← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 80

Sashe 46

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Iman ta tafi tabar Suhaif da tunaninta, begenta da tsantsar kaunarta. Baya walwala, baya son shiga mutane balle yayi hira dasu daga Masallaci sai dakinsa. Abincinsa kuwa idan yayi cokali daya, biyu, baya iya yin na uku sai yaji ya kasa ci. Babu abinda yake yi sai tunaninta wani lokaci ya debo wasikunta da hotunanta yana kallo. Sai ka ga hawaye ya surnano masa saboda tsananin damuwa. Abunda yafi tsaya masa a rai, shine irin wahalhalun da tasha a rayuwaarta shima yasa yaji ya kara sonta yana kuma tausaya mata yadda rayuwarta zata ci gaba da kasancewa bayan rabuwarsu. Yana ganin abu daya zai sa hankalin Iman ya kwanta a rayuwarta shine idan Allan Ya bata miji na gari mai tsoron Allah, mai sonta tsakani da Allah. Wannan mijin kuwa ba kowa bane illa Suhaif. Ina son Iman tamkar yadda nake son rayuwata, yadda bazan iya wulakanta rayuwata ba haka bazan wulakanta rayuwar Iman ba. Allah ka bani Iman. Ina zan sake ganinki Iman? Na rasa Iman na rasa mace ta gari, mai kirki, mai addini, mai kunya da tsananin tsoron Allah. Suhaif yana fada yana kuka.
Najib bai daina yiwa Suhaif nasiha ba har lokacin da ya shirya ya koma Kano. Mahaifan Suhaif basa jin dadin yanayin damuwar da Suhaif yake ciki. Suna ta bashi baki da nasiha kala-kala. Daga karshe Mahaifin Suhaif ya bashi shawara ya shirya ya koma Kano ko hankalinsa zai fi kwanciya, har Allah Yasa aikin da ake nemar musu ya fito. Suhaif bashi da zabi yasan Kano da Doko duk daya ne tunda ba Iman zai gani ba. Bai ki yarda da shawarar Mahaifinsa ba, ya shirya kayansa kakaf ya tafi Kano. Can ma bata sauya zani ba cikin damuwa yake, amma yana samun dan sanyi a ransa tunda koda yaushe Najib yana tare da shi dakinsu daya, su kwana su tashi tare. Ko zasu yi fada Najib bazai fasa fada masa gaskiya ba, yana cewa wannan damuwar daya saka a ransa babu abinda zata kara masa illa ciwo. Iman dai ta tafi zai yi wuya ta dawo dan haka gara ya barwa Allah komai, idan Allah Yaso zai sake hadasu kamar yadda itama Iman din ta fada sai su hadu. Tamkar dalmar wuta kalaman Najib suke yiwa Suhaif a zuciya, su Suhaif da Najib suyi ta fada wai dan me zai ce ya daina damuwa Iman ta tafi kenan. Daga baya Suhaif ya fara yadda da zancen Najib gaskiya ne babu alamar dawowar Iman, gashi wata da watanni. Sai ya fara bawa zuciyarsa hakuri yana daddaurewa yana fita wasu harkokin.
Baba Usman Mahaifin Najib ya shigo da wasu motoci guda biyu iri daya kalace kawai suka banbanta, daya kalar ja, daya kuma shudiya ce, motocin sababbi dal-dal a ledarsu, irin na zamani da kowanne matashi mai ji da kudi ko Mahaifinsa mai ji da Naira yake mafarkin samunta. Aka yiwa Najib da Suhaif albishir cewa ta su ce. Wai!! Wayyo Allah Najib yaji dadi har da ihu. Suhaif ma ya ji dadi sosai, suka je wajen Baba suka yi godiya suna baiyyana farin cikinsu. Baba yafi su jin dadi ganin yayi musu gwaninta kuma wadanda yayi dominsu sun gode.

Wai meya sanya wasu suke cewa ba'a tashi inda aka tsaya ne? Wa ya fada musu ana tsallake?

Gimbiya Zarah Matawata kenan ta ce ta ji dadi da ba'a mance da ita ba a wannan dandali..... lolxxx

*************** YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI

Dole in damu saboda nasan meye sanadin mutuwar tasu. Shi yasa nake kaffa-kaffa ko da Malamina ko a kawayena *yan ajinmu nake gudun hatsaniya ta hadamu, da zarar sun harzuka sai inyi ta basu hakuri, amma suki hakura lallai sai sun daga murya asan muna fada, rashin sani sai su zazzageni. Zasu kwanta da daddare lafiya zanyi mafarki an kashesu da safe za ace min sun mutu. Da naga anyi haka sau daya, sau biyu, kafin ayi na uku sai na hada kayana cikin dare zan gudu in bar garin. Niyyata kuwa inkaura dokar daji inyi rayuwa da namun daji in sun gaji dani su cinyeni. In shirya kayana in fito inyi ta tafiya, sai naji hankalina ya dauke in fadi in yi ta barci, sai in yi mafarkin matsafan sun daukoni aka sun dawo dani har dakina kan shinfidata. Ina farkawa daga barcin a shinfidata zan ganni, inyi ta mamaki. Mun yi haka dasu yafi a kirga. Da ga karshe dole na hakura na zauna. Amma basu dai na hadani fada da jama'a ba suna kashesu cikin dare. Allah cikin ikonSa jama'a basu gane ba har sai da Maimuna *yar garinmu tazo ta tona min asiri. Ta fadi gaskiya bata yi karya ba, ta sanni sosai duk da ba kawarta ba ce kawar kannen Hamma Huzaifa ce su Bilkisu Islamiyyarsu daya.
Bayan na sha kuka da takaicin tona asirin data yi min, sai bacci da ciwon kai ya kamani. Hakika gangar jikina ce a kwance ruhina ya tafi wajansu, ranar raina a bace ina ta zaginsu akan su rabu dani, su rabu da jama'ata. Nayi-nayi inyi addu'a Allah bai bani ikon yi ba, ina ji ina gani suka kashe Maimuna. Su Baba, su Goggo a kaina suna tashina ban farka ba sai da kurwata ta dawo, na farka daman ba bacci bane. Ina tashi kuwa na samu labarin Maimuna ta mutu, daman ko basu koreni ba dole in kori kaina.
Bayan na tafi samari suka bini zasu dake ni, to tun daga nan na rasa hankalina, suka turani tsohon ginin gidan Mahaukacin nan na shiga. Sun sami yadda suke so, Musulmai sun koreni, na zama ta su kenan. Na zamo a zaune kawai nake sun zagayeni babu ci babu sha, babu alwala bare salla, bana magana balle inyi addu'a. Gagarumar liyafa suka hada cikin dare a cikin gidan don murna, yau na zama tasu, yau sunci galaba kaina. Mutanen da nake so wato Musulmi sun kore ni daga cikinsu kwata-kwata. Ta kai ta kawo na ma daina ganinsu a mafarki ido biyu nake ganinsu. Suhaif ya ga jini an diddiga tun daga kofar gidan har cikin dakin dana ke, su suka disa akan takalmana, suka daura takalmi daya a akan saman rufin dakin yana diga, daya kuma yashe a tsakar gida da jini a jikinsa. Sunyi haka ne don Suhaif ya gani ya shaida ni mayya ce, suka daura min jajayen kyalle a jikina, sai daga baya na ciccire.
Suna fakon Suhaif sosai, sun kudiri niyyar sai sun kashe shi, saboda shine kadai ya rage mai takura musu da addu'a, shine bai tsane ni ba, bai rabu da zuwa inda nake ba. Babu makawa sun gama shirye-shiryen kashe shi tsaf a cikin daren dana ce masa ya kwana yana sallah yana addu'a kada yayi bacci. Da suka je zasu kashe shi suka kasa shiga inda yake balle su ganshi su kashe shi, sai suka kufula a daren kwana suka yi suna gana min azaba. Ban damu ba tun da mutuwa nake nema.

Babu wadanda suka jawo min wannan matsananciyar rayuwa sai Mahaifana, tun farko da na hadu da Matsafan da sun hadu sun taru sun rabani dasu da karfin addu'a da haka bata faru ba, duk da nasan kaddara ce. Amma kowannensu addininshi daban, wannan yana jin haushin wannan, idan ya kawo mai addu'arsa yana ganin kara min ciwo ake, kawai sai rigima ta harde su, daga karshe suka kyaleni da ciwo yana bibiyata har girmana. Duk lokacin da waninku ya hadu da dangina ku shaida musu abubuwan da suka faru dani har izuwa mutuwata. Nasihata zuwa ga Mahaifana itace su dawo su rungumi addinin Musulunci, suma su mutu a cikinsa kamar yadda nima zan mutu Musulma.

Iman ta rushe da kuka mai tsanani sai jama'a da dama a wajen tausayinta yasa su kuka suma. Cikin kuka ta dukar da kai kasa ta ce "Na gama labarina ku kasheni kamar yadda ku kayi alkawari, na gaji da rayuwar wulakanci da kyama da tsangwama a cikin *yan uwana. Kafin wani ya bude baki yayi magana, ganin Iman akayi ta daka tsalle ta fadi can gefe kamar wani ne yayi ball da ita. Sai ta tashi a gigice tana kallon wani gefe tana magana kamar a kwai wadanda take gani mutane basa gani. Cikin harshen Turanci take magana take cewa "Ku rabu dani, karku matso kusa dani, baku zaku kashe ni ba, ku bar *yan uwana Musulmai su kashe ni. Suhaif yana jin haka ya tashi da gudu ya fisgota ya kawota tsakiyar Malaman yana fassara musu abunda yaji tana fada da Hausa. Sai suka gane cewar matsafan sun zo su kasheta saboda ta tona musu asiri. Yanayin halin da suka lura Iman na ciki shine matsafan suna rike da ita suna shirin su kasheta.
Chapter 46 · 0% Book details