← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 80

Sashe 26

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wata rana da yamma ina ta riki-riki da itace da tukunya sun hadani da babban aiki wai tuwan shinkafa miyar taushe suke so. Ina gudun bacin ransu sai ban fada musu cewar ban iya ba fargaba ta isheni bansan yadda zan hada miyar taushe ba, ga dai kayan taushe reras na cefano. Na dora ruwan zafi ya tafasa na wanke shinkafar tuwo na zuba tana ta dahuwa.

Daya daga cikin kawayenmu da muka saba a sanadiyar abokan Micheal wato Fadila dadiron Gibrel ce abokin Micheal a gidan Gibriel din take din-din-din ya tsare mata ci da sha da sutura. Ya saka mata takun-kumin fita wajen wasu mazan. Amma abunka da ba maganar Allah ba, zama ne na sabon Allah tana satar jiki ta fita ta hole da wasu mazan idan yayi tafiya. Ran da aka sami akasi ya dawo bai isketa a gida ba to fa ranar saiya fasa mata wani wajen ajikinta don duka. "Excuse. Sallamar arna tayi min. Na daga ido na dubi me shigowa duk da boy's quater a wangale take babu zaure ba tsakar gida don ba'a zagaye da katanga ba ko zana a fili muke wangal sai dakuna biyu a jejjere da dan karamin bandaki a tsurkukin kicin. A filin bakin kofar dakin nake girki. Ina zaune akan wani katan bulo na saka rigar aiki iya gwiwa. Hayaki ya cika mun ido sai hawaye nake shar-shar.
Na tashi da sauri na rungume Fadila don munyi wata guda bamu hadu ba tun muna gidan Micheal.

Wa'iyazu billah,,,, Allah dan girman Ka da tsarkin Mulkin Ka, Ka tsaremu daga rayuwar bariki. Allah Ka da Ka sanyamu a jerin ta6a66u duniya da lahira.

Uhmm gaskiya ni bana son Iman din ma,,,, cikin biyu za'ai daya ko Naja'at ko kuma Zubaida ehe......

@watsapp__ 08097365237

YARENA, ADDININA.....

CIGABAN LABARIN
Na tsashi da murna na rungume Fadila don munyi wata hudu bamu hadu ba tun muna gidan Micheal.
Amma tunda muka dawo nan bata zoba. Sai a
ranar tazo shima da tambaya ta samu gidan.
Nadauko mata tabarmar kwanciyata daga daki
nazo na shimfida mata a gefe yadda hayaki bazai
dameta ba nace ta zauna. Amma fadila ta kasa
zama, tayi tsaye kawai tana kalle-kalle gidan da muke zaune. Ta dubi ko ina harda daga labulen
kofar dakin da mukayi da zani ta leka dakin sai
girgiza kai take ta juyo tadubeni cike da tausayi
tace "cafdijam pretty haka kuka zama? Yanzu
kune acikin gidan nan haka harsu janet da harriet
agidan suke zaune haka?' Na sun kuyar dakaina kasa na kasa bata amsa. Taje tazauna a tabarmar
dana shimfida mata nan ma kafinta zauna saida ta
karkade tana wani yatsuna kamar wacce zata
zauna akan kashi. Kirjinta da kunnuwanta da
yatsun hannunta da hannuwanta da kafarta
tsadaddu. Kanta babu dankwali anyi gyaran gashi a saloon anyi karin gashi har baya an zubo
dashi, sai kamshi da kyallin mai. Nace "Gabrel
yana sakar maki kudi fadila.' Nafada mata haka
yayinda nake dubanta ina murmushi. Nanfa
tahau feleke tana wata kwalmada tana iyayi
daman gwanace awajen feleke. ita ta koyamun hausa na iya magana da hausa sosai domin ita
bahaushiya ce gaba da baya kuma musulma
bakatsiniya. Tace "wai dan kinga nasa gold aiba
komai kika ganiba pretty. Gibrel fa ya bude mun
account yana zuba mun kudi sannan duk sanda
yaje lagos zai suyo mun kayan tsukewa da leshina. Idan yayi tafiya infita inje wajen wasu
mazan duk haka muke dani da kawayena su
Ngozi. Wallahi pretty bakida wayo bakima san
abunda kikeyiba. Koda yake yarinta na damunki
gaki kuma 'yar fari. Micheal fayafi su Gibrel kudi
da kika kwantar da hankalinki da kinji dadin rayuwarki. Naji labarin abunda ya faru kinban
kunya ko tsoron harriet kike? Danshi fa ba sonta
yake ba ita take sonsa shike yake SO duk mun
san abunda yake faruwa. jiya ma har karfe dayan
dare yakai a gidan da nake yana baiyana mun
har yanzu yana sonki ki yarda dashi, zai canza miki rayuwarki. Harriet din banza inhar kin yadda
zai kaiki gidan dako get din gidan su harriet baza
su iya tabawa ba balle su shiga suyi miki wani
abu. Yace ashiye yake ya kashe miki duk abunda
ya mallaka don shi arayuwarsa bai taba jin
yarinya da yaji yana kauna ba kamarki." ta dafa kafadata tace "haba kawata dubeki yadda kika
zama duk kinyi duhu. Wannan gashi naki har
baya kamar na turawa duk ya cukurkude kodan
mai bakya shafawa. Da yar gayu dake, kala ce sai
an wanke hannu kafin a tabaki yanzu kin zama
kamar bola. Wai girki da murhun itace haba pretty kinci baya. Garaki shigo bariki kiji dadin rayuwa
hajiyata. "NA fisge kafadata natashi daga kusa da
ita ina girgiza kai, kallo daya tayi min tasan ta bani
haushi, raina ya baci sosai. Najuya na dubeta
nace" fadila ki kularmin da abincin nan zanje cikin
ginin can yanzu zan dawo.' Na nuna mata wani tsohon ginin benen da ba'a kareshi ba, babu
kowa a cikin. Ta harareni tace 'me zakiyi aciki? To
gaskiya kiyi sauri idan baki dawo da wuriba zaki
tarar bana nan, donni ban saba girki a gas cooker
bama balle murhu kece dai wahalalliya.' Nayi
murmushi nace "yanzu zan dawo bazan dadeba." nadauki buta natafi kamar tafiyata da minti goma
nadawo. Fadila takalleni awalakance tace 'oh
kashima bakuda wajenyi sai kun shiga kwango?
Gaskiya pretty kin shiga uku. To in fada miki
gaskiya kece abar tausayi don jannet har yanzu
tana tareda solomon abokin micheal kudi sosai take samu shiyasa bata cika kwana anan gidan
ba kawai tana ciyar dake don ki kulada kawarta
harriet wacce tadauko ciki ba zata iya fantamawa
ba. Amma da harriet garau take bazasu yarda su
zauna dake a gidan nan ba. Ke kuma wawuya kin
tauye rayuwarki kin kunshe anan ki taho kawai ki biyoni. Nida nice da kyau irin naki daba saina
buga tsiya agarin nanba.." Nakoma kan bulon
dana zamar dashi kujera na zauna na bude
tukunyar girkina naga har yanzu ruwan
shinkafar bata tsotseba na rufe na gyara itace.
Najuyo na kalli fadila wacce ta zuba min ido tana sauraron amsar da zan bata. Nayi ajiyar zuciya
nace "fadila hankalina yana tashi jikina yana
sanyi duk lokacin da muka hadu. Zaki ga kome
janet,Harriet dasu Ngozi kawayenki zasuyi na
bariki da tabewa da maza bana ko daga ido in
dubesu saboda nasan ba musulmai bane." fadila ta zazzaro ido tana kallona cike da mamaki tace
'pretty nadauka duk addininku daya dasu,
nikadaice musulma acikin ku? Meyasa jikinki yake
sanyi idan kika ganni? Nasake zubo da hawaye
daga idanuwana. Nasa gefen rigata na sharce.
Nace fadila a matsayinki na musulma gaba da baya musulmar ma bahaushiya, bahaushiyar ma
bakatsiniya hausawan asali masu al'adu irin ta
larabawa. Nayi mamaki da rayuwarki ta zama
haka fadila na zauna da masu irin addiniki kala-
kala na tantance addininku addinin musulunci
addini ne me tsafta. Har mamaki nake idan naga musulmi yana bin arna yana bata. Domin dani na
samu Allah yayini a musulma hausa fulani
tsantsan na sami tarbiyyar musulunci tun ina
yarinya banga dalilin dazaisa na sabawa
ubangijina ba....
Chapter 26 · 0% Book details