Sashe 73
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Huzaifa ya dubi matarsa Zainab cikin harshen Larabci ya ce mata "Zainab kinga rayuwa ko? Kinga muhimmancin hakuri ko? Kawayenki a can suna zuga ki wai danme zaki yarda ayi miki kishiya bayan ku a kasarku ba'a cika yin haka ba. Kika dauki zuga kina cewa saidai in sake ki, dakyar na shawo kanki to kin gani komai sai Allah Yayi. Idan ba wata kaddara ba mai tsanani bani ba kara aure har abada, daman ita ce kadai wacce nake tunanin zan aura. Zainab tayi murmushi ta gyada kai ta ce "Hakika na ga muhimmancin hakuri, kuma na sake gane zaman duniya. Na yi nadama ku yafe min. Ta dubi Iman ta ce "Ki yafe min. Iman na kuka suka rungume juna Iman ma ta cewa Zainab ta yafe mata. Mahaifin Suhaif yayi ajiyar zuciya ya ce "To mun godewa Allah, Huzaifa! Suhaif ya taho muku da gudunmawarsa zai bawa ango da amarya. Motoci ne guda biyu yake da niyyar idan zamu tafi ya baku, daya ta amarya daya ta ango. Huzaifa da Mahaifansa suka yi godiya, Iman da Iyayenta ma suka yi ta godewa Suhaif. Nan dai suka zauna suka yi ta magana ta farin ciki da godewa juna har zuwa lokaci mai tsawo, sannan suka fito dan za'aje aci gaba da gudanar da shagalin biki. Huzaifa ya shiga gidansu kannensa su Bilkisu sun yi tatul sun cika da bakin ciki. Suna ganinsa suka hau yi masa korafi don me yasa zaiyi musu haka bayan sun shirya sun zo tun daga Abuja zai ce ya fasa ya barwa wani, ga anko har Lagos taje ta kai dinki, ga robobi da memo da kalandu duk sun bugo yanzu sun yi asara kenan. Suka bashi labari har Aljanu Amina ta tayar dan bakin ciki, dakyar ta sauka. Huzaifa yayi ta dariya yana tsokanar Amina yana cewa "Wato suma Aljanun sun yo sabon dinkuna zasu sha biki suka ji an fasa shine suka ji haushi kenan? Sai a lokacin suka bashi labarin tataburza da suka sha yi da matarsa Zainab tana kuka ta hada kayanta da *ya*yanta zata tafi suna riketa. Shi dai dariya yake tayi. Ya zauna ya wayar musu da kai ya fada musu dalilai masu karfi har saida suka gamsu suka saki ransu. Ya rokesu karsu fasa yin hidimar bikin da suka yi niyya, duk abunda suka yi niyya suyi, Fatima dama ai kawarsu ce. Kalandu ne kawai da memo mai hotonsu za'a kona robobi da kufuna kuwa sitika kawai za'a ciccire aje a sake bugo wata da sunan Fatima da Suhaif, zan baku kudin sitikar a lillika a raba. Suka amsa cikin fara'a suka ce babu damuwa sun huce. Sai yanzu farin ciki ya cika zuciyar Iman, hankalinta ya kwanta saboda sanda taji da Suhaif aka daura bata yi bakin ciki ba amma abun ya daure mata kai ta rasa dalilin wannan sauyi, amma yanzu da taji haka daga bakin Huzaifa sai taji hankalinta ya kwanta farin ciki ya lullubeta. Bata da zargin kowa a kanta, don da tana damuwa saboda Suhaif yana ganin bata sonsa dama shine yake sonta. Ga matar Huzaifa ta damu tana kuka dan zata aure mata miji duk ta tsangwami kanta, tasan kuwa har abada damuwar tana ranta. Yanzu Huzaifa ya wanketa bata bata da kowa ba. Zumunci tsakaninsu yanzu ya kullu, haka tsakanin Iyayenta da nasa da Iyayen mijinta Suhaif Alhamdulillahi! Aka sha biki! Budiri!! Birede!!! Babu kwabon Suhaif balle na Iyayensa duk Huzaifa ne yayi komai. Babu abinda Huzaifa bai tanada ba kuma bai fasa duk abunda yayi niyyar yi a bikinsa ba. Anyi liyafu kala-kala, haka duk abunda ake kaiwa gidan Iyayen Amarya na al'ada Huzaifa yasa an kai gidan su Iman a matsayin Suhaif ne ya bayar. Da aka kammala biki sai Suhaif da Iyayensa suka fara shirin komawa gida wato Kano. Yadda suka tsara tafiyar za'a kai su Baba, Goggo, Mama, Zubaida, *ya*yanta, mai aikinta da Naja'at Yola su hau jirgi su tafi. Sai Suhaif, amaryarsa Iman, Najib da Muslim su tafi a motar Suhaif. Huzaifa ya ce karsu damu su Suhaif su hau motarsu su tafi shi zai kai Iyayen nasu Yola su hau jirgi. Huzaifa da Iyayensa, kannansa, matarsa, Mamar Iman, Babanta, kannanta, Mama Tabita da kawayenta Mumuyawa duk sun rako ta bakin mota ana ta koke-koken rabuwa. Huzaifa da Suhaif suka yi musabaha suka gaisa Suhaif ya na masa godiya ba adadi. Huzaifa ya girgiza kai ya ce "Nasan dadin da kaji dan haka karka damu. Saboda Allah nayi, shi zai saka mun da alhairinsa. Huzaifa ya zaga wajen Iman yana mata nasiha ta bi mijinta sau da kafa suk da yasan ita me biyayya ce kuma ta sani amma tuni yake mata, cikin kuka take amsa masa yayin da kwalla ta cika masa ido shima. Iman ta rungume *ya*yansa Fatima da Huzaifa tana yi musu sallama tana kuka. Dakyar Iman ta shiga mota kannenta Abubakar da Hajara sai kuka suke suna rike mata hannu. Haka Mahaifiyar Iman ta damu dan rabuwa da *yarta, ba kamar Mama Tabita tayi kuka har idonta ya kunbura. Akwatinan lefenta guda takwas kadai aka saka mata a but. Suhaif da Iman a bayan mota, Najib ne yake tukawa, Muslim a gaba suka ja suka tafi, suna daga musu hannu suma suna daga musu hannu. A sababbin dalla-dallan motocin da Suhaif ya bawa Huzaifa da Iman wacce ana bata ita kuma ta bawa Mahaifinta kyauta, a ciki za'a kai Iyayen Suhaif Yola inda za su hau jirgi, *yan rakiya suka dunguma wajen motocin. Matan ne kawai suka cika motar Huzaifa, su kuma su Baba suka shiga ta Mahaifin Iman. Mahaifin Iman ke tukawa suka dinguma filin jirgin Yola. Suna da kudin yankar tikiti amma Huzaifa ya hanasu su biya, ya biya musu gaba daya. Su Huzaifa ba su baro filin jirgin ba har saida suka tsaya suka ga tashinsu. Suhaif da amaryarsa Iman suna zaune kawai suna kallon-kallo, farin ciki da kauna fal a zuciyarsu, sun bar Najib da Muslim a gaba suna ta zuba. Najib magana yake ba kakkautawa har saida Suhaif yasa baki ana hirar da shi daga nan Najib ya gangaro tsokanar Suhaif ya ce "Oh! Suhaif da tuni ka mutu, har ranka ya zo makogaro, ya aka yi ya koma? Dariya suke tayi har sai da cikinsu yayi ciwo ballema Iman. Muslim ya ce "Aini ban san farin ciki yana sawa a fasa mutuwa ba sai akan Suhaif. Suhaif dai dariya yake yana cewa "Kwaji da shi, ku ce duk abunda zaku ce ni dai na warke babu ciwo har abada. Su Baba sun rigasu isowa Kano, kafin su Suhaif su karaso har an gyara musu wani bangare in da amarya zata sauka. Kwanan su uku a Kano amma Suhaif baya iya ko leka bangaran Iman saboda kunyar Iyaye sai dai su hadu a falo da safe su gaisa. Daga Kano ya dauketa suka tafi Doko nan ma a bangaren Suhaif aka sauketa. A bangaren akwai falo, daki, bandaki a ciki. Suhaif kacokan shi da kayansa ya kaura gidan Kakarsa Hajja acan yake kwana saboda kunyar Iyaye. *Yan garin Doko sun sha mamaki lokacin da aka fesa musu labarin Suhaif ya auri Iman gashi ya zo da ita. Suka dinga tururuwar bin layi waccan na fita waccan na shiga suna zuwa suna gaishe da Iman. Kawayenta na da duk sunyi aure da *ya*yansu suke zuwa su sha hira da Iman. Daman *yan garin Doko suna son Iman tana birgesu, abunda ya faru yasa suka kita da suka ji labarinta tun asali sai suka daina ganin laifinta. Suhaif da Iman satinsu guda a Doko, dangi sunga Iman, itama ya kaita taga dangi na cikin Doko da kauyuka. Da suke je Garki wajen Iya Furera sai Suhaif ya ce da Iman "Ko in kaiki Gumel ki shiga garin Gumel yadda kika ci burin zuwa Gumel Allah bai yi ba. Iman ta ce "Kaini in ga Gumel tunda gani a motata ma bata haya ba. Suhaif ya kai Iman Gumel daman su Suhaif suna da *yan Uwa dankam a Gumel, yini guda cur suna zagaya Gumel. Iman ta ce "Gaskiya naji dadin yadda Gumulawa suke karbar baki, sun karbeni hannu bibbiyu. Bayan sun yiwa kowa da kowa sallama sai suka fito suka kama hanyan garin Abuja kai tsaye, suna tafe suna hira amma idan Suhaif ya dauko mata hirar soyayya sai ta rufe ido ta kasa bashi amsa, har yanzu kunyar nan tasa da take ji tana nan. Sun isa Abuja lafiya, kai tsaye suka kutsa cikin katafaren gidansa. Masu gadi da ma'aikatansa sun fito taron Suhaif. Amma sai suyi turus su tsaya a lokacin da suka ganshi rike da hannun Iman. Kamar yadda Suhaif ya saba hira da su yana yi musu wasa sosai. Sai suke tambayarsa "Oga yaushe ka samu matar da zaka aura bamu sani ba? Suhaif yayi dariya ya ce "Ku biyoni falo zan baku labari. Gaba daya ma'aikatan gidan ya ce a kira su zo ya na da magana dasu. Suka hadu reras sunyi su ashirin, gaba daya maza ne. Ya sanar musu da cewa Iman matarsa ce yanzu haka daga Jalingo yake can aka yi bikin. Ya musu gargadi, ya ja kunne ya fada da kakkausar murya cewar su kiyayi bata mata rai, idan ta ce a yi to ayin, in ta ce a'a to a bari, saboda zai iya yanke kowanne irin hukunci akan wanda ya bata mata rai. Ya sanar musu da cewar zasu iya yi masa laifi sai dubu ya hakura amma idan suka yiwa Iman sau daya ba zai yi hakuri ba. Ko shakka babu sun ji ajikinsu da gaske yake yana son matar nan ko ba'a fada musu ba. Akwatinan Iman direba daya kwaso daga but ya shigo da su falo sannan Suhaif ya sallamesu, kowa ya koma wajen aikinsa. Iman ta dubi Suhaif tayi murmushi ta ce "Yaya irin wannan fada da kake yi musu a kaina kamar ka auro *yar gwal? Suhaif ya ce "Ai kinfi *yar diamond ma Habitti (masoyiya). Tayi murmushi ta ce "Yanzu duk wadannan ma'aikatan gidan nan ne? Suhaif ya ce "Idan bakya sonsu sai in koresu a dauki wasu. Iman ta ce "A'a duk zamu zauna dasu ba kora, sai dai ina son a karo mata kamar guda biyar naga gaba