← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 80

Sashe 16

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Duk wannan shirye-shirye tsakanin Lamin da Patrica da iyayenta ne kawai ake yi, Iyayen Lamin basu taba sanin akwai wata halitta a duniya ba wai ita Patrica balle zancen aure a tsakaninsu. Don su a bangarensu har sun tanadar masa wacce zai aura a dangi. Yarinya mai kyau *yar Fulani Hauwa'u sunanta ta gama Sakandirenta a F.G.C Azare tana kiransa. Sai hanya-hanya yake yi musu har ta kai ta kawo ya fara dauke kafarsa daga garinsu don ana damunsa da maganar auransa da Hauwa'u. Idan mahaifiyarsa ta tuntubeshi game da zancen aurensa sai yayi ta hanya-hanya yana cewa a jinkirta akwai wasu shirye-shirye a gabansa yana so ya kamala. Haka mahaifina yayi ta shammatarsu har lokacin aurensa da Patrica, suka yi bikinsu ba tare da danginsa sun sani ba. A nan garin Jalingo ya samo wasu tsofaffi suka shige masa gaba aka yi aka gama. Amarya ta tare a gidan angonta a cikin Jalingo wata unguwa da gidajen ma'aikata suke wato G.R.A.
Mahaifina yayi ta nuku-nuku ya kasa shaidawa mahaifiyarsa da danginta cewar ya auri wacce ba musulma ba amma duk daren dadewa abun boye zai fito fili haka duk nisan dare gari zai waye. Wani dan uwansa ne yazo Jalingo kuma aka fesa mata labari cewar Lamin fa ya yi aure tuntuni wacce ya aura kuma ba Musulma bace kuma taki Muslunta. Bai yi wata-wata ba ya garzaya garin Gombe ya shaidawa Kakata da danginta halin da dansu Lamin yake ciki. Aka ce Mahaifiyarsa faduwa tayi fuk ta suma. Dangi gaba daya kuka suke yi tamkar gidan mutuwa. Ko da labari yakai kunnan Lamin cewar yazo maza-maza a gida ana nemansa sunji labarin auren da yayi sai yaki zuwa garinsu kwata-kwata. *yan uwansa da yawa sun zo sun iske shi har Jalingo suyi fadansu su tafi babu abunda ya ragu a jikinshi don shi yanzu ya fara zama da matarsa babu mai rabasu.
Allah Ya albarkacesu da samun haihuwa suka haifeni ko ban fada ba kunsan nayi kama da Mahaifiyata ne tunda jama'a da yawa suna mun kallon farar fata ce *yar kasar jajaye. Duk da idan ka karemun kallo zaka iya ganin ina kama da Babana amma nafi kama da Mahaifiyata. Ta radamun suna RUFKATU. Mahaifina kuma ya tara Musulmai ya yanka rago ya radamun sunan Mahaifiyarsa Fatima. Nan aka sha rigima da mahaifiyata wai ita babu mai kiran *yarta da sunan Musulmai Fatima. Shi kuma ya ce ba zai kira *yarsa da suna Rufkatu ba. Mahaifina yana kirana da Fatima. Mutanen gari suna kirana da Prety ma'ana mai kyau. Kowanne suna ina amsawa, amma da aka sakani a makaranta Rufkatu Lamin Mahaifiyata tasa ake rubutawa.

Ina da shekaru hudu aka haifi kanina kamarmu daya aka saka masa suna Bobby, mahaifina ya rada masa suna Abubakar. Bayan ya shekara biyu aka haifi *yar autarmu, mahaifiyata na kiranta da Rebecce Mahaifina yasa mata sunan kanwarsa mai binsa Hajara. Bacin rai sosai ya dasu a zuciyar mahaifiyata danme mahaifina yake yanka mana rago yake rada mana sunayen Musulmai baya kiranmu da sunayen data radamana. Bayan dashi aka yi yarjajjeniya *ya*yansu zasu bi addininta, ya ce ya yarda. Me yake nufi kuma yanzu? Fadan safe daban na rana daban. Ya shaida mata shi ba wai yana nufin *ya*yansa dole sai sunyi sallah ba, amma shi abun kunya ne wataran su shiga danginsa aji sunayensu bana Musulmai ba. Mahaifina yana ta aike a nemar masa gafara wajen Mahaifiyarsa, ace ta yafe masa yasan yayi mata laifi. Dakyar ya samu ta aiko masa da magana mai dadi ta ce ta yafe masa kuma tana masa fatan Allah Ya shirye shi ya kare shi daga barin addininsa kamar yadda ya yarda ya haifi arna a cikinsa. Da ya dauki hutu a wajen aiki, Mahaifiyata ma tana aiki a banki itama ta dauki hutu mu ma aka yi mana hutu a makaranta saiya cika mu a mota muka nufi Gombe muje muga danginsa, dangi kuma su ganmu.

Munsha wulakanci, munga takaici iri-iri domin baro-baro ake nuna mana tsana da zafuta da hantara. Ko randar Kakarmu muka je muka bude muka sha ruwa sai an fasa randar an sayo wata wai marasa tsarki sun saka mata najasa. Bamu isa mu zauna akan tabarmarsu ba balle abun sallarsu sai ayi ta yayyafa ruwa koma a wanke gaba daya. Mahaifiyata taji haushin wannan wulakanci da ake yi mata da *ya*yanta sosai, tasha alwashin har abada ba zata sake zuwa Gombe ba. Mahaifina ma baiji dadin yadda aka yi mana ba, amma ya kasa tarar danginsa balle yajawa kansa. Muka har-hado muka dawo gidanmu Jalingo.
Yaren Fulatanci shine yaren da yawancin *yan garin suke yi don haka fulatanci Mahaifina yake yi mana. Mahaifiyarmu ma haka amma tafi yi mana magana da turanci wasu lokutan da yarenta Igbo. Me rainonmu da mijinta maigadinmu suna zaune a boy's qoutern gidanmu su kuma yarensu Tangala ne mutanen Billiri karamar hukumar Gombe. Tun muna yara suke yi mana yarensu na tashi ina jin tangalanci. Rayuwata tana cike da rudani nakan kasa tantance wazan bi uwata ko ubana. Na tashi naga Mahaifina na yin sallah sau biyar a rana. Haka kuma na tashi naga Mahaifiyata tana zuwa wani waje suna bauta kullum. Gata ma'aikaciyar Banki ce tana fita aiki da sassafe sai da yamma likis take dawowa gida amma da zarar ta dawo ko hutawa bata yi saita shirya ta nufi wajen bauta har dare suna addu'a. Ranar Asabar da Lahadi kuma saita shiryamu ayi mana ado ni da kannene mu tafi wajen bautarsu. Mu bar Mahaifinmu a gida yana karatun Jarida wani lokaci yana karatun kur'ani mai tsarki.

Nafi son Mahaifina fiye da Mahaifiyata saboda nafi zama dashi don haka munfi sabawa. Idan ya fita wajen aiki karfe tara na safe shima baya dawowa sai da yamma likis. Yafi Mahaifiyata sakin fuska da wasa da janmu a jiki musamman ni yafi jana a jiki fiye da kannena, su kuma sunfi son Mamarmu. Ina wasa da Mahaifina kamar wani abokina, ya goyani, muyi wasan *yar tsanata dashi, yasa mana kida da waka ya tashi ni dashi muyi ta rawa. Amma baya garajen ya koya mun karatun kur'ani saboda gudun bacin ran Mahaifiyata.
Watarana ne Mahaifina yana sallar la'asar baisan ina bayansa ina binsa sallah ba. Mu dai munji muryar Mahaifiyata kamar zata tsaga gidan don kara muka juyo a firgice mu dukkanmu ni da shi. Sai ta ci gaba da fadace-fadacenta da zage-zage wai ashe daman idan bata nan sallah yake koyamin? Yayi mata rantsuwa da Allah shi bai san ina bayansa ba ina binsa Sallah. Ranar naga tashin hankali a wajen Mahaifiyata tayi min dukan da tunda nake babu wanda ya tabamun irinsa har jikina ya fashe, masu aikin gidanmu da mahaifina suka dinga riketa suna rokarta tayi hakuri tace sai tabar gidan ita da *ya*yanta baza suyi addinin Musulunci ba kuma zamanta da musulmi ya kare. Dakyar ta hakura, bayan Mahaifina yayi mata alkawarin irin haka ba zata sake faruwa ba.
Shekaruna basu wuce tara ba a lokacin amma kwakwalwata tana da kaifin hankali da tunani. A kullum kuma a koda yaushe bani da abun yi sai tunani ina so in tantance me yasa kowa da abunda yake bautawa? Haka kuma nake bi ina tambayar manyan da shekarunsu sukafi nawa wai shin su me suke bautawa, bayan sun fadamun musulmai ne ko ba Muslmai ba ne. Sai ince me yasa suka zabi wannan addinin basa yin dayan? Sukan rasa amsar da zasu bani sai suyi dariya kawai. Huzaifa wani saurayine makwabcinmu shine baya taba gajiya da bani cikakkiyar amsar duk tambayar da nayi masa akan addininsa da ma wanda ba nasa ba.
Idan na tashi da safe, Tabita me aikinmu sai ta shiryamu mu tafi makaranta. Mahaifiyarmu na da mota ita zata sauke mu a makaranta sannan ta wuce wajan aikinta. Mahaifinmu kuma sai ya dauko mu daga Makaranta shima dai-dai lokacin yake dawowa daga aiki sai mu dawo gida tare. Tabita ta bamu abinci muci, sau da yawa bayan Mahaifinmu ya ci abinci saiya fita wajen abokansa can wata unguwa mai nisa. Kannena kuma sai su kwanta suyi ta barci ko su fita kofar gida wajen abokansu. Da Tabita nake zama muyi ta hira a hankali sai take nuna mun abunda take bautawa. Abunda take bautawa kuma yasha bambam da abunda Mahaifiyata da Mahaifina suke bautawa. Wani sassakekken itace ne anyi mutum-mutumi da shi an rataya masa kahunhunan rago da wasu gashi-gashi. Sai suzo ita da mijinta su durkusa a gabansa suna rokarsa duk abunda suke so wani lokaci har suce nima in zo in durkusa in rokeshi zai ba ni. Wa'iyazubillah. Haka kullum muke yi da su. Idan kuma na gaji da zaman gida sai in sa takalmina in fito in tafi wajen kawayena da muke yin wasa tare, wadanan kawaye nawa ba wasu bane illa arnan daji. Zaka iya hango bukkokinsu daga can nesa da gidajenmu, sunan yaren mumuye.

Ehem,, gaskiya na gaji da zama, za kuji komai daga bakin IMAN..RUFKATU..PRETTY..FATIMA zuwa gobe da yardar Allah.

Reedwan Suraj Isma'il

>>>>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN
Chapter 16 · 0% Book details