← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 80

Sashe 7

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

sannan ta zauna kan katifarta ta bude wasikar ta fara karantawa. Fuskarta kawai zaka kalla kasan tana farin ciki. Ta karanta ta sake maimaitawa, sai tayi doguwar ajiyar zuciya ta lumshe ido. Ta dade tana tunanin me zata rubuta masa. Bayan ta gama tunano meya kamata ta rubuta, sai ta jawo jakarta ta dauko biro da takarda ta fara tsantsara masa wasika. Ta fara da yi masa godiya game da alkawarin da yayi mata addu'a Allah Ya bata miji na gari mai sonta. Sannan tayi masa addu'a Allah yasa wacce yake so ta soshi sai dai ta bashi shawara ya kamata ya sanarwa wacce yake so kafin ya tafi kada yaje tunaninta ya dameshi. Ya kuma cire tsoro da fargaba da gudun ko ba zata soshi ba, ta tabbatar masa da cewa shi saurayi ne irin wanda kowacce *ya mace take addu'a Allah Ya bata kamarsa don haka tana tabbatar masa yaje ya tareta zata soshi kowacece yarinyar. Daga karshe ta bashi shawara ya guji zurfin ciki da yawa musamman a fagen so, domin a bari ya huce shi ke kawo rabon wani. Ta linke wasikar ta fito zaure, taga takalmansa abakin kofar dakinsa da alama yana ciki. Sai ta je ta dora wasikar akan takalminsa ta kwankwasa kofar sannan ta shige cikin gida. Suhaif na bude kofa sai yaga babu kowa yayi sauri zaisa takalminsa ya leka waje ko mai kwankwasa kofar ya fita sai yaga wasika. Ya durkusa ya dauka ya koma daki ya zauna ya bude ya fara karantawa. Wanan karon farin cikin daya lullube shi ya wuce yayi murmushi sai dai dariya. Ya kyalkyale da dariya shi kadai, ya mike tsaye yana kai kawo a tsakar dakinsa yana sake karanta wasikar. A zuciyarsa yana tambayar anya kuwa Iman ce ta rubito masa wannan wasikar ko kuwa shine bai karanta daidaiba. Ya sake murtsike idonsa yana karantawa yaga da gaske ne abun da yake gani. Sai ya koma ya zauna ya dauko biro da takarda ya fara rubuta mata wasika. Fargabar da yake a zuciyarsa ta kau, kai tsaye ya fayyace mata abunda yake ransa na game da soyayyarta data damki zuciyarsa. Sai dai yana rokarta don Allah taji tsoron Allah, Allah Yana kallonta kada ta boye masa ta fada masa gaskiya menene ra'ayinta game da soyayyarsa. Idan bata amince ba ta fada masa wannan ba zaisa ya damu ba kuma zumuncinsu na nan a matsayin kanwarsa ya dauketa. Daya gama rubutawa sai ya nade wasikar ya fito. Kafin ya fito tsakar gida sai ya hango Zubaida da Naja'at a bakin rijiya suna brush. Don haka sai yaji duk ransa ya baci bai so suka tashi daga barci yanzu ba. Ya koma daki ya dauko kofin daya sha koko ya fito. Maimakon ya kai wajen wanke-wanke da ya hango Iman a kicin sai ya nufi kicin din ya mika mata kofi, ta karba sai taga wasika ce a cikin kofin. Ya juya ya fita, Naja'at da Zubaida suka yi sauri suka duka suka gaishe shi. Ba tare da sakin fuska ba ya amsa musu, ya wuce ya fita kofar gida Iman ta zare wasikar ta soke a cikin zaninta sannan ta fito takai kofin wajen wanke-wanke. Ta shaidawa su Naja'at ga kokonsu nan a kwanan sha, suka amsa mata da "To mun gode. Iman ta shiga daki cikin sauri ta dauko wasikar ta bude ta karanta. Sai ta tsinci kanta da tsananin farin ciki, sannan ta sake tabbatarwa da kanta ashe wannan tsananin kunyarsa da take yawan ji ashe so ne, sai dai kash yanzu su Naja'at sun tashi sai dai wani lokaci. Ta bude can kasar jakar kayanta ta boye wasikun. Hankalin Suhaif ya tashi yaga har azahar Iman bata rubuto masa amsar wasikarsa ba. Duk motsin da yaji a jikin kofarsa sai ya leko yaga ko Iman ce ta ajiye wasika amma sai yaga wayam babu komai. Ya sake duba kan wundon dake zaure inda ta ajiye masa wasikar farko nan ma babu komai bata ajiye ba. Sai ya sake shiga damuwa da zulumi. Ya shiga cikin gidan baya ganin Iman tana daki a zaune. Da yamma ne ya hangota a kicin tana dora tukunyar tuwo. Naja'at tana daka daddawa, Zubaida na wanke-wanke. Gwaggo kuma na zaune a tsakar gida. Yazo ya zauna yaji duk hankalinsa baya jikinsa, Gwaggo na magana bai cika fahimtar me take ce masa ba. Ta dala masa duka a kafada ta ce, Wai kai yau meke damunka ne tun zancen tafiyar jiya ka bi ka susuce, kayi hakuri mana kasan fa halin mahaifinka sarai idan yace sai anyi to fa sai anyi gara ka kwantar da hankalinka kawai. Suhaif yayi murmushi ya mike tsaye ya ce "Ke ta tafiya kike Gwaggo ni abunda yake damuna yafi karfin damuwar tafiya. Ta ce "Meke damunka ka fada mun mana. Bai iya ce mata komai ba ya fice. Har dare bai ga amsar Iman ba sai ya tabbatarwa kansa Iman bata amince ba kuma tana kunyar rubuto masa a'a sai ya zauna ya bude sabon tunani mai dauke da tsananin bakin ciki. Bai iya cin abincin dare ba ko loma daya da yaga barcin ya gagara sai ya daura alwala ya dinga nafilfili yana addu'a yana kai kukansa wajen Ubangiji Ya taimake shi yayi masa agaji ya sami soyayyar wacce yake so. Hawaye ne ke kwaranya daga idanuwansa yayin da yake ganawa da Ubangijinsa. Shi kansa yana tsoron halin da zai shiga muddin Iman ta kishi har asuba yana zaune yana addu'a. Da yaji ana kiran assalatu sai yaji motsin mahaifinsa yana bude kofar gida zai je masallaci, yayi wuf ya fito suka dunguma suka tafi tare. Bayan an idar da salla wasu na zama suyi zikiri a masallacin har sai gari ya waye. Suhaif da mahaifinsa suka zauna suma aka yi zikirin dasu har sai da gari yayi tangaran sannan suka fito daga masallacin. A hanyarsu ta tahowa gida ne Suhaif yake bawa mahaifinsa hakuri akan zancen tafiyarsa bautar kasa da ya nuna baya so amma yanzu yayi tunani yaga yayi kuskure yanzu ya sawa zuciyarsa ba komai zaije din. Mahaifinsa yayi farin ciki ya dora masa da nasihohi masu ratsa jiki na kwantar da hankali. Suhaif ya wuce dakinsa, mahaifinsa ya shiga cikin gida. Suhaif na shiga daki sai ya kwanta ya runtse ido zatonsa zai iya barci saboda kansa yayi masa nauyi, idanuwansa suna masa tsaki-tsaki da alama dai barcin daya kwana bai yi ba ne yake tambayarsa. Amma ina! Barci ya gagara yazo, mummunar faduwar gaba data addabe shi idan ya tuna Iman bata amince masa ba. Bakwai da rabi dai-dai ya jiyo muryar Iman tana yiwa Gwaggo Sallama akan zata tafi makaranta saboda taron da za'ayi yau a makarantarsu har ana sa ran Mai Martaba Sarkin Gumel Alh. Ahmad Mohd Sani zai halacci taron bude wasu sababbin ajujuwa da masallaci da za'ayi a makarantar. Kasancewar Iman itace aka nada shugabar dalibai saboda kwazonta da kulawa da makarantar da take yi shine yasa, aka ce tazo da sassafe tasa yara su share filin makarantar a kamo bencina su fito dasu su shirya wajen da manyan baki zasu zazzauna.
Chapter 7 · 0% Book details