← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 80

Sashe 45

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

A gigice Suhai yake janta yana so ya kwace ta daga hannun matsafan duk da baya ganinsu yasan janta suke yi. Nan da nan manyan Malamai suka bude Alkur'ani suka fara karatu. Ba su kadai ba jama'a da yawa suka ruga gida suka dauko Alkur'ani cikinsu harda Najib ya kwaso Kur'anan gidab gaba daya. Suhaif ma ya karba aka zagaye Iman ana tayi mata karatu. Ta dora hannu akai, ta nutsa kanta cikin gwiwowinta kamar zata nitse cikin kasa, saboda tsabar tsananin zafin addu'ar da take kona matsafan da suke jikinta. Ta mika hannu da kyar ta kamo bishiyar dake kusa da ita ta kankame bishiyar da karfi tana yare wanda babu wanda yake jin yaren. Haka kuma bai hanasu daina ragargazarsu da ayar Allah ba. "Mu muna sonta tun kafin ta rungumi addininku. Ta fada cikin wata kakkausar murya wacce ko kusa bata yi kama da muryar mace ba, cikin harshen Hausa take magana yanzu. Wani Malami ya ce "Karya kuke makiya Allah yau sai munga bayanku azzalumai. Kamar yadda kuka kashe sai an kasheku. Ana ta karatu an zagaye bishiyar da ta rike ta rasa inda zata sa kanta, idonta yayi jajawur sai zufa take keto mata tamkar ana ruwan sama ta jike hagaf. Ta sake cewa "Kuna kona mu kuna kashe mana *ya*yanmu da jama'armu fa. Sai su kuwa masu karatun suka sake daga murya suna karatun da karfi. Ukuba tayi ukuba, zafin kuna yayi zafi, sai Iman ta fadi kasa numfashi sama-sama. Baisa sun daina karatu ba, ana ta jan ayoyi masu karfi. Matsafan ji suke kamar ana musu ruwan wuta. Yau sunga ta kansu sun gamu da gamunsu, a yau suka yi nadamar haduwa da Iman, sun yi dana sanin nacin da suka yi shekara dashekaru. Tuba suke, hakuri suke bayarwa daga yau zasu rabu da ita. Ko hanyar da tabi ma sun daina bi, amma tuba da nadamarsu yau baza tayi amfani ba. Babu mai sauraronsu, babu mai tausayinsu, babu mai shirin sassauta musu. Tun ana jin abinda Iman take fada har ta fara magana a hankali yadda ba'a fahimtar ta har tayi shiru bata ce wa komai ta rufe ido kamar mai bacci. Ba'a tsagaita da karatun ba yi ake tayi. Can Iman tayi magana wannan karon muryarta ce. Ta ce "Gaba dayansu gasu nan sun mutu, sun kone kurmus da wuta. Suhaif yayi ajiyar zuciya ya fada a baiyane "Alhamdulillahi. Ana ta karatun ba a daina ba har saida Iman ta tashi zaune daram tana kallon kowannensu daya bayan daya cike da mamaki. Sai ta tambayesu "Me yake faruwa? Suka tsaya da karatun itama suka tambayeta meya faru tsakaninta da matsafan? Ta yi shiru tana tunowa can ta ce "Na gansu suna ihu suna kamawa da wuta daga karshe suka fadi suka mutu, sun kone kurmus gaba daya garinsu ya kone kayan tsafinsu ma ya kone. Sai gaba daya *yan wajen suka yi kabbara. Malami daya daga cikin Malaman ya ce "Muna miki albishir kuma muna taya ki murna daga yau kin sami lafiya, kin rabu dasu har abada da izinin Ubangiji. Wannan wutar da kika gani tana konasu karatun da muka taru muka yi miki ne don haka mun konesu kurmus da ayar Allah.
Iman taji dadin da tunda uwarta ta haifeta bata taba ji ba. Sai ta rushe da kuka tana godiya ga Allah. Wani Malami ya ce "To ai shikenan sai ta dauki kayanta ta koma gidan su Suhaif ta ci gaba da rayuwarta, ku kuma jama'ar gari kunji da kunnuwanku ba laifinta bane don haka banda tsangwama da kananan maganganu. Samun mutum irin Iman sai an tona a wannan zamanin. Ta sadaukar da rayuwarta, ta sallama rayuwar jin dadin duniya saboda ta shiga Musulunci. Sai kowa yayi kabbara.
*Yan garin Doko gaba daya suka ji suna son Iman, saboda karfin Imaninta. Da gaske Iman take tana son Musulunci da *yan uwanta Musulmai. Yarinya mai kunya da ladabi, ko a hanya taga mutane zata yi musu sallama ta duka har kasa ta gaishesu. Haka jama'a suka gauraye wajen da yabonta. Suhaif yaji dadi sosai har kamar zaiyi tsalle don murna. Ya dauko jakar kayanta ya dauko mata takalmanta ya ce "Iman saka takalmanki ki zo mu tafi gida kiyi wanka, kici abinci ki huta kinji. Ta sharbe hawaye ta yi murmushin karfin hali ta ce "Na gode Suhaif Allah Ya saka muku da alheri kai da Iyayenka, *yan uwanka da mutanen Doko gaba daya. Ba zan kara ko kwana daya a garin nan ba, yanzu lokaci ne da zan koma gida wajen Iyayena in ga halin da suke ciki. Alhamdulillah abunda na zo nema na samu, na samu ilimin addinina. Zan iya kare addinina in kuma bada hujjoji masu karfi da za'a yarda abunda nake bautawa shine gaskiya. Hakika zan sami Iyayena in musu wa'azin da zai ratsa su, su karkato zuwa ga addinina musamman Mahaifiyata nafi ji, ta Mahaifina mai sauki ne domin yasan gaskiya karfinsa aka fi kawai. Ga Mama Tabita mai kaunata zan so ta kasance Musulma ba mushirika ba. Zuwana Kano da Doko na karu sosai, kuma a sanadiyyar haka na samu lafiyar ciwon da ya dade yana addabata.
Malamai su ka ce "Ai haka ya yi gara ki koma garinku ko hankalin Iyayenki zai kwanta, kin bar gida shekaru biyu kenan. Wannan hukuncin bai yiwa Suhaif dadi ba ransa ya baci, jikinsa yayi sanyi, ya shiga damuwa. Baya son Iman ta tafi ta barshi. *Yan sanda suka ce to ta shiga motarsu, su kaita Kano sai su sakata a motar garinsu. Suhaif ya yi caraf ya ce "A'a ku barta gobe zan kaita Kano in sakata a motar garinsu. Babansa yayi wuf ya katse shi ya ce "A'a ka bari tunda ga masu tafiya ka bari a kaita yau mana. Kafin Suhaif ya sake magana Iman har ta shiga mota, dan sanda daya ya karbi kayan Iman a hannun Suhaif ya saka a mota. Malamai suka shiga motocinsu, *yan sanda ma suka shiga, kafin aja motar *yan garin suka baibaye jikin wundon da Iman take zaune suna tayi mata sallama da fatan alheri. Iman tana hawaye tana mika musu hannu suna musabaha da bankwana ko rai kanga rai. Zubaida da Naja'atu suka zo wajen Iman, sai kuka ya kece musu su duka ukun. Zubaida tayi karfin hali ta ce "Iman ki yafe mana abubuwan da muka yi miki, baki taba yin fushi ba, baki taba kai kararmu wajen wani ba, bakya gaba damu. Cikin kuka Iman ta ce "Na yafe muku tuntuni Zubaida ku yafe mun nima.
Suhaif da Najib suka karaso jikin wundon Iman, sai kuka ya sake barkewa Iman ganin hawaye daga idanuwan Suhaif. Suhaif yayi karfin hali ya ce "Iman tafiyarki zata iya haddasamun abubuwa guda biyu, na daya zan iya rasa jin dadi a rayuwata har abada, na biyu zan iya kamuwa da ciwon rashinki har ya ja in iya rasa raina saboda damuwa. Iman karki tafi ki barni. Ta ce "Suhaif karka damu, kada rashina ya haddasa maka ciwo, Allah ne ya hada mu, kuma shine zai raba mu a yau. Shine kuma idan Ya so da izinin Sa zamu sake haduwa. Zai yi wuya in manta da kauna da halaccin da kayi mun a rayuwata, babu wani mahalukin daya taba sadaukar da rayuwarsa a kaina irinka. Ka soni a lokacin dana zama abar tsana, abar tsoro, abar gudu. Ina sonka nima bazan daina ba ko zai zamanto bazan sake ganinka ba har karshen rayuwata...... Ba ta karasa maganarta ba aka ja motar suka tafi. Tana hangen Suhaif yana ta bin motar da gudu yana ce wa "A tsaya! A tsaya!! Kuka mai zafi ya rufto musu ita dashi. *Yan gari suna ta dagawa Iman hannu har saida suka daina hango motar. Gwaggo da *yan matanta kuka suke tukuru na rabuwa da Iman. Haka jama'a da yawa basu shirya yin kuka ba, amma sai suka ji hawaye ya kece musu saboda bakin cikin tafiyar Iman. Sabo turken wawa, Iman ta shiga ransu sun saba da ita, ta saba dasu.
Zaku tausayawa Suhaif idan ku kaga halin da yake ciki, a cikin kasa ya zauna turmus yana damkar sawun tayar motar da Iman take ciki. Najib ya dade yana bashi baki amma kamar zugashi yake. Kowa ya watse ya barsu shi da Najib a wajen. Suhaif yaki tashi su tafi shi kuma ya kasa tafiya ya barshi, Suhaif sai rokon Najib yake Allah Annabi yake, ya tafi ya kyale shi anan shi ba zai koma gida ba, Najib yaki tafiya. Baba ya fito sallah Masallaci ya hangosu a zaune sunyi jugum-jugum ya zo ya same su, ya tambayesu me suke yi. Najib ya fada masa abunda yake faruwa. Ya shiga bawa Suhaif baki akan yayi hakuri ya manta da Iman Allah zai iya bashi wacce tafi ta. Suhaif yana dagewa shi fa Iman yake so gashi bai karbi adireshinta na garinsu ba, babu inda zai ganta. Haka Baba da Najib su kayi ta lallashin Suhaif da kyar Suhaif ya tashi suka nufi gida.
Chapter 45 · 0% Book details