← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 80

Sashe 54

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 10 min read

To fa! Cafdi!! Rigiji gabji!!! Budar bakin Mahaifinsa keda wuya sai ya ballowa Suhaif wani danyen aiki. Da ya fesa masa labarin da yake tafe da Zubaida. Baba ya ce "Da kuka Zubaida ta shigo mana wiwi a zaton mu ma wani ne ya mutu a Kano. Mahaifiyarka kuwa tuni ta zata kaine kayi hatsari tunda an ce mana gaka nan zuwa. A gigice muka tare ta muna tambayarta "Waye ya mutu? Ta ce "Ba mutuwa aka yi ba, bayan mun lallasheta, ta daina kukan muka takura mata da tambaya meya faru sai take shaida mana cewar Babanta ya ce zai musu aure. Naja'at tana da saurayin da take so itama Zubaidar tana da saurayi amma bata sonshi kai take so.
Suhaif ya yi shiru ya sunkuyar da kai kasa tamkar ruwa ya cinye shi, ya kasa magana. Goggo ta ce "Ban da abun Zubaida wannan ai ba abun daga hankali ba ne, tuwo na maina. Na san kai ma zaka fi son hakan *yar uwarka, jininka. Mun ce mata ta kwantar da hanakalinta insha-Allah ba zaka koma Lagos ba sai da daurin aurenku. Suhaif ya zabura ya mike tsaye kamar cinnaka ne ya cijeshi. "A'a kai! Lafiya kake zubure-zabure kamar kayi gamo? Baba ya tambayeshi "Allah Ya kyauta "Suhaif ya fada yayin da ya dauki jakarsa ya nufi dakinsa dake zauren kofar gida ya bar Mahaifansa suna kallon-kallo.
Suhaif kwance yake akan yaloluwar katifarsa yana tunanin mafita "Kai babu mafita Zubaida tayi min da baibaiyi da sakar karfe mai wuyar tsinkawa. Wanda hakori ko wuka ba zasu iya cizgewa ba, da dai na tsumma ne, inji zuciyar Suhaif. Ba na son in auri Zubaida, ina sonta a matsayin na kanwa, bana so ta tsinci kanta a matsayin matata saboda zata wulakanta, zata sha wuya ba zata samu soyayyata ba. Tamkar GANGAR JIKINA ZA TA AURA, zuciyata da ruhina yana wajen Iman har abada. Kamar na Ramla da Haisam, Suhaif ya fada a baiyane.

Nima dai na ce GANGAR JIKINSA zata aura zuciyarsa da ruhinsa yana ga Iman.

Ehem anya ba zamu sasanta da Suhaif ya ce a aura min Zubaida a MADADInsa ba?

Reedwan Suraj Isma'il
08097365237 @watsapp

:::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI

Da daddare a tsakar gida Suhaif da Iyayensa suna cin tuwo suna hira. Baba ya sake tuntubar Suhaif da zancen Zubaida sai Suhaif yaji ya kasa kai lomar dake hannunsa bakinsa, yayi shiru bai ce komai ba. Goggo ma tasa baki suna ta yi masa nasiha, suna nuna masa alhairin hakan. Yana jin nauyi, yana jin tsoron bacin ran da zai afku a zuciyar Iyayensa idan suka ji amsar da zai fada. Amsar ita ce "A'a bana so. Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce "Ka fadi alhairi ko kayi shiru. Dan haka Suhaif ya yi shiru bai ce musu komai ba.
Yaran unguwa ake ta aikowa daga kofar gida "Wai Suhaif ya zo inji abokansa. Ya san mutanen da ya yiwa alkawari ne, suka taru a kofar gida. Ya ce da *yan aike su ce musu yana zuwa. Hajja da jikarta suka shigo da kuka, hankalin Mahaifan Suhaif ya tashi Goggo ta tare su da gudu tana tambaya "Waye ya mutu? Suhaif bai damu da yasan dalilin kukan ba, ba zai wuce godiya suka zo yi ba. Ya je ya wanke hannunsa a wajen rijiya. Hajja ta ce "Ba mutuwa aka yi ba godiya muka zo muyi, dadi ne yayi mana yawa har muka yini muna kuka. Suhaif ya tuntsire da dariya ya ce "Shegiya *yar Hajja kema har dake kukan? Bari in haskaki da fitila, na san kukan karya kike yi. Hajja ta ce "Ni na ce tayi kuka ko ba hawaye saboda wannan abun arzikin yafi karfin mu shigo ba kuka. Suhaif ya kwashe da dariya yayi ta dariya har cikinsa yayi ciwo, ya fice kofar gida wajen abokansa, bayan ya shiga dakinsa ya ciko aljihunsa da kudin da zai raba musu. Hajja ta mike kafa ta zaiyana musu abun arzikin da Suhaif yayi musu alkawari. Iyayensa su ka ce su basu ma sani ba, bai fada musu ba. Sun ji dadi sosai har fiye da Hajja da jikarta, yau ga dansu ya zama mutum yana abun alkhairi da dukiyarsa. Suka hadu suna ta shi masa albarka.
Suhaif bai dawo gida ba sai da misalin sha daya na dare. Shi da abokansa sun nutsa cikin gari gaishe-gaishen *yan uwa da abokan arziki da aka dade ba'a haduba. Har Garki suka je wajen Babbar yayar Mahaifinsa Iya Furera. Itama ta yi masa kukan danta zai yi aure kuma bashi da kudin hada lefe. Suhaif ya yi alkawari zai hado masa lefen. Ya dauko kudi mai tsoka ya bata, tayi murna sosai. Lokacin da Suhaif ya dawo gida Iyayensa har sun kwanta, su Hajja sun tafi gida tuni, ya rufe kofar gida ya shiga dakinsa ya kwanta. Bacci ya gagari idanuwansa yana ta kwatanto Zubaida a matsayin matarsa, ya ga ko zai hakura, ya danne zuciyarsa ya aureta, sai ya ga ina! Bazai iya ba, Iman ce har yau a cikin lissafinsa. Gashi babu Iman amma ya kasa hakura ya auri wata, ba Zubaida kawai ba *yan mata da yawa suna sonsa amma ya kasa sonsu.
Manyan dalilan shine duk wadanda yake haduwa dasu basu da nutsuwa da halaye irin na Iman, ko kusa bai taba samun mace mai hankali da biyayya irin na Iman ba. Ya sha daurewa zuciyarsa ya fara zuwa zance gidajen *yan matan da suke rokarsa ya je amma idan yaje sau daya, sau biyu baya komawa na ukun. Saboda *yan boko ne, yanzu wayewa ce ba'ajin kunyar saurayi sai su saki jiki da saurayi kamar mijinsu. Daga zuwa zance wata budurwa ta tubure masa wai sai ta bashi abinci a baki. Tun daga ranar ya rabu da ita. Wata kuwa daya gwada zuwa gidansu, da gyale a jikinta da ta ganshi sai ta cire tasa matsattsan kaya. Wannan rashin kamun kan ne yasa ya barta, don ba haka Iman dinsa take ba. Daga karshe ya hadu da mai saka hijabi har kasa kamar Iman, har ya fara murna ya samu mai hali irin na Iman. Ashe hijabin ne iri daya ba zuciyarsu daya ba. Sun yi watanni tare har yana saka ran zai yi maganar aure da manya a rashin Iman. Wata rana yayi mata zuwan bazata gidan da ake rikonta, gidan yayarta. Ya isketa da kananan kaya (english wares) matsattsu. Tana zance da wani dan caburos har yana kai hannu yana taba ta. Tana ganin Suhaif kafin ta iya motsi ya shiga mota yayi tafiyarsa. Tasha kuka tasan ta rasa Suhaif, daman hijabin yaudara ne, ta lura yana zon mace mai hijab shine take yaudararsa da hijab. A zamanin nan ina zan samu mace kamila mai tsoron Allah irin Iman? Suhaif ya fada yayin da hawaye yayi masa kawanya yana kwance.
Washe gari misalin karfe goma na safe, bayan Suhaif yayi wanka ya fito tsakar gida ya gaishe da Iyayansa. Bayan Goggo ta bashi koko yana sha sai ta dube shi sosai taga idanuwansa a kunbure suke. Ta tambaye shi, "Babangida kuka kayi, ko kuwa rashin bacci ne idanuwanka suka kunbura? Suhaif yayi murmushi bai ce komai ba. Goggo ta dauko masa zancen abun arziki da ya yiwa Hajja Mahaifiyarta. Tayi ta shi masa albarka, ta ce ya ci gaba da taimako irin wannan. Amma ya kamata ya dinga samunta ko Mahaifinsa yana fada musu abun alherin da ya yiwa wani ko neman shawararsu akan abunda yake so ya bawa wani domin ya kamata su sani kar a zo yi musu godiya su hau zare idanu basu san akan me ake yi musu godiya ba. Suhaif ya amsa mata da "To daman gani nayi saboda Allah na yi, shiyasa ban fadawa kowaba' Mahaifinsa ya ce "Haka ne, amma mu dai ya kamata ka fada mana.
Suhaif ya shaida musu yana so ya biya musu Makka amma yaga Baba na Kano ya biya musu waccan shekarar sai yayi tunanin ya rushe gidan nan ya sake gina musu na siminti, na zamani. Amma yaya suka gani? Suka ce haka yayi tunda sunje Hajji wancan shekarar ya musu gyaran. Baba ya ce "Kafin ka fara yi mana gini na fi son ka bani kudin da zanyi noma sosai wannan shekarar in dauki ma'aikata, in sayi takin zamani da magungunan kwari. Goggo ma ta ce jari take so ya bata tana so ta dinga saro atamfofi daga Kano tana rabawa ma'aikata. Suhaif ya ce "Duk mai sauki ne zan baku kafin in tafi.
Baba ya gyara zama ya sake dauko zancensa da Zubaida, ya ce "Muna magana tun jiya ka ki cewa komai ka barmu muna bolokoko mu kadai. Ni yanzu da ka ganni Kano zan je ko in aikeka Kanon ka kiramin Usman Mahaifin Zubaida, mu zo a hadu da Mahaifiyarka da Yaya Furera ta Garki a yi magana. Suhaif ya yi caraf ya ce "Baba ya kamata ku gane abun da nake nufi, tunda amsar da zan baku ta yi min nauyi a bakina, na kasa ce muku a'a bana so. Dan Allah Baba ku yi hakuri ku bar zancena da Zubaida. "Sai wa kake so ka aura tunda baka son *yar uwarka? Baba ya tambayi Suhaif a shelake. Suhaif ya ce "Babu wacce nake so takamaimai, amma ina gudun a bani *yar uwata in zo in wulakantata. Goggo ta ce "Kai Babangida kaji tsoron Allah, har ka iya kallon idanuwanmu ka ce baka son Zubaida. To kar ka sake ka dubi Mahaifanta kace baka son *yarsu, duk halaccin da suka yi maka, tun kana yaro har ka girma ka zama mutum sak. Suhaif ya ajiye kofin koko ya ce "Oh my God, Dad, Mum kun kasa gane abunda nake nufi. Akwai wacce na yiwa alkawarin aure bana so in zama mayaudari. Baba ya fusata ya ce "Kai dalla rufe mana baki Dad kake cemin da kuma Mum kake cewa Goggo? Wai kai dan boko ko? To badan Mahaifin Zubaidar ba ina zaka san sunan uwa da uba da turanci? Da ba kana kauye kana noma ba? Goggo ta ce "Wacece wacce kake so din, kasan yanzu duk wacce zata ce tana sonka badan Allah za ta so kaba saboda abun hannunka zata so ka. Ba gara ka auri *yar uwarka ba. Suhaif ya ce "Wallahi waccan ma don Allah take sona tun bani da komai. Goggo ta ce "Iman din dai har yanzu? Baba ya yi jan ido ya ce "To bari kaji maganar karshe ita ce ka auri Zubaida ka gama, ko bayan raina a daura musu aure. Kar ka kara kawo mana zancen banza, a garin neman Iman ka rasa aikinka. Idan ka sake kiran sunan Iman a gidan nan saina bata maka rai. Yanzu ka shirya ka kaini Kanon in je in yi magana da Usman.
Ran Suhaif ya yi mummunan baci, ya rasa abunda yake masa dadi, sai wata kwalla mai zafi ta cika masa ido ya gwammace bai zo ba ma kwata-kwata. Tun da suka shiga motar suna tafiya babu wanda ya sake magana shi da Mahaifinsa, har suka isa Kano. Suhaif ya wuce dakinsu ya kwanta babu abun da zuciyarsa take sai bugun uku-uku. Babu wacce yake tunowa a ransa sai Iman, baya fitar da ran zai ga Iman kuma ya aureta. Kamar daga sama ya sake jiyo muryar Mahaifinsa da Baban Zubaida. Bayan Baba na Doko ya gama fadawa Baba na Kano duk abunda yake faruwa tsakanin Zubaida da Suhaif da kuma hukuncin daya yanke. Yanzu kafin Suhaif ya tafi, dole ya bayar da sadaki koma ba'a daura auren ba, tuwona maina. Baba na Kano yana bude baki cewa yayi "Har yanzu banji kalma daya da Suhaif din ya ce ba. Naji na Zubaida, naji naka. Me shi Suhaif ya ce? Baba na Doko ya zabura ya rufeshi da fadan da ya saba ya ce "Kai! Kai dakata bana son kwakwa ni dai na gama magana, aure zan daura shi ko baya so yarinya dai tana so, ni da Mahaifiyarsa muna so.
Chapter 54 · 0% Book details