← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 80

Sashe 21

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

Cikin gaggawa Mahaifina ya hadamin kayan tafiya kamar sababbin dinkuna na zamani, privision. Takalman gayu akwatina masu tsada littafi biruka, Pencil da dai sauransu. Ya kaini har Bauchi
Da kansa ya tayani muka yi registration saida ya tabbatar ya kammala mun komai. Ya biyamun kudin daki a hostel dake cikin makarantar. Yayi min fada sosai in tsaya inyi karatu kamar yadda shi da Mahaifiyata suka yi suka fito da first calass degree. Har ya zazzagaya dani wasu wurare a makarantar yake nunnunamin inda suke zama da Mahaifiyata suyi karatu tare. Don haka kar in biyewa kawaye marasa son suyi jaratu. Abu daya Mahaifina ya bani mamaki da bai taba yimin fada akan in rike addinina ba, har yayi min fadan ya gama ya shiga mota zai tafi naga baiyi min zancen addini ba. Sai na ce "Daddy baka ce in rike addinina ba. "Ya tsaya yana kallona kwai ya kasa magana. Sai hawaye ya zubo daga idanuwana, na ce "Daddy ko dan ba addininmu daya ba? Jikinsa yayi sanyi hankalinsa ya tashi sosai. Cikin harshen fulatanci na yi magana na ce "Bakar saniya mai cin ciyawa koriya ta bada farin nono. Ya sake zare ido yana kallona, saina juya na tafi hostel ina daga masa hannu. Ya kifa kai akan sitiyarin motarsa, yafi minti goma sha biyar bai tafi ba yana tunani da hawaye. Ina lekensa ta daki, sannan ya share fuskarsa ya ja mota ya tafi. Daga Bauchi sai ya shiga Gombe garinsu don ya gaishe da Mahaifiyarsa da danginsa, duk da yana gani a fuskokinsu basu bukatar ganinsa sun ma cireshi a dangi haka kuma ko kyautar kudi ya yiwa Mahaifiyarsa bata karba kome ya sayo bata ci. Kuma duk sanda ta ganshi sai tayi kuka, dan haka hankalinsa yana tashi idan yaje Gombe sai ya rage zuwa sosai jifa-jifa.

Allah Ya tsaremu daga sa6awa Iyaye maganarsu. Ameen

Sai kuma Allah Ya kaimu gobe da yaddarSa.

Ina cigiya wanda yake da wannan littafin a hannu pls.

Reedwan Suraj Isma'il

"""""""""""""""""" YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN

Na hadu da kawayena Harriet da Janet suma kuma duk cours dinmu daya. Ranar da muka fito daga lecture farko su Janet suka cemun ga wani abokinsu sunansa Micheal yazo daukarsu zasu je suga gidansa dake New G.R.A. Wai inzo in rakasu. Na ce meyasa zasu tafi bayan da yamma muna da lecture? "Suka ce "Ai yana da mota zai dawo damu kafin lokacin. Fadan da Mahaifina yayi min shiya fado min a rai, ya ce kada inyi kawance da wadanda basa son yin karatu. Sai nace su je ni ba zani ba. Suka takura mun, Micheal din ma ya zo yasa baki wai in daure inje yanzu zamu dawo a matsayinmu na baki a Bauchi shi kuma dan gari shine yake so ya nuna mana gari da gidansa. Ko ba komai dai mun san wani, koda muna bukatar wani abu, shi kuma zai rikemu a matsayin kannensa zai taimaka mana. Naji lafazinsa masu sanyi na shiga mota muka tafi. Ashe daga wannan tafiyar ba zamu sake dawowa mu shiga lecture ba. Gidansa mai kyawun gaske mai dauke da dakuna uku kowanne da bandakinsa. Falo babba, kicin cike da abinci kala-kala ga kuku mai dafawa ya jera a dining area. Ko'ina a gidan sai sanyin A.C, wannan gidan daya ne daga gidajen Micheal da babansa ya mutu ya bar masa ne, ga tulin dukiya. Sai yace mu zauna a gidan kawai ba sai mun koma zaman hostel ba, shi kuma zai tafi sauran gidajensa daman ba'anan ya fiya zama ba, ya ce mu zauna mu kadai kowacce da dakinta. Ina son gidan amma nayi tunani naga ba yadda za'ayi haka ta yuwu domin hostel Mahaifina ya kaini. Na ce musu ni tafiya zanyi bazan zauna ba. Harriet ta dinga mun masifa wai danme zance bazan zauna ba, bayan mu kadai ne a gidan ba iskanci za muyi ba, ga direba zai dinga kaimu lectures. Ni dai nayi shiru ina tsoron masifar Harriet amma ba dan raina ya so ba. A hankali su Harriet suka je suka kwaso mana akwatinan kayanmu daga makaranta kowacce tasa a dakinta. Sai mun shirya tsaf da litattafanmu zamu je lecture direba yazo ya daukemu sai inga anyi ZARANDA HOTEL. Sai in tambaya "A'a ba makaranta zamu je bane? Sai suce wai Micheal zasu gani a dakinsa na hotel yanzu zamu fito mu tafi. In zauna a mota ina ta jiransu su shiga ciki su dade sai ni sai direba a zaune a mota ina tsaki ina duban agogo. Can sai inga Micheal ko wasu abokansa su Debid, Solomon, Gibreal, Emeka da sauransu su zo suyi ta rokona wai in shigo ya zan zauna a mota, ga rana inzo mu shiga. Su dameni dole sai sun takura mun na shiga. A dakin hotel din nan ake zama ana hira ana ta ciye-ciye. Abin yana ba ni mamaki yadda na ga kawayena Harriet da Janet sun saki jiki ko fargaba ba sa yi, sun saba da mazan nan har tafawa suke yi, suna cin abinci tare suna kwantowa akan cinyarsu. Ashe daman ni suke yi wa dabara, samarinsu ne tun sanda suka fara zuwa. Ni dai ina makale da littattafaina na takure a lungu idan raina yayi dubu ya baci. Duk wanda ya matso kusa dani a cikin mazan sai inyi zumbur in mike ina shirin buda kofa in arce, sai Micheal ya yiwa abokansa tsawa ya ce, su kyale ni. Kome a ka kawo gabana na ci ko nasha sai in ki ci ko sha, suka yi ta roko na in ki. Idan suka gama ciny-ciye da shaye-shaye har da giya sai su ce za su shiga dakin disco su yi rawa inzo mu je, in ki zuwa. Micheal ya miko min jarida wai in kwanta in yi ta karantawa kafin su dawo, su fice su bar ni. Na fashe da kuka mai tsanani, na yi tunani bari kawai in tashi in fita in hau acaba, in yi tafiyata makaranta, sai in ji ashe sun datse ni ta baya, na dawo na zauna na sharbi kukana. Sai da yamma likis sannan direaba ya mayar damu gidan da muke. Ina shiga na hau hada kayana zan tafiyata makaranta su Janet suka hanani tun suna rokona da lallashi har ta kai ta kawo sun fadamun baro-baro ba zan je ba ni in je inyi karatu, idan na koma Jalingo in yada su a gari in ce ba karatu suke ba iskanci suke. Suka karanto min manufarsu shine in kwantar da hankali muci kudi kawai ba wahalar karatu. Idan muka sami kudin sai mu biya lecturers dinmu su ba mu marks. Akwai yarinta a tattare da ni ga rashin sani don a lokacin shekarata goma sha biyar kacal duk sun girmeni. Sai na yarda na saki jikina a gidan mukayi ta cin dadi. Kuku ya dafa mana abinci kala-kala. Micheal ya zo ya daukemu ya yawata gari damu, super markets kala-kala kowacce ta dauki abin da ranta ke so na ci ko kayan tsukewa jeans, t-shirt, takalma da dai sauransu.
Amma ko alama ban taba ganin wani daga cikin samarin nan ya neme ni da iskanci ba za su zo gidan mu zauna a falo mu yi ta hira. Dama ni ba na binsu Zarandah Hotel. Idan zasu je club su yi rawa. Su yi su yi da ni sai na ki, in shige dakina in kulle, ina kallon films. Su Harriet da Janet dai suna zuwa, kuma ko alama ba sa nuna min suna iskanci da mazan nan. Na san dai suna fita su dade su kai har sha biyun dare.
Chapter 21 · 0% Book details