← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 80

Sashe 56

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Suhaif yana ta magana shi kadai ya ce "Naja'at ce? Ta amsa da cewa "Eh" ya ce "Wai bakya magana ne? Ko baki iya gaisuwa ba ne? Ba'a ce miki Suhaif ba ne? Muryarta na karkarwa ta gaishe shi, sai ya gane muryar Zubaida ce. Yayi ajiyar zuciya ya ce "Naja'at ce ko Zubaida? Ta ce "Zubaida ce, Naja'at bata nan. Suhaif yayi shiru kamar ruwa ya cinye shi, ya rasa mai zai ce mata, kawai sai ya ajiye kan wayar. Bai so Zubaida tasan ya kira Naja'at ba, cikin sirri yake so ya tambayeta halin da ake ciki game da maganar auransa da Zubaida. Suhaif yayi dogon tunani yaga mafita ita ce ya kira Baba na Kano suyi maganar, hakika kamar yadda Mahaifansa suka fada gaskiya ne bai dace ya dubi idon Baba na Kano ba ya yi kirmisisi ya ki aurar *yarsa. Bayan ta fada shi take so. Ya ci sa'a kuwa ya sami Baba na Kano a layin wayarsa na office. Bayan sun gaisa sun taba *yar hira akan harkokin kwangila da kasuwanci, sai Suhaif yayi gyaran murya ya ce "Baba ina tunanin zan zo Kano karshen watan nan akan maganar da muka yi da kai. Baba ya tambayi Suhaif ya ce "Wacce maganar fa? Suhaif ya hau kame-kame can ya ce "Zancena da Zubaida. Baba yayi murmushi ya ce "Ai wannan zancan ya wuce tuntuni. Ba su fada maka bane? Karka damu kanka ka ci gaba da harkokinka, Zubaida ta yarda zata auri Muslim. Daman munyi maganar aurensa tuntuni da Babansa. Suhaif ya ce "Amma Baba ai.... Baba ya katseshi ya ce "Na ce ka kwantar da hankalinka, ka manta zancen ya wuce. Baba na Doko ma ya gamsu da hujjojin da na bashi. Ba komai Suhaif karka damu. Su kayi sallama suka ajiye kan waya. Suhaif ya shiga halin damuwa mai tsanani yana ganin anya Baba na Kano ko dai ya dauka baya son *yarsa ne? Sai Suhaif ya kira Najib ya tuntube shi da zancen aurensa da Zubaida. Irin kalaman da Baba ya fada masa haka Najib ya fada masa. Hankalin Suhaif a tashe ya hayo jirgi ya zo Kano babu shiri. Ya iske Mama ita kadai a gida, tayi matukar mammakin ganin Suhaif. Bayan sun gaisa sai ta ce "Amma baka ce min ba zaka zo kwanan nan ba. Suhaif ya ce "Wallahi nima ba shiri na taho. Bayan ya zauna tasa masu aiki suka kawo masa ruwa da abinci, ya tambayeta ina *yan gidan? Ta ce "Duk sun tafi harkokinsu sai ita kadai. Suhaif ya gyara zama ya zaiyana mata abunda ke tafe da shi, ya zo akan maganar aurensa da Zubaida. Ya fada mata yadda suka yi da Baba da Najib, sun ce ya kwantar da hankalinsa kar ya damu Zubaida zata auri Muslim. Sai yake ganin kamar fushi suka yi ko suna ganin shi ya ki aurenta. Shi kuma ba haka bane tabbas Iman yake so. Amma ina Iman din take yanzu? Kuma ko tana nan ai wata kusan tafi wata, gara ya auri kanwarsa Zubaida. Haka Suhaif ya karka ce yana yiwa Uwar *ya dadin baki, alhali har ga Allah Iman ya fi so ya aura.
Mama taji dadi sosai da kalaman Suhaif dan sauran kullatar da ta yi masa ta goge. Ta yi dariya ta ce "Haba haba Suhaif karma ka kawo wannan a ranka. Mun san ba zaka ki aurar kanwar ka ba, kai da idan ba ranmu kai zaka zabar mata miji na gari wanda zai rike ta amana. Ta zayyanowa Suhaif dalilan da suka sa Mahaifinta ya ce ta auri Muslim tunda har anyi magana da Mahaifinsa. Shima yaro ne mai hankali, mai sonta. Suhaif ya ji dadi tamkar an sauke masa wani kaya dingimeme mai nauyi a kansa. Yayi ta addu'a akan Allah Yasa haka shi yafi alheri kuma Allah Ya basu zaman lafiya. Mama tana amsawa da amin. Ya ce ta bashi mukullin motarta zai je Doko gobe zai dawo, jibi kuma zai koma Lagos.
Suhaif ya isa Doko ya ci sa'a ya iske Mahaifinsa da Mahaifiyarsa a gida. Ya zauna ya tambayesu dalilin da yasa aka fasa aurensa, shi dai ga yadda suka fada masa a Kano, ya Zaiyyana musu yadda suka yi da Iyayen Zubaida. Har ya nuna baiji dadi ba da aka ce an yiwa Zubaida miji don shi yanzu ya zo da shirin aurenta. Mahaifinsa ya ce "Ai daman Zubaida ta wuce ka, bayan har an kawo min kudin aurenta na karba sai dai ka nemi wata. In kuma har yanzu Iman kake jira sai ka yi ta jiran yarinyar da baka tabbatar bama ko tana raye ko ta mutu. Yanzu nan da watanni uku za'ayi auren Zubaida, Naja'at da Najib. Shima ya ce min ya sami mata zaiyi mana magana lokacin da zamu kai kudin auren. Ka zauna kana turo hula gaban goshi za ka tsufa baka yi aure ba kannanka zasu yi aure su haihu. Suhaif yayi dariya ya ce "Lokaci dai Baba. Goggo ta hau lallashin Suhaif akan yayi hakuri ya nemi wata ya hakura da jiran Iman shima nan da wata ukun a hada da na *yan uwansa.
Bayan komawar Suhaif Lagos da wata biyu Najib ya kira Suhaif a waya. A lokacin Suhaif ya tare a dankareran gidansa na Abuja. Yana zaune a bakin swimming pool din gidan a kishingide kan kujerar hutawa yana sanye da dan dajeren wando da yamma. Masu yi masa hidima duk maza ne suna ta kai kawo suna ta jera masa kayan makulashe akan teburin dake kusa dashi. Yana shafa gashin burgujejen Karen daya suyo daga England. Suhaif ya amsa wayar Najib cikin fara'a ya ce "Najib ka ki zuwa sabon gidana ko, balle ka kawo su Mama da Baba da Goggo, Hajja, *yar Hajja, Zubaida da Naja'at da sauran dangi suzo su sa albarka ko? Najib yayi dariya ya ce "Ai ni zuwa Abuja zai yi min wuya, kasan yanayin aikina. Amma nan da wata guda zan dauki hutun bankina, a gidan zamu zo muyi honey moon ni da amaryata.
Suhaif ya tuntsire da dariya ya ce "Kaji Sarkin makaryata, karya kake yi kana cewa ka samu mata har yau babu wanda ka taba nunawa ita. Najib ya ce "Wallahi da gaske nake, yau kuwa zaku gaisa da ita da bakinta zata fada maka sunanta. Suhaif yaji muryar mace ta karbi waya a hannun Najib ta gaishe da Suhaif, suhaif ya amsa cike da tunanin kamar ya san mai muryar. Sai ya ce "Amarya yaya sunanki? Ta ce "Sunana Naja'at, Suhaif ya zabura ya tashi tsaye ya ce "Wacce Naja'at? Babu tantama har muryar Naja'at kanwarsa ce. Ta bawa Najib wayar, ta zura daki da gudu itama sai yanzu ta gane Suhaif ne, dan Najib bai fada mata ko waye ba. Najib ya karba yana dariya ya ce "Ita ce matata, wallahi ita zan aura insha Allah. Mamaki ya rufe Suhaif ko kadan babu wanda yasan Najib da Naja'at suna soyayya. Bayan wata guda Suhaif ya zo Kano aka sha bikin Zubaida da Muslim, Najib da Naja'at. Suhaif yayi musu hidima da dukiyarsa abunsa, mutane suka yi ta mamaki duk wanda ya zo bikin ya kunshi goma ta arziki.

Gidan Amare ya kawata da gadaje da kujeru, show glass da kayan kicin duk na Italy ne Dubai da London. Baba na Kano ya sayi wasu, Suhaif kuma ya sayi sauran. Bayan ansha shagalin biki Suhaif ya koma Abuja, cike da damuwa kan damuwa. Yasan yanzu idon kowa ya dawo kansa dole za'a dame shi da zancen aure a dangi. Hankalinsa a tashe duk ya bi ya sukurkuce yana cikin tashin hahkali. Tunda ya kasa zabar wata ya aura wacce yake so, yake jira kuma shiru ba ita babu labarinta. Suhaif ya dubi sama da kasa a gidansa babu abinda ya nema ya rasa na rayuwar jin dadin duniya. Ya jawo wata brief case ya bude babu abinda ke cikin ta sai Dallers, ya wurgar da akwatin, kudin da ke ciki ya watse a tsakiyar dakin, ya buga kai a jikin gadon da yake zaune. Ya ce "Babu abinda na nema na rasa a duniyar nan amma bana jin dadin rayuwata saboda na rasa Iman, na rasa farin cikina.
Chapter 56 · 0% Book details