← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 80

Sashe 29

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

Iman ta ce "Nayi kuka, nayi takaici har kamar zan zautu. Daga karshe na dangana, na yiwa Maman Huzaifa sallama ita kuma taci gaba da bani baki tana kara karfafamin gwiwa akan ko ba Huzaifa ita zata maye gurbinsa iya karfinta zata taimaka min duk abinda ya cushe min na game da addini in zo in tambayeta zata warware min. Sannan duk lokacin sallah in dinga yin wayo ina sulalo jiki ina zuwa dakinta ina yin sallah a boye a ranar da Mahaifanki suke gida. Na mata godiya na fito na nufi hanyar gidan mu. Kafin na iso gida nake jiyo kukan dan Jaririna a Boy's quater, da alama wanka Mama Tabita take yi masa. Hankalina ya tashi na nufi inda suke da sauri ina tunanin idan an gama yi masa wankan wanne kaya za'a saka masa gashi bani da kudi. Na isa inda suke kan baranda na zauna a gefe ina kallonsu sai wanke shi take da sabulu. Ta juyo ta dubeni ta ce "Ashe ko wankan haihuwa ba'ayi masa ba. Yau ki ka haife shi ne? Na sunkuyar da kai kasa na ce "Jiya da daddare aka haifeshi. Tabita ta maimaita abunda na fada, "Jiya da daddare aka haifeshi. Ban sake cewa komai ba. Ta ce in shiga dakinta cikin akwati in dauko wankakkiyar atamfarta in kawo ta lullubeshi. Na tashi na shiga dakin na dauko zanin na kawo mata ta lullebeshi. Sai tsotsar hannu yake saboda yunwa. Ta jawo dan kwandon kayan kwalliyarya ta dauko mai basilin tana shafa masa. Ta ce "Bari in gama shafa masa mai sai ki karbe shi ki bashi nono ya sha yunwa yake ji. Ko babu ruwan nonon bai fara zuba ba? Nan fa gabana ya fadi na ce "Eh bai zo ba. Cikin rawar murya na fada. Tabita ta kalleni ta ce "Pretty ki kwantar da hankalinki, ki rungumi danki, ba'a kanki aka fara ciki ba a haihu, ashayar da dan ko ruwan nono bai zo ba dole ki bashi ya dinga sha har ruwan ya zo. Nan ma gabana ya sake faduwa na ce "Mama Tabita ba sai na bashi nono ba, ina laidar da kika karba a hannuna akwai Madararsa a ciki. Tabita ta nuna min inda ta ajiye ledar. Na tashi na shiga kicin na dauko kofi da cokali na tarar da wata katuwar tukunya cike da ruwan zafi akan murhu yana ta tafasa, wai ruwan wankan jego ta dora min. Na dibi kadan a kofi na zo na zauna a kusa da ita na dama madarar na firfita ya huce sannan na mika mata, ta dinga tarfa masa yana sha har ya koshi. Bacci mai dadi ya kwashe shi, ta tambayeni ina kayan sawarsa a saka masa na ce "Bashi da kaya. Cike da mamaki ta sake tambayata "Ina Mahaifinsa? Nayi shiru can na ce "Yana Bauchi, ta ce "Baisan kin haihu bane, ko bai karbi cikin bane ya kyaleshi tsirara? Na sake yin shiru can na ce "Yasan an haifeshi mana. Tabita ta girgiza kai don tausayi ta tashi ta shiga daki da jaririn, ta kwantar dashi akan katifa ta dauko Jakarta ta fito. Ta kalleni ta ce "Bari inje kasuwa na siyo masa riga ko guda daya ce kafin muga yadda za'ayi. Na laluba cikin ledar da na zo da ita na zaro sauran kudina daya rage na bata na ce ga sauran kudina ki hada ki siyo masa. Ta karba ta zuba a jaka sai ta ce min "Ga ruwa can a murhu idan ya tafasa ki juye kiyi wanka. Ko baza ki iya juyewa ba saboda jikinki ba kwari in zauna idan ya tafasa in juye miki in miki wanka yadda zaki gasu sosai? Nayi sauri na ce "Yi tafiyarki zan iya juyewa, zanyi wankan da kaina. Ta amsa min da to ta tafi ta nufi kasuwa. Tana fita na tashi na debi ruwa dai-dai wanka, na kwalfe sauran na zubar a rariya na kashe wutar. Na shiga nayi wankana da soso da sabulun sosai saboda nayi datti da yawa. Bayan na shafa mai nake tunanin kayan da zan saka, don kayana kakaf na baro su a can Bauchi, kuma sauran da na bari suna cikin gidanmu a dakina, bazan iya shiga gidan ba ina tsoron arangama da Mahaifana. A gefen katifa na takure daure da tawul ina kallon kyakkyawan jariri mai kama da Ubansa sak, sai addu'a nake tofa masa Allah Ya sa kada ya biyo halin uwarsa da ubansa. Allah Yasa Musulmi ne mai yiwa Musulunci hidima. Shigowar Mama Tabita ce ta katsemun tunanin da nake. Ta shigo dauke da leda, tana shigowa ta mikomin ledar na karba na bude. Riguna ta siyo masa kyau kala biyu, da *yan wandina (panties) na manya shima biyu. Ta ce "Wandinan manyan naki ne, "Na yi murmushi na ce "Na gode Mama Tabita. Ta farke riga da wando daya ta sakawa Jaririn ta sake kwantar da shi tana jijjigashi har ya sake komawa bacci. Muryar Mahaifiyata ce ta daga mana hankali tazo bakin kofar dakin tana ta bugun kofar tana fada "Tabita yau ba zaki fito ki dora mana abincin rana bane? Yanzu karfe goma sha biyu da rabi na rana ga yara sun fara jin yunwa. Aikin abinci na dauke ki ko aikin jego? Tabita ta hau rawar jiki tayi wuf ta fito tana bawa Mahaifiyata hakuri. Ita kuma kamar sake zugata ake sai fada take. Fadan dai Tabita ake yiwa amma maganar duk tawa ce. Wai ita babu ruwanta in rube mana ni da Jaririn kada Tabita ta sake makara bata dora abinci ba kuma ta tabbatar ta gama musu kowanne aiki kafin ta je ta fara gyara wani shegen Jariri. Na yi shiru sai kwalla nake nasan sai mun wulakanta ni da yaron nan, in ma ba'a koremu ba daga gidan. Ina zan je in zauna ni da Jaririn nan idan aka kore mu? Nake tambayar kaina da kaina.

DUK WANDA BAISAN AN QARA DA YAMMA BA YA SHIGA WAJEN "SHOW MORE" ZAI GANI
Sannan ba'a kammala na 1 ba yau da yammacin insha Allah Surayya Abukar zata karasa.

Reedwan Suraj Isma'il

YARENA ADDININA
CIGABAN LABARI.
Chapter 29 · 0% Book details