shiru? Baba yake tambayar shi. Suhaif ya boye masa ya ce "Babu komai Baba, Baba ya ce "Akwai wani abu Suhaif, karka boye min ka fada min ko maye. Ko sai Baba na Doko kake fadawa matsalarka? Suhaif yaji zancen Baba banbarakwai yana nufin dai ko dan bashi ya haife shi ba. Suhaif da yaji haka sai yaga bari ya fada masa kada ya dauki wani abu daban. Sai ya gyara zama ya bawa Baba labarin Iman tun daga farko har karshe ya kuma shaidawa Baba son Iman ne kadai matsalarsa da damuwarsa. Baba yayi murmushi ya ce "Ai duk wannan ba matsala ba ce zamu je garinsu mu nemo maka auren Iman. Suhaif ya ce "A kwai matsala Baba saboda ban san adireshinta ba Baba. Baba ya gyada kai ya ce "Lallai tunda babu adireshi babu zuwa amma duk wannan ba zai sa ka ci gaba da damun kanka ba ka barwa Allah komai. Ya yiwa Suhaif nasiha kala-kala, ya bashi hakuri. Hakika Suhaif yaji dan sanyi-sanyi a ransa, yayi godiya ya tashi ya nufi dakinsa. Sun bar maganar aikin akan gobe za'a ci gaba da maganar idan Najib yana nan. Washe gari da sassafe Suhaif ya shirya ya fadawa Najib idan *yan gida sun tashi ya ce musu ya tafi Doko dauko su Zubaida. Najib ya tambayeshi "Lafiya? Suhaif ya amsa masa "Lafiya kalau munyi magana da Baba ne ya ce a daukosu sun sami admission a BUK. Najib yayi murna ya ce "Lallai yaran nan sun faso gari. Wai wa yaga idanuwansu a Jami'a? Suka yi sallama Suhaif ya fita, a motarsa ya tafi Doko. Da la'asar likis suka shigo Kano sun kuwa ci sa'a Baba da Najib suna gida, da Mama dukkansu zuna zazzaune a babban falo. Bayan sun gaggaisa suka tambayi lafiyar mutanen Doko. Sannan Baba ya sanarwa da su Zubaida cewar sun sami admission kuma ya aika Gemany a shigo musu da motocinsu, suka yi ta murna suna godiya. Ya juya ya dubi Najib ya ce "Najib kai kuma wata mai zuwa za ka je Jos yin interview, Suhaif kuwa sati mai zuwa zaka je Lagos domin tantanceku. Alhamdulillahi abun alheri ya samu lokaci guda, ina rokon ku dan Allah masu karatu ku rike karatunku ku mayar da hankalinku ku ci jarabawa, ku gama karatunku akan lokaci. San nan ku kuma da Allah Yasa ku ka gama karatun lafiya, Allah yasa ku ka sami aiki kuyi kokari ku rike aikinku, har Allah Yasa kuyi iyali ku rikesu. Mama ma ta ce "Gaskiya ku godewa Allah Ya kara budawa Mahaifinku, ya sassaya muku motoci, ya yi kokari ya samar muku aiki, matan kuma ya taimaka kun sami admission a Jami'a duk lokaci daya. Suhaif ya gyara zama ya ce "Haka ne, mun godewa Allah kuma mun gode muku, ku Iyayenmu da ku ka bamu ilimi. Kuma Insha Allah zamu rike aikinmu, ku kuma *yan makaranta ku san abin da ya kai ku jami'a, karatu ne ya kai ku ba zance da samari ba. Najib ya karba ya ce "Ku sani a jami'a zaku hadu da jama'a kala-kala kowa da dabi'ar gidansu, da al'adar yarensu don haka ku kiyaye ku san irin kawayen da zaku yi, ku guji mayaudaran samari, *yan matan suna amsawa da to. Bayan Suhaif ya koma dakinsa sai ya nemi bacci ya rasa ya shiga tunanin inda zaiga Iman shine matsalarsa, yayi tunani da kwakwalwarsa iya kokarinsa ya tankade ya bakace yaga kawai ba zai iya zuwa wajen aiki ba, domin rayuwarsa gaba daya ta sukurkuce saboda rashin Iman, babu aikin da zai iya a rayuwarsa. To amma ta ina zai kubce, ya ya zaiyi, wacce hujja zai bawa Baba akan ya rabu da shi ba aiki? Ana gobe ranar da za'a tantance su Suhaif a Lagos, tun da daddare Baba ya bawa Suhaif kudin Jirgin da zai tafi Lagos ya ce ya shirya da sassafe a kaishi filin Jirgi ya tafi. Ran Suhaif bai so ba amma ya rasa ta inda zai fara yiwa Baba bayani. Ya kwana yana juyi yana tunani, yaji a ransa ba zai iya lulukawa ya tafi har Lagos ba, ba tare da yaje neman Iman ba don haka ya yanke hukuncin da yaga ya dace da rayuwarsa. Kudin Jirgin da Baba na Kano ya bashi na zuwa Lagos da sauran kudaden ya hada ya daure a cikin jakar kayansa daya shirya tafiya Jalingo neman Iman ba wajen aikin zai jeba. Ya rubuta wasika ya ajewa Najib a kan gadonsa yayin da yake ta shakar bacci da sassafe misalin karfe bakwai. Al'adar gidan ce bayan sallar asuba sai a koma bacci, sai dai idan akwai mai uziri ya tashi ya shirya ya yiwa masu aikin abinci magana suyi masa nasa kalacin ya ci ya tafi, sauran kuwa sai sanda yunwa ta addabesu za kaga suna fitowa daya bayan daya. Daman Suhaif tun asuba yayi wanka ya shirya daya tabbatar kowa ya koma bacci haikan sai ya kinkimo jakar kayansa ya je ya saka a motarsa ya tashi mai gadi a hankali ya bude masa get in zai fita. Ya shiga mota ya na sanda ya kunna, ba tare da ya bata wuta ba, ya sulale ya fita don kar Baba yaji fitarsa. Misalin karfe goma sha daya Baba ya fito yana tambayar mai gadi "Ina Suhaif ya ce zai je ne tun karfe bakwai saura? Ashe ya ga fitarsa ta wundan dakinsa. Mai gadi ya ce "Bai fadamin inda zaije ba amma na ganshi da jakar kaya. "Jakar kaya, ina zaije da jakar kaya ba dai Lagos din zai tafi a mota ba, bayan