← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 80

Sashe 32

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mahaifiyata ta wuce tana fada, Tabita tana rawar jiki ta shigo ta dauki mayafinta ta fita. Har ta fita, na tashi da sauri na ce "Mama Tabita ki dauko min kayana set daya a durowata zan saka, ta amsa min da to ta tafi. Bayan tafiyar Tabita da minti biyar sai ga kanwata Rabecca ta shigo ta tsaya, ta kalleni ta kalli jaririn cikin harshen turanci ta ce min "Aunty Rufkatu kizo inji Daddy ki dauki kayan da kanki, Mama Tabita ba zata dauko miki ba. Na amsa mata da "To ina zuwa. Ta fita ta tafi, a zaune nake ina tunani wai me suke nufi da inzo da kaina? Shiguwar Mama Tabita ce ta katsemin tunanina, ta shigo da sauri ta ce "Pretty dauko yaron ki fito kizo muje gidan ki roki Mahaifanki gafara tun da sunyi fushi dake. Duk fadan da zasu yi miki suyi miki yanzu ki huta. Babu yadda za'ayi keda jaririn nan ku zauna cikin kunci da rashin gata. Na girgiza kai na ce "Ba zan shiga gidan ba "Tabita tayi ta lallashina dakyar na yadda na dauko mayafi na lulluba, ta mikamin Jariri na karba muka fito. A kicin Tabita ta labe ta ce in shiga cikin falon. Na kwankwasa kofar na shiga, gaba daya suka dago ido suna kallona na sunkuyar dakai kasa na wuce sum-sum cikin dakina, ina shiga na kwantar da Jaririn akan gado na bude durowa ta kayana na dauko wani leshi yellow riga da siket da dankwali na saka. Mahaifiyata ta shigo a fusace ta harari dan Jaririn dana kwantar akan gado, ta juyo ta harareni ta ce "Ki kwaso kayanki kakaf ki koma wancan dakin ki barwa Rabecca dakinta, kije can ki karata keda buhunhunan abinci. Na zubo da kayana kakaf akan gado na warware wani dan kwali na zuba na daure. Ta sake daka min tsawa "Kizo ki dauke wannan yaron kafin ya jikawa yarinya gado da fitsari. Na taho da sauri na dauke shi zuciyata cike da bakin ciki. Muryar Mahaifina naji ya kugamin kira cikin kakkausar murya, jikina na rawa na amsa na fito Mahaifiyata na biye da ni. Ya nuna min tsakiyar falo kan kafet ya ce inzo in zauna shi kuma yana zaune akan doguwar kujera. Mahaifiyata tazo ta zauna a kusa da shi. Ta juya ta kalli kannena ta ce "Su tashi su fita, ko su shiga dakinsu suyi kallo. Cikin fushi Mahaifina yake magana, cikin harshensa na fulatanci ya ce min "Fatima kin bani kunya, kin bani mamaki. Abunda kika yi kin kyautawa kanki kenan? A kwai wani yaro dan nan garin ne, dan abokina ne ya sanki, kece baki sanshi ba shima a ATBU yake tun wancan satin ya dawo gida sun gama jarabawa, na tambaye shi ko yana ganinki a makaranta? Ya shaidamin bakya makaranta, ya takaicemin yace sunanyenku na nan kafe an fitar da result an rubuta an koreku kwata-kwata, bakwa cikin makaranta kuna can kuna yawan iskanci. Baki taho min da result din jarabawa ba sai kika taho min da result din yawan iskanci kamar shi muka turaki. Kaina a sunkuye a kasa hawaye nake. Tun da nake da Mahaifina bai taba nuna min bacin ransa ba balle ya fada min bakar magana, tsakani na da shi sai wasa da dariya da nasiha. Ya dakamin tsawa gami da kawo min duka da gefen hannunsa na goce ya ce "Ba tambayarki nake yi ba kika yi shiru kina min kukan munafunci? Na ce sakamakon jarabawar kenan kika kamo hanya ki shigo min gida da goyan shege? Na sake rusa kuka, na kasa magana. Mahaifiyata ta tambayeni ta ce min "Waye uban dan? Nayi shiru ban amsa ba. Ta sake daka mun tsawa "Waye yayi miki ciki? Na share hawaye na ce "Ina so inyi bayani. Mahaifina ya daka min tsawa ya ce basa son bayani na, in amsa musu tambayar da ake min. Waye uban dan? Cikin rawar murya na ce "Wani ne mai suna Micheal a Bauchi yake. "Micheal suka hada baki suka maimaita. Na gyada kai na ce "Eh. Mahaifina bai kara magana ba ya koma ya jingina da kujera. Mahaifiyata sai ta hau murmushi. Abun ya bani mamaki. Ta gyara zama ta ce "Meye addininsa? Nayi shiru can na ce "Addinin ku daya. Ta harareni ta ce "Addininmu daya banda ke? Taci gaba da cewa "Naji dadi da Allah Ya sa addininmu daya, kina da labarin Mahaifinki da kannanki mun zama addini daya muke bi, kin ci sa'a kuma ga uban danki addininmu ne. Na daga ido na kalli Mahaifina sai ya kawar da kai gefe. Hawaye mai radadi ya zubomin. Dukkansu sun gane banyi farin ciki ba da wannan sabon labari dana ji, sunsan yadda nake kin addinin tun ina karama, su kan rasa to ni me nake bautawa. Na dora Jaririn akan kafadata ina jijjigashi don ya tsula min fitsari ya jikani ya hika zanin da aka nade shi. Nayi gyaran murya cikin marainiyar murya na ce "Nayi kuskure, nayi laifi, ku yafemin. Nima ba da son raina ba na bar makaranta inda ku ka turani karatu. Wannan yaron da kuke gani ba dana bane tsintarsa nayi. Su duka suka yo kaina kamar zasu cinyeni danya tun ban dahu ba don masifa, kowannensu na zagina da yarensa. Wai in rufe musu baki basa son karyar banza, su zan mayar yara. In tashi in basu waje kafin suyi ball dani da Jaririn. Na tashi cimak ina rusa kuka na nufi dakina da aka nuna min aka ce in koma in bar dakina na da. Tabita ta biyoni dakin ta fara lallashina ta ce inje kicin in zauna bari ta share mana dakin ta kade kura, ta shimfida mana wankakken zanin gado a tsohuwar katifar dake jingina a dakin. Haka kuwa akayi, ni da kayana kakaf na dawo dakin nan. Tabita kullum na shigowa ta yiwa yaron wanka ta bashi madara nima ta kawomin nawa abincin. Sabida tashin hankali bana iya ci sosai. Allah Ya dubi zuciyata Yasa yaron ba mai rigima bane sosai. Baya min kukan dare duk da wataran a dakin Mama Tabita yake kwana idan mijinta yana aikin dare, me gadin gidan mu ne watarana ya kwana wata rana wani ke canjarsa. Tana kula da ni sosai da jaririn. Tana gasa masa cibiyarsa dare da rana da safe don haka a kwana uku cibiyar ta fadi. Mama Tabita tana kula dani, ko kadan bata ga alamar jego a tare dani ba audugar matan data siyo min tana nan ko budeta ban yi ba. Ga fama da take dani saina bashi nono, ni kuma naki sai dai madara. A tsanake take tambayata gaskiyar al'amarin nan. Na zauna na bata labarin abunda ya faru tsaf. Ta gamsu dani ta kuma kara tausayamin da dan Jaririna. Ta ce min ba dan Mahaifana zasu ga laifinta ba, daman yanzu ma harararta suke idan suka ganta da yaron, da taje ta basu labarin abunda ya faru, amma ba zasu saurareta ba, na ce kawai ta kyalesu. Ranar da muka yi sati biyu da dawowa, da misalin karfe daya da rabi na rana, na fito daga gidansu Hamma Huzaifa da goyon dan Jaririna a baya. Na je sallar azahar kasancewar Mahaifiyata tana gida yau asabar bata je aiki ba. Sai naga wata mota katuwa baka kirar CRB tana biye da ni ana min hoon. Na juya na dubi motar sosai sai naga babu abinda nake gani kasancewar gilasan an fentesu sunyi duhu, kuma ban taba sanin me irin wannan motar ba, sai na sawa raina ba dani suke ba. Na juya naci gaba da tafiya na nufi hanyar gidanmu. Dai-dai get din shiga naji an sake matsa hoon an ja burki an tsaya dab da bakin get dinmu. Har na bude karamin get zan shige sai dai na sake juyowa na dubi motar. Sai naga an sauke gilashin. Yanzu ina iya ganin samari guda biyu a cikin motar gabadayansu sanye suke da kwabta-kwabtan bakaken gilasai a idanuwansu. Ina yiwa dayan kallon sani amma na kasa gane ko waye. Suka bude kofofin motar suka fito suka tunkaro ni suna min murmushi gami da kiran sunana "Pretty. Nayi kasake ina kallonsu naga da gaske ni suke tinkarowa sai na tsorata naja da baya, dogon sosai ya zare gilashin dake fuskarsa ya ce "Pretty baki gane ni bane? Kallo daya na yi masa ba gilashin na gane shi Micheal ne. Wata uwar tsana da takaici da tuna baya suka ruftawa zuciyata. Sakon daya yayi yawa annurin fuskata kakaf suka gushe, na bata rai, na murtike fuska tamkar naga kashi mai tsutsa naja dogon tsaki gami da wata uwar harara na kada kai na fada get din gidanmu, suka yi wuf suka biyoni ciki. Micheal na rawar murya yana magiya in saurare shi inji sakon da ya zo min dashi, bai isheni kallo ba balle in saurari maganarsa. Ficik naji an fincikoni inda nake tafiya a arewa naga an juyo dani kudu. Micheal ne ya fisgoni ta baya. Cikin fushi na fara zaiyano masa kalaman batanci, da zagin da ban taba yiwa kannena ba balle kawayena ko balle uwa uba na gaba dani. Ransa ya baci ya dakamin tsawa ya ce "Ya isa haka, kanki ya zare ne, don me zaki ce in bar kofar gidanku bayan ga dana kina goye dashi. Na fusata na ce "Danka? Ya aka yi ya zama danka, daman kana da da? Ya sake fada cikin fushi "Ki bani dana sai kiga nabar zuwa gidanku. Na sake fusata na ce masa "Ban gane abunda kake nufi ba. Ya aka yi wannan yaron da nake goyo ya zama danka? Dan makwabtanmu ne na daukko raino. Yayi murmushi ya ce "Pretty kin dauka bani da labarin Harriet ta haifar min cikin da nayi mata? Ko bani da labarin ke kika dauki yaron? Wannan abokin nawa dan garin nan ne, bayan haka munyi waya da Fadila ta fadamin kakaf abunda ya faru, na nemo wannan abokin nawa a waya na sanar masa na masa kwatancen gidanku na ce ya zo ya bincika mun kin zo da jariri? Ya ganki da idonsa goye da Jariri da yayi kama da ubansa. Ko kin manta nasan gidanku, mun taba zuwa daukarki? Dan haka na shiryo nazo takanas dan inga dana. Nayi shiru tamkar
Chapter 32 · 0% Book details