Sashe 66
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 9 min read
Cikin harshen fulatanci na cewa Mama Tabita "Annabin farko shine Annabi Adam, bayanshi an yi Annabawa da yawa sannan daga karshe Allah (S.W.A) Ya turo Annabi Muhammad (S.A.W) sai wasu mutane suka ki yarda da shi. Don haka Annabi Muhammad (S.A.W) ne Annabin karshe shine ya zo da addinin karshe wato addinin Musulunci. Mahaifiyata na karatu sai naga ta rufe jaridar, ta cire gilashin dake fuskarta tayi shiru na lokaci mai tsawo sannan ta juyo ta kalleni muka hada ido sai tayi sauri ta juya ta ci gaba da karatunta. Na gyara zama na cewa Mama Tabita "Ki na da labarin wata rana da ake kira ranar lahira ko kuma tashin kiyama? Mama Tabita ta amsa mun a shelake ta ce "Haka naji wai-wai a gari ana fada. Nayi murmushi na ce "Yafi karfin wai-wai a gari gaskiya ne. Rana ce wacce ita ce ranar karshe, ranar da Allah (S.W.A) zai yi hisabi dan wuta ya shiga wuta dan Aljanna ya shiga Aljanna. Rana zata sakko kasa-kasa a lokacin da kwakwalwa zata dinga tafasa. Babu wata inuwa da mutane zasu shiga su fake sai inuwa guda daya itace karkashin Al'arshin Ubangiji. Jama'a zasu kagu ayi musu hisabi susan matsayinsu saboda wahala da azaba tayi yawa. Allah (S.W.A) bai kula kowa ba, sai mutane su dunguma wajen Annabin farko Annabi Adam su ce masa "Ka rokar mana Ubangijinka ya kula mu yayi mana hisabi. Sai Annabi Adam ya ce "Nima bazan iya tunkarar Ubangijina ba domin ina fargabar nayi masa laifi a lokacin daya hanemu cin wata itaciya, shedan ya zuga mu muka ci. Sai mutane su tafi wajen duk sauran Annabawa suma za su ce sun yiwa Allah laifi ba zasu iya zuwa wajen Ubangiji ba a wannan rana. Daga karshe sai mu dunguma wajen Annabin karshe Muhammad (S.A.W) sai ya ce ku zo mu je wajen Ubangiji. Ya roki Allah, Allah Ya amsa masa.
Mahaifiyata ta zuramin ido tana kallona sai tayi murmushi ta kira ni, na je na zauna a gabanta. Nan fa muka hau fafatwa ni da ita, ta ce wannan in ce ba haka bane. Kar kuce tana niyyar yarda da ni, a'a tana nunamin ba gaskiya bane. Akwai tambayoyin da taimin masu tsaurin gaske wanda ilimina bai kai nan ba don haka na kasa amsa mata. Haka muke ni da ita kullum muna muhawara. Sai naga ashe har yanzu da saurana, bani da ilimin tunkararta, ta fini ilimi tasan abubuwa da yawa a cikin littafina kamar yadda tasan littafinta yarda ne kawai baza tayi ba ta Musulunta.
Wata rana kanin Hamma Huzaifa ya zo ya ce in zo in ji Hamma Huzaifa. Naji gabana ya fadi murna ta rufeni na zabura na tambayeshi na ce "Hamma Huzaifa ya dawo ne? Ya ce "A'a waya yayi, kullum yana tambayarki aka ce bakya nan shine yau ya kira aka ce kin dawo shine ya ce in kiraki zai sake kira. Ko sakon daya ban bata ba na zari gyalena sai gidan su Huzaifa. Bayan na gaishe da Mahaifiyarsa ko zama banyi ba, wayarsa ta shigo. Na dauka bayan mun gaisa sai yake min fada danme zan tafi a neme ni a rasa har tsawon shekara biyu, matsayina na mace, karamar yarinya. Ban iya ce masa komai ba har ya gama sannan na bashi hakuri na yarda nayi kuskure, muka yi sallama na tafi gida. Duk ranar da yayi waya sai ya aiko a yi kirana mu gaisa. Har takai ta kawo nima ina kiransa mu gaisa. A cikin hirar da muke yi ne ya lura nasan kur'ani da hadisai har ina jan aya in fassara. Yake tambayata ya akayi na koyi duk wannan. Sai a lokacin na bashi labarin yadda akayi na samu ilimi. Na shaida masa ina da matsala wacce take damuna. Cikin sauri ya tambaye ni "Wacce irin matsala? Na shaida masa har yau bani da ilimi, ilimin da nake dashi bai isa in tunkari Mahaifiyata wacce take da tsananin sani a addininta. In bata hujjojin da zata gamsu dani har ta yarda da addinina. Zan bazama in nemi ilimi cikin duniya daga nan har Birnin Sin. Hankalin Hamma Huzaifa ya tashi da ya ji nace zan sake bazama duniya neman ilimi, sai ya shiga bani shawara yana bani hakuri ya ce in ci gaba da wa'azantar da ita a hankali har Allah Yasa ta yarda watarana. Na girgiza kai na ce Mahaifiyata tana da ilimi sosai, tasan wasu bangarorin na kur'ani, idan ta kawo min wata tambayar bana iya amsawa ita take amsa min. Na fada masa Mahaifiyata ta shaida min cewar duk abunda na sani ta fini sani tuntuni, Musuluncin ne ba zata yi ba. Kamar wani dutse ne ya tokaremun a zuciya, kamar wani gungumemen dutse aka dora mun akai, haka nake jina. Bacci wani sa'in yana gagarata ina tunanin hanyar da zanbi Mahaifiyata ta Musulunta. Nayi masa misali da Mama Tabita da Mumuyawa wadanda ba su san ma wanda ya haliccesu ba ma balle su san Akwai Annabawa, na fara samun galaba akansu sosai na wayar da su sun yadda akwai Allah Shine Ya haliccesu saura kiris su yadda dani su karbi addinina. Amma Mahaifiyata har yau har gobe babu jijyarta guda daya data fara rissinawa balle zuciyarta tayi marmarin shiga Musulunci. Hamma Huzaifa ya ce in kwantar da hankalina tunda na ce ina so in koma in nemo ilimi, zai karbo min form ya aiko ta hannun dan uwansa daya masa hanya tafiya, nima sai inje Jami'ar koyan addinin Musulunci ta Makka ita ce mai mata da maza. Wacce yake ta Madina maza ne kawai. Ya tambaye ni zan iya yin shekara uku ne karatun tunda na iya larabci kuma na iya rubutawa. Wanda bai iya larabci ba ne zai yi shekara hudu, shekara daya cur za'ayi ana koya masa magana da rubutun larabci kafin ya fara karatun. Da gudu nace masa ina so ya aiko min da form din zan je. Ya yi min alkawari zai aiko amma in fara neman shawarar Mahaifina.
Ashe a lokacin Mahaifina yana ta fafutukar nemo min admission in samu in hada digirina. Koda na shaida masa zan je karatu Saudia sai ya shaida min yana nemar min admission, me zai hana in hakura in zauna in yi digirin a nan tunda Allah Ya sa na sami abinda na samu na ilimin addinin? Na shaida masa manufata har yau ilimin da nake da shi bai isa in gamsar da Mahaifiyata ba ta rungumi addininmu. Bai hanani ba, sai ma yayi min addu'a Allah Ya taimaka ya bani sa'a. Sai bayan da Hamma Huzaifa ya kusa kammala min komai na tafiya har ma sun aiko sun dauke ni sannan na shaidawa Mahaifiyata cewar zan je karo ilimin addini a Saudia. Kafin ta ce komai sai da tayi dariya sannna ta ce Allah Ya bani sa'a in je in dawo tana nan tana jirana, amma kafin in tunkareta in tabbatar na san komai a cikin addinina idan ba haka ba zai zamanto ita zata dinga kure ni.
Kamar yadda Huzaifa yayi da zarar Ambasadan kasarku yasa maka hannu shikenan babu abinda zaka biya, kyauta zasu baka visa da tikiti, gidan zama, abincin da zaka ci hatta kudin jrigin da zaka zo ganin gida kyauta ne. Ba tare da bata lokaci ba aka aiko aka ce in taho. Na shirya na yi sallama da kowa da kowa. Alhamdulillahi kafin in tafi na Musuluntar da Mama Tabita da kanwata Hajara har na koya musu karatun salla, na Musuluntar da mutane uku a garin Mumuyawa maza biyu mace daya kawayena, suna Sallah a boye.
Tun sanda na je kasa mai tsarki na dukufa da karatu haka komai ya zo min cikin sauki sai da takai ta kawo na zama a bar kwatance a makarantarmu saboda kokarina. Bamu cika haduwa da Hamma Huzaifa ba sai in ya shigo Makka ko kuma nima idan na je Madina Ziyara kabarin Annabi Muhammad (S.A.W) a lokacin aikin Hajji ko Umara muke haduwa mu gaisa. Kafin in je kasar Hamma Huzaifa yayi aure shi da matar suna Madina. Na je ban dade ba Hamma Huzaifa ya kammala karatunsa a turasu Bahrain a matsayin Teaching Practice, daga nan suka rikeshi suka daukeshi aiki. Shi Bahrain ta zamar masa gida domin matarsa *yar asalin kasar ce. Don haka sai yayi zamansa a kasar Bahrain gaba daya.
Sai bayan dana cika shekaru biyu da fara karatu sannan na dauki izinin zuwa ganin gida gaishe da Iyayena, aka barni na zo. A lokacin ina jin kaina kusan babu tambayar da za'ayi min a cikin addinina ta gagareni amsawa ko kuma babu fejin da za'a bude a cikin littafi mai tsarki a ce in karanta ban karanto ba, har in fassara kuma in yi karin bayani, in tafi lokacin da aka saukar da ayar da kuma dalilin da yasa aka saukar da ayar. Don haka bani da fargabar tunkarar Mahaifiyata kai tsaye.
Bayan zuwana da sati guda muka fara gwagwarmaya da Mahaifiyata ta ce wanan ince ba haka ba wancan ne. Tayi-tayi ta kureni ta kasa na mata tambayoyi da dama ta kasa amsawa, haka na zaiyano mata hujjoji babu adadi, na mata wa'azi mai ratsa jiki har jikinta sai da yayi sanyi da alama ta fara tantance gaskiya da karya.
Na kutsa kauyen Mumuyawa da karfina ina ta wa'azantarwa duk da ban tunkari shi ainihin shugaban nasu ba, kuma bai san abunda nake aiwatar masa a gari ba. Ya dauka har yanzu wasa nake zuwa wajen kawayena su Maho. Cikin ikon Allah suna ta yarda dani suna karbaar Musulunci da yake duhun kan nasu ya ragu naga yanzu suna saka sutura ba fata ba, sannan sun fara shigowa gari suna gina gida su zauna masu halinsu. Harma suna shiga wasu Addinai ba nasu na gadon-gado ba.
Mama Tabita da kanwata kuwa Musulunci ya ratsa su, suna sallah da Azumi. A lokacin kanina Abubakar ya tafi Jami'ar Jos shine yake koya musu karatun Al-Kur'ani kuma daman Mahaifina ya sa shi a makarantar Islamiyya har ya sauke. Abu duk ya cushewa Mahaifiyata duk jikinta yayi sanyi da alama ta gane gaskiya nauyi da kunyar *yan wajen bautarta ne yake damun ta yadda zata kallesu ta ce musu ta Musulunta bayan girma da mukaman da suka bata take rike da shi, watanni uku nayi a kasar nan kafin in koma, Ana sauran sati guda in tafi Allah Ya taimakeni. Mahaifiyata ta karbi shahada, dadin da naji bazai misaltu ba.
Sai su Goggo suka yi kabbara. Muslim ya gyara zama yana sauraran Iman cike da mamaki.
Iman taci gaba da cewa "Mahaifina yafi kowa mamaki ko a mafarki bai zata akwai wa'azin da zai ratsa Patrica ta karbi Musulunci ba, domin yayi iya kokarinsa da ilimin da Allah Ya bashi tun ba yau ba ya musuluntar da ita taki yadda fur. Yayi murna tamkar ya goya ni, yayi min addu'ar alhairi wacce bai taba yi min irin ta ba tunda aka haifeni. Na tafi na barshi da ita yana koya mata addini. Bayan sun tambayi Malamai yaya matsayin aurensu yake a yanzu? Malaman sun yi musu bayanai da gyara akan aurensu.