← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 80

Sashe 30

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 9 min read

Fadila tayi nadama ta gamsu da shawarwarina ta shaidamin in Allah Yaso ko kwana uku bazata
karayiba agarin nan zata kwashe kayanta ta
gudu ta koma garinsu tanemi gafarar iyayenta
tarike addininta. Nima na shaida mata da zarar
anyiwa yan jami'a hutu zan lallabasu janet su bani
kudin mota in koma gida duk da bansan mezan fadawa iyayena ba dakuma yadda zamu karke da
mahaifiya akan sabon addinina.
Fadila ta zage tadaura zanina tazo ta tayani girki.
Ita tayi miyar taushenan tas. Harriet ce ta shigo
tana tafe tana layi idonta sharkab da hawaye.
Muka tashi muka tareta muka rirriketa mun dauka ma ko nakuda takeyi domin watanni
cikinta tara cifcif. Muka zaunar da ita akan
tabarma muna tambayarta meke damunta,
dakyar ta iya bamu amsa tace na tsani
rayuwata,rayuwata ta dagule, nafi sha'awar
mutuwa da inci gaba da rayuwa. Karuwanci ba rayuwar alkhair bace. Ina labe tundaxu abayan
wundo inajin hirarku, pretty kin fimu hankali kin
fimu sani ciwon kanki, kinfimu jin tsoron Allah.
Naji natsani kaina. Ni jahilace wace basan addinin
da nake cikiba saboda wurin bautar iyayen
nawama bana zuwa. Nagamsu da addininku addinine me tsafta addinin gaskiya. Zan karbi
musulunci in mutu a ciki musulunc." gaba su
suhaif suka dau kabbara. Iman ta fashe da kuka
taci gabada cewa "nida fadila da harriet muka
rungume juna muna ta kuka. Aranar na
musuluntar da harriet ta zabi suna khadija. Na sata tayi wanka kamar dai yadda hamma huzaifa
ya koyamin. Nafara koya mata karatun salla da
yadda ake yinta. Abincin da bamu iya ciba mu
dukka hankalinmu a tashe muna nadama. Bayan
munyi sallar isha'i. Fadila tace zata tafi gidan gibrel
ta hado kayanta washe gari zataje banki ta kwashe kudinta ta gudu garin su amma kafin ta
tafi zata zo tabamu kudin mota muma mukoma
gida. Sai dai fatan Allah yasadamu da alhairinsa.
Ta tafi ta barni da harriet abu kamar a mafarki
harriet ta musulunta. Ta zauna zaman dirshen wai
ita adole yau saita koyi karatun sallah. Har sha biyun dare ina koya mata karatun dana iya, ta
tashi tayi alwalla ta sake yin magariba da isha'i
sannan muka kwanta.
Nafara bacci kenan harriet ta daka min duka na
tashi figigit saina ganta a durkushe tana
murkususun zafi. Na kunna fitilar lantarkin dakin sai naganta afujajan sai zufa take tana cije baki
wai cikinta ciwo. Nace ko nakuda ce? Tace eh.'
gabana yafadi nahau salati na rirriketa nida ita
dukka yarane bansan yaya zanyi mata ba. Nafita
da gudu na kwankwasawa mr.segun daki naga
kwado a datse abakin kofar shima yau bazai kwana a gida ba. Ga janet ma bata dawo ba, na
dawo wajen harriet sainaga wani ruwa yana
fitowa daga jikinta ciwan kuma kara karuwa
yake sai ihu take tana kuka. Nima na fashe da
kuka jikina yadau karkarwa. Nace "yaya zamuyi
yau? Na tambayeta akwai kudi ajakarta ne inje insamo mota? Tace naira ashirin ce kawai a
jakarta, fitar da take aiba namijin dayake
daukarta da wannan tsohon cikin. Wani waje
take samu tazauna tayini cur sannan ta dawo
gida bakin cikin rayuwane kawai ya isheta. Nace
to bari in dauki naira ashirin in nemi achaba inje in kirawo micheal yazo yakaita asibiti ko yaki ko
yaso shiyayi mata cikin ai. Harriet fadi take
inyisauri in kirawo shi yazo yakaita asibiti kafinta
mutu. Nadauki naira ashirin na fita da gudu. Dare
yayi sosai bbu yan achaba, na tuna akwai wani
dan achaba. dakinsa awata boy's qauter dake kusa datamu. Naje da gudu na kwankwasa masa
kofa nace yataimaka yazo yakaini wani wajen
nan cikin G.R.A. ne zanbiyashi, yafito da babur
dinsa nahau ahanya yake tambayata "lafiya? Na
shaida masa "harriet ce zata haihu zan kira
wanda yayi mata ciki. Yace aida asibiti nafara kaita kafin akirashi. Nace bazata iya hawa babur ba
dan a durkushe take kuma bamuda kudin zuwa
asibiti saiyazo. Ya figa ya kaini kofar katafare
guest house din micheal inda ina kyautata zaton
anan zan sameshi don fadila ta shaidamun yanzu
anan yafi zama. Nace hadi dan achaba yajirani in shiga inji yadda zata kaya. Nakwankwasa, mai
gadi yaki bude mun yace in tafi inbashi waje bazai
iya kirawo mai min micheal ba. Narokeshi nace
yace pretty ce. Ya tafi dakyar yafadawa
ubangidansa. Koda yaji sunana nanda nan
micheal yace yaje yashigo dani. Afalo na iskeshi 'yan mata biyu karuwai a zagaye dashi. Yana
ganina ya kuramin ido yana kallona, kallo irin na
'yan iska. Sai a lokacin ma na kula da cewar rigata
yar yaloluwace shara-shara 'yar karama iya
gwaiwa, ta barci, kaina ba dankwali. Takalmin
kafata wari da wari don gigicewa. Nasa hannayena nadinga kare jikina don kunya. Yayi
murmushi cikin harshen turanci yace "you are
well come pretty. I'm glad to see u my baby come
and hug me". Ya yiwa yan matan nan biyu nuni
da hannunsa alamar su matsa daga kusa dashi,
suka koma gefe. Na matso kusa dashi a tunaninsa zanzo in rungumeshi sai yaga na
durkusa a gabansa. Yayi murmushi yace
'common stand-up baby feel free, relax don't shy
i am your lover, i love you my baby yasa hannu
zai jawoni jikinsa na goce gefe muryata na
karkarwa nace "zance harriet ne ya kawoni." ya bata rai yaji an ambaci harriet yace fadi meye inji"
nace ka taimakemu kazo ka kaita asibiti zata
haihu..dan bazaka jeba kabamu kudi da direba. Bamuda
kowa agarinnan saikai kuma danka ne za'a
haifa." uwar tsawar daya daka mun bani ba 'yan
matansa ma sun razana sunja da baya. Na mike
da gudu nayi bakin kofa yace "fita daga gidan
nan kar in kara ganinki indai zancen harriet zaki dinga yimin. Ina ruwana da haihuwarta ta mutu
mana." ya kira 'yan matan sa ya rungumesu a
gabana suka dinga aikata masha'a. Ban daddara
ba na rushe da kuka naci gaba da rokarsa
yataimaka ko cikin banasa bane yataimaka ya
kaita asibiti. Yace ya tuna alkawarin daya yimana yace shi kadai muka sani agarin nan duk abunda
muke so zai taimaka mana. Maganar daya sake
yicewa yayi idan zan yarda in shiga dakinsa
inbashi minti uku mu kebe zai yarda yakai harriet
asibiti, idan kuwa bazan yarda ba na fice nabashi
waje. Na ishe shi da magiya akan basai nashiga dakiba yadaure yakaita asibiti tunda shi yayi mata
ciki. Yazaro belt ya biyoni aguje. Gudun da ban
tabayin irinsa ba, na bude get nayi waje ba shiri.
Na cewa hadi maza ya kunna babur mubar kofar
gidan nan. Tambayoyin da hadi yakemun "ku
arna inda ake kwararku kenan ba kamar mu musulmai ba kuje kuyi ta iskanci da mazan banza
suna muku ciki wai dan dakan kuka a haihu ba
aure. Ku acikin arnan ma karuwai ne ai munada
labarinku, makaranta iyayenku suka turoku
kuka falle kuka kiyin karatun. Kebakiyi kama
dasu ba kamar bafillatana kike ko balarabiya ko shuwa. Bai kamata ki shiga cikin arna ba kina
tacewa. "nasake rusa kuka naji na tsani kaina na
tsani rayuwata. Abakin dakin mu ya saukeni nace
ya tsaya in shiga in rikota ko zata iya hawa
achaba mu kaita asibiti. Nashiga natarar da harriet
wanwar a tsakar daki cikin jini kaca-kaca kan da yafara lekowa ta galabaita ko maganarta bata fita
sosai. Na kwalla kara na fito da gudu a gigice
nace da hadi dan achaba "taimaka min kazo mu
daukota jini ne yake zuba daga jikinta." ya
yatsuna fuska yace "to da jini zan dauketa, yaya
ma zatayi ta iya zama akan babur? Gaskiya mota yakamata ku samo, kuma da ace matar aure ce
zata haifi dan sunna da saimu bugawa wani kofa
yafito da mota yakaiku asibiti ace ya taimaka
amma duk an sanku a unguwar nan karuwai ne
babu me sauraronku. Yanzu ki biyani kudina
saiki bani wasu kudin inje intaso abokina me taxi yazo ya kaiku asibiti idan yaga an biyashi zaije."
namika masa naira ashirin din nan nace "ita
kenan garemu kataimaka." ya galla mun uwar
harara. Yace "akan naira ashirin kika katsemun
barcina dan ubanki? Ya kawo mun mari na kauce,
yayi wurgi da naira ashirin din ya buga babur dinsa ya tafi yana zagina. Na koma cikin daki da
gudu na tarar da kan da yana sake fitowa waje.
Ina kuka narike hannun harriet, tarikeni tace
pretty mutuwa zanyi idan na haihu dan yayi rai
kidauka kirike minshi amana nima yar uwarki ce
musulma ki taimaka ki rikemin dana ko 'yata. Kicewa iyayena su yafe mun. Pretty kici gaba da
kyamar zina, ki gujeta kikoma gida kiyi aure, irin
wannan rayuwar da muka jefa kanmu ba alkhairi
bace." harshenta yafarara hardewa sai gumi take
kamar ruwa sai wani nishi take da karfi kamar
akuya. Nahau salati da karfi itama saita kamayi sai tayi nishi mai karfi guda daya sai da ya sunbulo
ya fado ya cara kuka, yayin da ita kuma nishinta
na karshe a duniya ta cika.
Abun yafi karfin kuka saina koma na zauna ina
kallon bakin dan kankanin jariri yana tsala kuka
sai in juya in kalli uwarsa a kwance ta mutu. Jini face-face ajikin su bansan yadda zanyi ba, banida
sauran tunani. Harreit data zama gawa ta fini jin
dadin yadda nakejina a ranar. "dama nima
akamani a harbeni ace nina kasheta. Haka nake
addu'a. fakam naji an daga labule an shigo. Fadila
na gani sanye da rigar bacci irin tawa harma tafi tawa kankanta iya cinyarta. Ta dora hannu aka ta
kwalla ihu ganin harriet da dan ta face-face a
kwance a cikin jini. Tambaya take 'harriet ta
mutune?" na gyada kai don bana iya magana
alamar "eh ta mutu.
Saita jawo hannuna tace pretty tashi mubar dakin nan, taso mu tafi tun daga unguwarmu da kafa
na taho inzo in shaida miki abunda yake faruwa.
" na kalleta cike da fargaba nace "meke faruwa?
Jikita yanata karkarwa sosai a tsorace take. Tace
"janet ma ankasheta solomon saurayin janet an
kashe shi, ngozi da easter kawayena an kashesu. Ta rushe da kuka tace Gibrel saurayina shima
yana cikinsu ankashe shi. Yanzu motar yan sanda
ta zagaye gidan micheal za'a kamashi shima a
kashe shi? "Na zabura na mike tsaye na dafe
kirjina nace "me sukayi? Ta rushe da kuka tace
ashe duk kudin nan dasu micheal suke kashewa bana iyayen su bane, ba sana'a sukeyiba fashi
sukeyi. Micheal ne babbansu shi yake turasu suyo
fashi idan sukaje lagos ma fashi sukeyi. Dazu
suka tafi jos wai harda su janet suka rakasu
sukayo fashi yan sanda suka biyosu suna harbin
yan sanda 'yan sanda na harbinsu. 'yan sanda suka harbi tayoyin motarsu suka gangara motar
ta kife duk suka mutu. Wani abokinsu ne guda
daya emeka bai mutu ba amma ya jijji ciwo, ya fita
daga motar kafin yan sanda sukaraso yabi duhu,
ya tsere bakin titi ya dane motar daukar kaya. masu motar basu sani ba ya shigo Bauchi duk a cikin
daren nan. Ya dibi kudin Gibreal ya ce yanzu zai gudu
garinsu Lagos, nima na debo mana kudin mota, taho
mu gudu.
Chapter 30 · 0% Book details