← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 80

Sashe 41

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

Mummy Naila tana dan jin Turanci amma mijinta yana magana da turanci sosai ta haka muke magana. Amma na dage saina koyi Larabci dan haka nake kin yin magana da turanci, nake kwaba larabci. Ita kuma tana rokona in dinga yiwa danta turanci tana so ya koya kafin ya shiga makarantar boko. Na samu shekara guda a gidan larabawan nan cikin ikon Allah larabci ya zauna a bakina saboda a gida larabci, makaranta daman kakaf larabawa ne komai da larabci ake yi don haka siffata, shigata da maganata duk ta larabawa ce. Haka a shekarar na sauke Alkur'ani mai girma, na haddace Hadisai masu yawa, nasan Tauhid da Fikihu. To kunji inda naji yaren Larabci na kuma iya karatun Alkur'ani.

Iman tayi hawaye tasa gefen hijabinta ta goge. Su Suhaif sun zuba mata ido suna jin wannan labari mai dinbin al'ajabi kamar almara. Iman taci gaba da cewa "Sai kuma yanzu za kuji dalilin barina gidan. Gidan da ake min gata, ake kaunata tamkar jinin jikinsu.

Ta ce "Babu wani mugun hali da suka yimin har nabar gidan, haka nima har muka rabu babu ha'inci ko zamba ko cin amana dana yi musu, illa mugayen matsafan da suke jikina suka rabamu. Tun sanda na kama addinina haikan ba dare ba rana bautar Allah karatun Alkur'ani ya shiga bakina sai kuma na shiga tashin hankali, rayuwata ta shiga barazana. Kullum na kwanta barci sai in ga wadancan matsafan a mafarki kuma kamar ido biyu. Suna kirana kuma suna lallabata, suna bani shawara in fita daga addinnin da nake. Sabida addinin akwai addu'a mai zafi da nake damunsu da ita suna nisanta daga gareni, su kuwa a kullum suna tare dani dan suna sona, zasu bani arzikin da zanfi kowa. Inyi farat in tashi a firgice amma da addu'ata fal baki. Da naga haka sai na shiga bin Malaman makarantarmu daban-daban suna bani addu'o'in tsari daga sharrin mugaye. Na kuma bazama neman litattafan addu'oi iri-iri sune abokan hirata.
Haka kuma nake ganina a mafarki inata kona su da Ayar Allah, don haka na fara fin karfinsu. Matsafan ma suka bazama neman abun tsafin da zasu tsafeni suci galaba a kaina, suna kai kukansu kasa-kasa, gari-gari wajen manyansu suce wai yarinya karama ta gagaresu shakara da shekaru.
Da Allah Ya kaddara za suci galaba a kaina daga baya sai na zama yin addu'ar yana min wuya. Musamman da daddare sai in kasa addu'a in zan kwanta bacci. Wata rana cikin mafarki sai naga matsafan sun daukoni suna murna, suna tsalle suna waka. Suna magana da duk yaren da nake ji, suka daure ni a jikin wata bishiya, suna waka suna zagayeni. Ina ta zullo ina so in kwace daurin da suka yimin na kasa kwacewa, sun kuma dauremin bakina na kasa ihu balle addu'a. Babu abin da zan iya hanga a wajen sai dokar daji da *yan bukkoki, sai itatuwa waje-waje an kunna wuta, suna rike da wasu itatuwan a hannayensu suma a kunne da wuta. Matansu da Mazansu, yara kanana da manyan dukkansu babu sutura ajikinsu. Gajerun wanduna mazan suka saka sai jajayen kyallaye a daure a kansu da dukkannin gabobin hannayensu da kafafuwansu. Haka suma matan banbancinsu da mazan karamin siket ne maimakon gajeran wando sai dan siririn jan kyalle da suka daura suka rufe kirjinsu. Sunyi zane-zane da farin fanti a goshinsu da cikinsu, kayan tsafi kuwa gasu nan birjik ko ina jifgi guda a gabansu, kamar su kan dabbobin gida daban-daban da na daji, kan kunkuru, kan macizai da kokon kan mutane. Abun mamaki naga wasu mutanen da na sani a cikinsu, naga wannan senior data fara sakani cikin ukuba naga da yawa daga cikin *yan makarantarmu na sakandire harda wani babban mutum makocinmu ne mai suna Mr Izera.. Babban abin tausayi harda yara *yan furamari.
Babbansu ya fito suka matsa masa suka bashi hanya yazo gabana, da sauri suka dauko masa abun zaman ya zauna, ya dube ni ya tuntsire da dariya mai karfi da firgitarwa ya ce "Rufkatu! Rufkatu!! Rufkatu!!! Yau gaki a hannunmu amma duk da haka kinfi karfinmu ko yanzu muka bude miki baki zaki karanto addu'ar da zata kona mu. Kinyi nisa mun kasa rinjayarki cikinmu, kuma mun so mu halakar da ke mun kasa saboda karfin addu'arki, da wacce dan Makwabtanku yake yi miki da Mahaifinki. Amma yanzu ladan wahalar da kika bamu zamu zamar dake abar tsana, abar gudu, abar cutarwa a cikin *yan uwanki Musulmai. Yanzu ma zamu gwada miki abunda muke nufi. Sai naga sun dauko wani yaro. Ina duban fuskar yaron sai naga Abdul-Malik dan rainona. Hankalina ya tashi ina ta fisge-fisge ina so na balle na kasa. Suna dariya irin ta mugunta suka bankare yaron sun shake shi zasu kashe shi yana ta tsala kuka. Cikin ikon Allah na daka tsalle da karfi sai na kwance daurin da suka yi min na fusge kyallan da suka rufe min bakina, na dinga karanto addu'o'i, suka fara ja da baya naje da gudu na dauke Abdul-Malik na zura da gudu cikin daji. Sai suka biyoni da gudu. Muna ta gudu ba tsagaitawa, dai-dai nan nayi firgigit na farka daga barci ina ta shesheka kamar da gaske nayi gudun. Jikina gaba daya ya min nauyi yana ciwo zuciyata tana ta bugun uku-uku. Hankalina a tashe, na firgita kwarai da gaske, don ban taba mafarki irin wannan ba. Na gyara fulo na jingina ina mai matukar damuwa da tashin hankali, na fara hawaye ina tunanin yadda rayuwata zata kasance nan gaba. Gashi yadda nake jin yanayin jikina duk sanda zanyi addu'a sai na kasa, nasan dole sun fara samun galaba a kaina. Na tuna irin wahalar da nasha a lokacin da nake Bauchi duk da dai wadanda na farfasawa kai *yan iskane masu san aikata masha'a dani. Nayi sauri na jawo Abdul-Malik da yake kwance a gefena na dube shi, na firgita na mike da gudu yayin dana ga numfashinsa na harbawa sama-sama, jini yana zuba ta hancin sa. "Ina zaki je ne? Kije ki dauke shi a kai shi asibiti, waye yasan abunda kika gani a mafarki? Zuciyata ta fadamin haka.

ALLAH YA KAREMU DAGA SHARRIN MAKIYANMU AMEEN

INA MUKU FATAN ALKHAIRI

Reedwan Suraj Isma'il

*************** YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Chapter 41 · 0% Book details