Sashe 28
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read
Iman ta girgiza kai ta ci gaba da cewa "Sai ajiyar zuciya nake na kasa yiwa Maman Huzaifa bayani. Nayi shiru na kasa magana. Sai ni sai zuciyata da Ubangijina muka san gaskiya, babu abin da zan fada su yarda dani, tashin hankalin da nake ciki ba zai barni in iya bayani ba. Ni da Maman Huzaifa muka yi shiru muna tunani can na daure na bude baki nayi magana na ce "Mama nazo wajen Hamma Huzaifa ya aka yi ya bari haka ta faru da Mahaifina? Maman Huzaifa ta kalleni ta ce "Meya faru da Mahaifinki Fatima? Sai na rushe da kuka na ce "Mahaifina na gani sanye da kayan bauta irin na Mahaifiyata, da alama ma wani babban mukami suka bashi a wajan bautarsu. Mahaifiyata ta ja Mahaifina ya bar addinin Musulunci ya bi nata. Cikin shesshekar kuka na ci gaba da cewa "Har yanzu ni Musulma ce ban bar addinin Musulunci ba, yanzu ma nake kara zurfafa a cikinsa, nazo da niyyar in tunkari Mahaifina in shaida masa na karbi addininsa, na Musulunta kuma zan bishi koda kuwa Mahaifiyata zata yankani. A yanzu nake son tsananin taimako da shawarwari daga Hamma Huzaifa sai gashi Allah mai yadda Yaso ya dauke min Huzaifa lokacin da nake tsananin bukatar taimakonsa, wanda bana fargaba bana kokonto, da jikinsa da dukiyarsa zai taimake ni in rike addinina. Bugun kirjin da nake ina tinkaho Mahaifina Musulmi ne zan iya binsa in Musulunta, sai gashi komai ya canja min. Bani da sauran mai karfafa min gwiwa inci gaba da bin addini Musulunci sai Allah. Meya sa Babana yayi min haka? Danme ya bari suka rinjaye shi ya bar addininsa, addinin gaskiya, addini mafi tsafta mafi can-canta a bishi? Bayan tsawan shekarun da aka dauka yana rike da addininsa, yaki shiga nata yanzu kuma kwatsam ya bari ta rinjayeshi. A tunanina shine namiji ni kuma babbar *yar mu zamu hadu mu hada kai mu rinjayeta ta shigo Musulunci sai gashi shi ta rinjaye shi. Allah ne kadai gatana, shine jagorana, Shi zai tsareni Ya kareni, don bazan iya canja addinina ba saboda Mahaifina ya bar addinin, ko don Huzaifa ya bar kasar. Na sake kifa kai akan gwiwata kuka mai radadi ya ketomin.
Maman Huzaifa ta matse hawayen daya cika mata ido ta dafa kaina ta ce "Fatima kinyi gaskiya kada kibar addininki komai ukuba. Dare da rana, safe da yamma Huzaifa yana tunani, gashi zai tafi wazai ci gaba da taimakonki akan addininki, yana ta sake-sake yana neman shawarata. Sai muka yanke hukunci kafin ya tafi yaje ya sami Mahaifinki a boye ya sanar da shi cewar kin Musulunta ya ci gaba da baki goyon baya ki rike addininki. Kafin Huzaifa yaje ya fada masa sai rashin lafiyar ciwan kafa ya dami Mahaifinki bayan tafiyarki makaranta. Kafar ta rure, ta kumbura ko fita baya iya yi, ganin halin da yake ciki shi ya hana Huzaifa ya je ya sanar masa na ce ya bari ya samu sauki tukunna don ya dade yana jinya. Anyi maganin asibitin, anyi na gargajiya abu ya faskara kullum kafar sake suntumewa take. Aka rasa kan ciwon musamman idan dare yayi ciwon yafi damunsa ihunsa har gidan nan. Baban Huzaifa ma yayi masa kokari, duk inda ya samu labarin mai magani zai je ya dauko shi ya kawo shima yayi bajintarsa ya tafi, ciwo dai yana nan danye sharaf. Ciwo daga Allah babu wanda yasan sanadiyyar ciwon, haka kuma babu wanda yasan maganin ciwon.
Iman ta sharbe hawaye, suhaif ya sake sa hannu a aljihunsa ya dauko mata wani hankici ya mika mata, ta karba ta goge hawaye. Jama'a sai sake gyara zama suke suna jin wannan abun al'ajabi. Taci gaba da cewa
"Na dakata da kukan da nake na tattara hankalina gaba daya ina sauraran Maman Huzaifa, zuciyata cike da fargaba da tsananin tausayin Mahaifina da kuma kaguwa inji karshen labarin. Me ya hada ciwon kafa da canja addini? Maman Huzaifa ta ci gaba da cewa "Kinsan tsakanin mata da miji sai Allah, ashe Mahaifiyarki koda yaushe tana lallashin Mahaifinki ya yarda ta kaishi wajen bautarta, a kwai wasu turawa da suka shigo garin nan suna yada addininsu. Allah Yana basu iko su warkar da mutum duk tsananin ciwo, amma fa da sharadi kafin su warkar da mutum. Zasu saka masa doka idan ya warke dole ya koma addininsu. Wanda bashi da rabo, hankalinsa ya gushe, ciwo ya tsananta so yake ya rabu da ciwon ya huta, sai idonsa ya rufe ya manta magani da ciwo duk yana hannun Allah, sai kaga mutum ya amsa musu da "Eh na yarda idan na warke zan koma addininku. Kuma babu mahalukin daya isa su warkar da shi ya tsere yaki shiga addininsu, kana warkewa abu na farko da za su yi maka shine su baka babban mukami a wajan bautarsu, su baka kudi masu yawa idan kana dashi ma sai su kara maka lunkin naka, su zamana koda yaushe suna tare dakai suna koya naka addininsu har sai sun tabbata addinin ya ratsaka ka manta da naka na da, kafin su daga maka kafa. To irin haka ne ya faru da Mahaifinki. Da tsananin ciwo ya dame shi ya amincewa Mahaifiyarki, wacce take member ce a cikin kungiyar, ta dauko wadannan turawa suka zo suka dinga zano masa sharuddan gaba daya ya amince. Allah Ya basu iko suka warkar da shi a cikin sati biyu kacal yayi garau, duk da ransa bai so ba dole ya dulmiya ya bar addininsa. Wato ranar da muka ji labarin haka ta faru da Mahaifinki hankalinmu ya tashi musamman Huzaifa ke yafi tausayawa, babu yadda zamu yi dukkanmu. Huzaifa ya so ya fasa tafiya Madina ya zauna saboda ya taimaka miki ki rike addininki amma babu yadda za'ayi ayi haka, tunda ya gama komai na tafiya har sun turo masa da takardar an dauke shi, suna nemansa a wannan lokacin za'a fara karatu. Mahaifinsa ya ce lallai ya zo ya tafi.