← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 80

Sashe 23

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 7 min read

Hutu ya kare zan koma makaranta, Hamma Huzaifa ya bani carbi da littafin addu'o'i saiya dauko kudi ya bani me yawa. Da farko naki karba ganin ba aiki yake ba, shima a jikin Mahaifinsa yake samu duk da Mahaifinsa mai hali ne. Sai ya ce kada inki alhairi, Musulmi dan uwan Musulmi ne. Kyauta tana kara dankon zumunci. Ya karamun da cewa in zama mai kyauta da son mutane duk da yasan halayena ne. Yayi min nasiha da in rike sallah kada inyi wasa da ita kuma inyi akan lokacinta. Mahaifana sun hadamun duk abunda zan bukata. Zasu sa direba ya kaini nace kawayena su Harriet zasu zo su daukeni a motar gidansu kamar yadda suka shirya min suka ce in fada, amma Micheal ne ya zo ya daukemu muka tafi. Ko makaranta bamu nufa ba gidansa kawai ya ajiyemu. Kowacce ta shigar da kayanta dakinta, muka ci gaba da zamanmu cikin jin dadi. Abunda yake bani mamaki shine yadda Micheal da abokansa suke kashe mana kudi kamar ruwa. A ina suke samun wannan uwar dukiya Oho? Nafi shakuwa da Micheal fiye da sauran, saboda kyautata min din da yake yi. Idan Harriet da Janet basa nan sai yazo ya kawo min kayayyaki kala-kala da damin kudi yace kyauta ya bani. Ban san me zan saya da kudin ba ko kuma wanda zan bawa ajiya. Hankalina ya tashi ince bazan karba ba. Ya ce dole in karba, ya fita ya barni da himilin kudi. Inyi sauri in sami lungu a dakina in boye. Dan ko zan hadiyi laya idan nace ina zamana ya dauko ya bani ba zasu yarda ba, naga shima a boye yake bani karsu sani. A hankali Micheal ya fara fito min da manufarsa, ashe shi sona yake yi yamin bayani ya ce babban makasudin da yasa ya bamu gida muka zauna saboda ni ya bayar kuma duk wannan hidimar da yake mana ya ciyar damu, ya shayar damu, ya saya mana saboda tsananin son da yake min ne. Amma baya so in fadawa su Harriet abunda ke tsakaninmu. Sai kawai naji na fara jin haushinsa saboda bani da ra'ayin soyayya, ban iya ta ba kuma, ban taba yi ba, kuma bana so nayi. Amma kunya dajin nauyin Micheal bai iya cewa bana sonsa ba sai dai kawai in dinga amsa masa sama-sama. Harriet da Janet basu cika yinin gida ba yanzu, da sassafe sai in ga sun shirya mota tazo ta daukesu basa dawowa sai dare. Ni kadaice a gidan sai wasu sababbin kawayenmu Fadila, Ngozi da Elizebeth suke zuwa mu yini muna hira da ciye-ciyen kayan dadi. Suma *yan matan abokan Micheal ne. Micheal koda yaushe yana zuwa ya taya ni hira haka kuma yake ajiyemin damin kudi duk sanda yazo. Na tambayeshi wai ina su Harriet suke tafiya yanzu basa zaman gida. Idan na tambayesu sai su ce in kyalesu tunda idan sun fadamun ba zuwa zanyi ba. Micheal ya ce min ai yanzu a wani sabon Guest house dinsa suke yini ko zanje ya kaini? Na ce "Ba zani ba.
Watarana ina zaune a gida ni kadai da yamma tunani nake yi yayin da kuka ya rufto min saboda kawai bana jin dadin wannan rayuwar dana tsinci kaina a ciki. Micheal ya zo ya same ni hankalinsa ya tashi ganin ina kuka yayi ta bani hakuri gashi da iya lafazi masu dadi nan danan naji damuwar ta fara gushewa a zuciyata. Ya ce zaman kadaici ne yake sani damuwa inzo ya zazzaga gari dani. Muka fita ya kaini wajen shakatawa kala-kala. Daga karshe muka shiga Zaranda Hotel. Ya ce zai dauki wata takarda a dakinsa in raka shi ciki, ganin tunda nake dashi bai taba nunamin wata alama ta iskanci ba sai na yadda muka shiga daki. Naga mutum yasa mukulli ya datse kofa. Na ce "Ya haka, ba takardar zaka dauka ba mu tafi? Sai ya hau dogon turanci wai yadda muka gaji ya kamata mu huta wajen dare sai mu koma gida. Na ce bazai yiwu ba ni tafiyata zanyi. Kamar yadda na ce Micheal saurayine son kowacce budurwa saboda dan gayu ne na karshen zamani ga uwa uba kyau fari ne dogo sosai, hanci, ido ga iya magana mai dadi. Yayi ta lallashina yana roka na wai inzo in zauna a gefen gadon muyi hira, naki zama. Har durkusawa yayi akan gwiwarsa yana hawaye yana rokata. Hankalina ya tashi na kasa gane wannan al'amari "In zauna muyi hira. Kamar yaya? Ina ganin mutuncin Micheal ga hidimar da yake yi mana musamman ni sai nazo na zauna a gefan gado na takure. Ya zo ya zauna shima a gefe guda muna kallon talabijin din dake dakin. Yana ta yimin hira tun bana amsa masa har na fara kula shi da ke hirar duniya ce kawai, yana ba ni labarin kasashe daban-daban da al'adunsu da ke ya zauna a kasashen wajen.
A hankali Micheal ya matso kusa da ni, hirar kasashe ta fara komawa ta soyayya. Ya fara yabon halayena ina da hankali, ga nutsuwa ga ladabi da tausayi sai kuma ya koma yake yabon kyawuna yana suffanta ni wai irin macen da kowanne da namiji yake so na yi dan murmushi na ce masa "Na gode. Sai ya ji dadi ya sake matsowa kusa dani ya ce "Priety irinku ba su da yawa a Africa, kai a duk nahiyoyi. Na yi dariya na ce . "Kai haba ni din me? Ya ce, "Kin fi ma haka, kalli hannunki kamar na jarirai masu laushi ga kyau. Sai ya riko hannuna. Na ji wani yar a ranar namiji ya taba rike min hannu. Na janye hannuna da sauri. Ya sake rikewa ya fara marairaice mun yana rokona wai ban san yadda yake ji ba saboda so na. Na ce "To me zan yi maka? Ya yi murmushi ya gyara zama ya jawo ni jikinsa yana fadamin dadadan maganganu, na lumshe ido don maganganunsa suna sosa min zuciyata. Kalma daya ya fada ta zaburar da ni da yace in yarda ya nuna min irin kaunar da yake min, idan mun kwana tare babu wanda yasan muna nan ba wanda zai ganmu, ba wanda zai gane wani abu ya faru a tsakaninmu. Na mike tsaye zumbur na dauki jakata cimak na nufi kofar fita, na ce tafiya zan yi. Babu abin da ya fado min a raina sai kalaman Hamma Huzaifa ya ce "Kada kiyi zina ko kun rufe kun kashe fitila Allah Yana kallon ku. Ya taso ya biyo ni ya sa hannu zai rungume ni, yana min dadin baki, sai naja gefe na ce "Kar ka taba ni, bude min kofa in tafi gida. Ya zaro mukulli a aljihunsa ya ce "Kin ga mukullin ba zan ba ki ba ki balla kofar ki fita. Ya juya ya tafi kan gado ya kwanta ya boye mukullin a karkashin filo. Raina ya baci sosai nan da nan na kasa controlling kaina. Abin da da ke jikina wato matsafan nan da suke kokarin jana cikinsu suka motsa. Idona ya yi jawur, karfi ya zo min, hankalina ya gushe, tafiya nake akan yatsan kafata guda daya. Na tunkari inda yake. Ya firgita ganina a wannan hali, hannu daya nasa na fisgo shi na wugar gefe ya fadi ya buga goshi da bango goshin ya fashe. Na dauki mukullin kofar dakin na bude na fita, ni kaina sai da safe na ganni a kwance a falon gidan da muke ba zan iya cewa ga yadda na yi na zo gida ba.
Su Harriet sun ga goshin Micheal a fashe sun tambaye shi bai fada musu dalili ba, amma ya fada wa abokansa wadanda tun tuni sun san irin son da yake yi mini. Su kuwa abokan suka zagaye suka gulmata wa kawayena, wai ni na fasa masa kai don ya ce yana so na. Ni ban taba sanin ashe ni yake so a rashina yake kulata. Ashe sabon gidansa yake turasu su yini don ya sami damar zuwa wajena ba tare da sun sani ba. Ina kwance a dakina daya amma sai na ji Harriet ta shigo a fusace na tashi firgigit na zauna kafin in bude baki in gaisheta na ji wani wawan mari tas a kumatuna. Na rike kuncina na yi shiru, radadi ya hanani magna, balle in tambayi dalilin marin. Sai na fuskanci dalilinta a zage-zagen da take yi. Micheal nata ne, ita yake so shi ne daman nake sadan-sadan kamar ba ruwana, ashe gulama ce son sa nake yi, ina lallabawa in je wajensa. Na yi na yi ta bari in yi mata bayani ta ki saurarona, dakyar Janet ta janye ta suka fita daga dakina. Na kwanta na rushe da kukan da na sa ni, na sake ji an banko kofar dakina da karfi, na daga kaina da sauri na duba sai naga Micheal wannan karon ransa a bace yake sosai. Na dubi goshinsa naga ansa masa plaster ashe ba karamin buguwa yayi ba goshin yayi loto tamkar dan jinjirin Jaki.

Hmmm Allah Yasa mu dace, Amin

Sai kuma gobe da yardar Allah.

Reedwan Suraj Isma'il

YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN
Chapter 23 · 0% Book details