Sashe 60
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sun isa falon da yake dauke da tafkeken dining area me kunshe da zungureren table da kujerunsa. Huzaifa kawai suka iske ya iso, Suhaif cikin fara'a ya mika masa hannu suka gaisa. Suhaif ya ce "Jiya ina jinku a jirgi kuna ta hira ciwon kai ya hanani magana. Huzaifa ya girgiza kai ya ce "Ayya! Allah Ya sawake, wallahi ban sani ba, kuma Najib bai fadamin ba da nayi maka sannu. Yaya ciwon kan yanzu? Suhaif ya ce "A'a yanzu na warke da nayi bacci. Huzaifa ya ce "Alhamdulillahi Allah Ya sawake. Shigowar su Iman ce ta katsesu sai dukkansu hankalinsu ya koma ga duban bakin kofa suga masu shigowa. Iman da matar Huzaifa dukkansu suna sunke a cikin burgujejiyar bakar riga daga sama har kasa amma yau basu saka nikaf ba fuskokinsu a bude. Fatima da Huzaifa suma fes dasu Iman tayi musu wanka ta caba musu ado da wandon jeans da riga shirt iri daya banbancin kawai ta Fatima anyi adon irin na mata a jiki na Huzaifa kuwa anyi ado irin na maza. Yaran kyawawan larabawa ne babu abu daya da zaka gani a halittarsu kace sun hada jini da bakar fata, duk da dai namijin kamarsu daya da Mahaifinsa amma gashinsa da fatar duk na larabawa ne. Suhaif ya fara dimaucewa yana kokarin rikicewa irin wacce ya saba yi idan suka hadu da Iman. Yayi yaki da zuciyarsa ya daure ya saki ransa kamar baya jin komai. Iman ta dubi angonta Huzaifa wanda tun shigowarsu ya zuba mata ido, ta gaishe shi da larabci, matarsa taje ta rungumeshi sannan ta sumbaci kumatunsa yaransa ba irin gaisuwar da suka yi masa kenan. Ya yiwa yaran magana da fulatanci ya ce su je su gaishe da su Suhaif. Fatima da Huzaifa suka je suka yi musu sallama suka mika musu hannu suka gaisa. Matar Huzaifa ma ta dubi su Suhaif tayi murmushi tayi musu sallama, suka amsa cikin fara'a. Iman ta karasa kusa da Najib ta gaishe shi tana mai fargabar gaishe da Suhaif tana gudun kada yaki amsawa. Suhaif ya katse kokonta ya ce mata "Amarya Iman ina kwana. Sai abun ya basu mamaki da dariya ita da Najib. Ta ce "Amarya Iman ka saka min? Huzaifa ya ce "Ai kuwa sunan yayi dadi daga yanzu ma Amarya Iman zan dinga kiranki. Wai shin ina kika samo suna Iman ne? Sunan yayi min dadi tun ran nan nake tambayarki baki fada min ba. Iman ta dubi Najib ta juya ta dubi Suhaif, yayin da su duka suka zuba mata ido tayi murmushi ta ce da Huzaifa "Tambayi Yaya Suhaif ko Yaya Najib. Sai su duka suka kyalkyale da dariya suka dunguma kan teburin cin abinci. Irin kayan alatun da aka jera yafi karfin cikin mutane shida, mutane ashirin zasu iya ci su koshi su rage, babu abin da babu kai har da dumamen tuwo miyar kuka duk an hado musu sai wanda kake so zaka zaba. A waya Suhaif ya zanowa Kukunsa abubuwan da zasu daddafa tun jiya da daddare suke aiki har wayewar garin yau. Lallai kuwa wannan kayataccen Breakfast ya burge wadanda aka yi dominsu. Suhaif yana dan cin abinci duk da dakyar yake iya hadiyewa saboda kallon soyayyar daya fuskanci Huzaifa yana yiwa Iman. Ita kuwa kanta a sunkuye a kasa ta kasa kallon kowannensu. Suhaif ya fake da yiwa yara wasa da yake Babansu ya koya musu turanci da fulatanci don haka da turanci Suhaif yake musu magana. Najib da Huzaifa sun barke da hirar da suka saba yi tun jiya, hirar dai bata wuce halin wahala da talauci da masu mulkin kasashe suka jefa talakawansu ba. Iman da matar Huzaifa suma sun juya harshe suna ta larabci. Haka suka kasance suna cin abinci amma kowa da abokin hirarsa. Bayan sun gama sai suka dunguma zuwa kujerun falo inda suka zazzauna. Wayar Huzaifa tayi kara kanwarsa ce Bilkisu. Bayan ta gaishe shi cikin yarensu fulatanci ta shiga nuna bacin ranta da damuwa akan kin zuwansu jiya. Ta ce har sha biyun dare ta hana direbanta tafiya dan yaje ya daukosu idan sun karaso amma taji shiru. Yanzu ma kamar da wasa ta gwada lambar taji ta shiga, wato da bata kira ba ma baza su bugo suce mata sun karaso ba ko? Huzaifa sai dariya yake yi ya dannan speaker yadda Iman zaya ji. Ya ce da kanwarsa "To kin gama tutsiyeni? Ga Iman tana jinki ita zata baki amsa. Iman ta ce "Bilkisu kiyi hakuri, ba haka bane. Ai yanzu zamu zo. Bilkisu ya ce "Kuzo ina? Aini yanzu haka ma bana gida, gani nan har zamu shiga jirgi zan tafi Lagos. Huzaifa ya kashe speaker, ya tashi ya fito baranda suna magana da kanwarsa ta sirri. Matarsa ta bishi barandar bayan ya gama waya ya juyo ya dubeta ya kirata da sunan masoyiyarsa cikin harshen larabci ya tambayeta me yake damunta ne? Ta shakwakkwabe ta ce ta gaji duk jikinta ciwo yake, haka kirjinta yana mata ciwo. Yayi mata sannu yayin da ya jawota ya rungumeta. Ya jawo hannunta ya ce ta zo ya rakata daki ta kwanta ta huta yanzu zai fita zai sayo mata magani. Iman tayi-tayi da yaran su zo wajenta su zauna kada su dami Mahaifiyarsu, suka ki suka bi Mahaifiyarsu daki. Bayan dan wani lokaci Huzaifa ya dawo ya ce da Najib "Bani mukullin mota zan je Gwarunfa yanzu zan dawo. Suhaif ya ce "Akwai direbobi a waje, mukullan motar na hannunsu ka zabi daya ya kaika. Huzaifa ya ce "Ba komai zan je da kaina, nima fa dan gari ne bazan bata ba. Sai su duka suka kyalkyale da dariya. Suhaif ya ce "Muje wajen motocin sai in karbar maka mukullin. Bayan Suhaif ya bawa Huzaifa mukullin motar, Huzaifa ya shiga suka yi sallama akan yanzu zai dawo ba dadewa zai yi ba sako kawai zai karbo. Suhaif ya dade annan a tsaye ya rasa me yake yi masa dadi, hakika idan ya ci gaba da zama kusa da Iman zai iya kasa controlling kansa ya fadi abunda Huzaifa zai gane halin da yake ciki. Sai kawai ya yanke shawarar ba zai koma cikin gidan ba sai ya nufi katafaren lambun da yake bayan gidan, ya samu lungu ya zauna yana tunani. Najib da Iman ne kadai ke zaune a falo suna *yar hira. Iman ta ce "Ina Yaya Suhaif, ko ya bi Hamma Huzaifa ne? Najib ya ce "Anya, naga giftawar Huzaifa shi kadai ne a motar, bari in leka watakila ya tsaya da masu aiki ko direbobi suna lissafi. Najib ya leko farfajiyar gidan yaga babu kowa, sai ya dawo falo ya zauna. Ya dubi Iman ya ce "Baya area nan ban san inda ya kutsa ba, yayi wani bangaren. Iman tayi ajiyar zuciya ta ce "Najib na tambayeka ka ki ka fadamin tsakani da Allah abunda yake damun Yaya Suhaif. Nasan dole akwai abunda yake damunsa, wallahi da kasan yadda na shiga damuwa da ka tausaya min. Ban san dalili ba tun ina Doko idan naga Suhaif yana cikin damuwa sai naji na damu. Kaga kamar lokacin da zai tafi bautar kasa ya ce baya so yaje kudu, Baba ya ce sai ya je damuwar da yayi tasa na rasa abunda yake min dadi. Zan tafi da damuwa a sanadiyyar damuwar da na bar Yaya Suhaif a ciki. A tunanina, na dauka dan zanyi aure ne ya sa shi damuwa, amma kace bashi ne damuwarsa ba. Yaya Suhaif mai fara'a, ga son wasa, ga shi da bayar da labari. Yanzu fa? Dubi halin da yake ciki, kace min kuma babu komai. Huzaifa dauke da Invitation card din bikinsa da Iman ya sako kansa cikin falon abun da kunnensa ya jiye masa shine Najib yaji yana cewa. "Iman kamar yadda kika sani Suhaif yana tsananin sonki tun kafin ku rabu, to ko bayan rabuwarku Suhaif ya kasance yana matukar kaunarki, kaunarki tasa ranar da za'a tantancesu a wajen daya sami aiki ya ki zuwa ya tafi garinku nemanki. Satin Suhaif guda a Jalingo yana nemanki bai ganki ba, ya dawo a lokacin angama daukan ma'aikata. Duk tsawon shekarun nan Suhaif ya kasa daure zuciyarsa ya auri wata, a koda yaushe yana fadin Iman yake jira, saboda na kasa son kowacce *ya sai Iman. Mun bashi shawara ya hakura ya barwa Allah idan ke rabonsa ce ko bayan yayi aure sai ku hadu kuma ya aure ki. Ya ce duk *yan matan da yake haduwa dasu basu da hali irin naki don haka idan bake ya aura ba ya hakura da aure a duniya. Ya mallaki komai na rayuwa, wannan gidan da muke ciki nasa ne amma shi kadai yake rayuwa a cikinsa saboda rashinki. A koda yaushe yana addu'a Allah Yasa ya ganki, haka makasudin zuwanmu Makka yanzu takanas don yayi addu'a Allah Yasa ya ganki. Allah Ya amsa addu'arsa ya ganki, amma a kurarran lokaci. Ma'ana a satin bikinki don haka ya shiga damuwa fiye da ta da kafin ya ganki. Iman ta runtse ido sai hawaye sharr-sharr yake zuba daga idanuwanta. Najib ya dubeta yayin da hawaye ya surnano masa ya ce "Ba kuka za kiyi masa ba addu'a da nasiha za kiyi masa a matsayinki na Malama ki nuna masa kaddarace da jarabawa daga Allah, a matsayinsa na Musulmi dole ya yarda da kaddara mai kyau ko marar kyau amma ni kaina ina tsoron halinda Suhaif zai shiga nan gaba, in dai ba Allah bane Ya saka masa dangana. Iman ta hau karkarwa jikinta da bakinta da kyar maganarta take fita ta ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hakika na tausayawa Suhaif kuma bani da abunda zan bashi ko in fada masa yaji damuwar da yake ciki ta gushe. Illa nayi alkawari zan dauwama har karshen rayuwata, ina mai yi masa addu'a Allah Ubangiji Ya yaye masa ya kuma bashi macen da zai so fiye da ni. Bayan rabuwata da Suhaif sannan na sake gaskatawa na tabbatar Suhaif mai sona ne, so na hakika kuma tsakani da Allah. Ya soni a lokacin da kowa ya ki ni, Suhaif ya tsaya a lokacin da kowa yake guduna. Suhaif ya lallasheni lokacin da kowa yake hantarata. Suhaif ya kirani da masoyiya a lokacin da kowa yake kirana makiyiya. Suhaif ya kira ni da