Sashe 67
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun bayan dana koma bansake dawowa ba sai wannan dawowar da muka yi gaba daya, duk da tun waccan shekarar na kammala karatuna. Sai Hamma Huzaifa yasa na sake yin wani karatun na shekara guda wato Masters, shima na gama. Hamma Huzaifa ya tunkareni da maganar aure, sai naji ba zan iya aurensa ba, saboda ya zama tamkar dan uwana na jini, wato Babban wa magajin Uba haka Hamma Huzaifa ya zama a wajena. Ga Uwa Uba matarsa Zainab ta zama kawata in dai sun zo Makka tana wajena tare muke kwana mu tashi, nima kuma zuwana Bahrain biyu wajen su. Sai na nuna masa ba zan iya ba.
Suhaif ya dago ya kalli Iman, kallo mai hade da harara. Don tunda ta fara bada labarin sai yanzu ya dago ya kalleta, tun dazu kansa a sunkuye yana murda agogon hannunsa. Yana sauraron labarin Iman yana jin muryarta a kunnansa tamkar ana busa sarewa don dadi. Iman ta kalleshi sai ta sakar masa wani tsantsareran murmushi da yake tayar masa da dankararriyar soyayyar data daskare a zuciyarsa. Ya ji kamar a yanzu ya fara sonta, son da yake mata a da duk ba so ba ne akan yadda yake ji yanzu. Nan da nan ya ji zuciyarsa ta hau bugawa, sai ya mike da sauri ya nufi kofar fita. Najib ya yi sauri ya ce "Suhaif ina zaka je ne? Dare yayi fa yanzu zamu tafi mu kwanta a masaukinmu. Suhaif ya ce "Idan kun gama ku sameni a waje.
Tun daga lokacin Iman ta ji ta rikice ta kasa ci gaba da labarin tama manta in da ta tsaya, hankalinta ya koma wajen Suhaif. Zubaida ce ta fito daga ban daki ta ce "Babban aiki ya same ni gashi dare yayi. Duk suka juya suka dubeta "Kamar yaya babban aiki ya sameki? Mama ta tambaya. Zubaida ta zo kunnen Iman ta rada mata cewar audugar mata take so. Sai Iman tayi dariya ta ce "Shine aikin daya sameki? Kar ki damu bari inje gida in dauko miki yanzu-yanzu. Huzaifa ya kalli Iman cike da shaukin so, kauna da bege, yayi murmushi ya ce "Ko kina jin tsoro in zo in raka ki, naga wajen da duhu. Iman ta dan harareshi ta ce "Haba dai tsoro, aini baka sanni da tsoro ba mantawa kayi, sai dai Zainab matarka ita ce mai tsoro. Najib ya ce "Je ka rakata. Huzaifa yayi dariya ya ce "Tsokanarta nake yi ai bata da tsoro ko kadan, wannan sai dai ta dinga rakanu ma ni da Zainab din gaba daya. Duk kansu suka yi dariya. Goggo ta dora musu labarin rashin tsoro irin na Iman a zamanta na Doko. Iman tana dariya ta fita.
Tana fita ta mance da sakon Zubaida sai ta shiga wurwurga ido ko zata ga Suhaif, amma bata ganshi ba, har motocinsu ta lelleka baya ciki. Ta zagaya bayan gidan kamar da wasa, bata yi tunanin zai shiga cikin ciyayi da duhun nan ba sai kuwa ga Suhaif ya rike kai a tsugune. Ta tunkaro shi da sauri tana kiran sunansa gami da tambayarsa "Lafiya? Me ya faru? Me ke damunka? Ya zabura ya daga hannu biyu ya dakatar da ita kada ta karso in da yake. Ya kara da cewa ta yiwa Ubangijinta ta tafi ta kyaleshi babu abin da aka yi masa shi.
Iman ta rushe da wani kuka mai turiri tun daga kahon zuciyarta zuwa idanuwanta, ma'ana kana jin kukan kasan yana dauke da bakin ciki mai tsanani ba irin wanda ake kirkirowa bane wato kukan dadi ko na kissa. Tsananin damuwar da Suhaif yake ciki, zazzafan kukan da ya labe yana sharba sai ya lafa, hankalinsa gaba daya ya tashi ya dira akan halin da yaga Iman ta shiga yanzu-yanzu. Iman me ya saki kuka? Me aka yi miki? Suhaif ya fada a lokacin daya je ya tsaya a gabanta. Ta kasa magana kuka take tayi abinta. Ya gigice gaba daya, ya hau lalube-laluben aljihu ya lalubo mata wani farin hankicin ya mika mata yana mai tsananin bata hakuri, har sai da kukan ya lafa. Ta dago ta dubeshi cikin sanyayyiyar murya ta ce "Na yi zaman mutunci da amana ni da *yan uwanka, iyayenka, da jama'ar garinku. Mun yi zama ni da kai zaman amana, ka taimake ni, ka tsaya tsayin daka har sai da na yi rayuwar jin dadi da kwanciyar. Mun rabu kana kuka ina kuka, na tafi na barka da sona da tunanina, na tafi da tunaninka da sonka. Ko da yaushe kana addu'ar ka ganni, nima ina addu'ar in ganka. Kamar yadda Najib ya fada min kazo garin nan nemana, nima na taba zuwa Doko nemanka da daddare na aika Yaro gidanku aka ce ka kaura Lagos, takanas don kai naje Doko tun daga filin jirgin Kano lokacin da zan tafi Makka karatu. Tunaninka ne yayi min yawa dole na je ganinka koda jirgi zai tafi ya barni. Ina gani na a Kano naji bazan iya barin kasar nan ba tare da naje na ganka munyi sallama ba kafin in wuce. Duk sanda naga mai sunanka, ko mai kamarka sai naji gabana ya fadi in zata kai ne. Mun hadu ni ina murna kai kana bacin rai, duk da dai mun hadu a cikin wani yanayi na babu zancen soyayya tsakaninmu. Suhaif ina sonka ne kawai a raina amma nasan bazan aureka ba saboda har tsinuwa Mahaifanka suka ambata idan baka rabu dani ba. Amma ina son muyi rabuwar arziki yadda idan mun hayayyafa *ya*yanmu zasu yi zumunci ko kuma ma suyi aure tunda mu bamu yi ba. Suhaif bani da niyyar in yaudareka, ba yaudararka nayi ba. Kaji dalilin da yasa zan auri Hamma Huzaifa ba kai ba. Mun rabu a zatona ma kayi aure ka manta dani. Sai kuka ya kece mata.
Sai nima kuka ya kece min domin na tuna tsumammen tsumin so da kauna wanda na sha nai tatul daga karshe........... Gwalo... Bazan karasa ba ehe.
Reedwan Suraj Isma'il
¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤? YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Suhaif ya matse idanuwansa ya ce "Daina kuka, kar kiyi kuka. Kukan nan naki zai iya dasuwa a raina ya zamarmin damuwa. Iman nasan baki yaudareni ba, nasan ba mu isa mu gocewa kaddarar Ubangiji ba. Damuwata ita ce yadda rayuwata zata kasance nan gaba. Sai ya yi shiru ya kasa magana. Iman ta ce "Kamar yaya? Suhaif yayi shiru ya girgiza kai ya ce "Kimin addu'a duk lokacin da aka ce miki na mutu kada ki sake ki bari Huzaifa yasan ina sonki. Ya juya ya tafi, ya dafe kirjinsa da alama zuciyarsa ce ta matsa masa da ciwo. Da kyar yake iya jefa kafarsa ya nufi cikin mota ya zauna ya kifa kansa akan sitiyari.
Iman ta kalli gabas yamma, kudu da arewa ta rasa mai taimakonta, ta ji kamar ta zauna tayi ta kwala ihu sai ta kamo kalmar Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Ta taho ta nufi hanyar gidansu kamar wacce kwai ya fashe mata a ciki, dakyar take tafiya. Ta zo dai-dai motar da Suhaif ya shiga ya kulle kansa ta kwankwasa masa glas, ya dago ya dubeta, ta ce ya sauke gilas. Ya girgiza kai alamar a'a, yayi mata nuni da hannu alamar ta tafi. Hawaye mai radadi yake zubowa daga idanuwansu. Sai ta daga masa hannu ta ce "Good bye Suhaif I miss you. Shima ya daga mata hannu ya ce "Bye-bye Iman I miss you too. Ta tafi tana waiwayansa tana daga masa hannu, shima yana daga mata hannu su duka kuka suke har ta kure ya daina ganinta, ta daina ganinsa.
Iman tasha mamaki da taga Hamma Huzaifa a zaune a cikin get din gidansu akan wani benci kusa da dakin mai gadi, shi da ta bari a gida tare da su Najib. Yaushe ya fito? Ta ina ya biyo basu ganshi ba? Mai ya zo nema? Sai tayi sauri ta goge hawaye ta hau murmushin karfin hali. Taje wajensa tana tambayarsa ita ya zo nema? Yayi dariya ya ce "Na zo in ganki kafin inje in kwanta, yau kwana zan yi a zaune, ba zan iya barci ba saboda farin cikin daurin aurenmu gobe. Zan auri macen da na taba so a rayuwata, wacce nake so a rayuwata, wacce na fi so a rayuwata, wacce zan ci gaba da so har karshen rayuwata. Sai Iman ta fashe da kuka ta zauna a gefensa a sanyaye. Huzaifa ya rikice ya tambayeta kukan me take? Sai ta ce masa kukan me zata yi wanda ya wuce kukan dadi. Ita kuwa ji tayi hankalinta yayi mummunan tashi, ta taho da tausayin Suhaif ga kuma Huzaifa. Duk sun yi mata halacci a rayuwa, kuma ta saba dasu su duka.
Najib da Muslim sun zo sun iske Suhaif zaune a cikin mota. Sun nemi Huzaifa basu ganshi ba, sai suka shiga mota suka tafi, daman sallama zasu yi masa. Sun shiga katafaren Hotel din da aka sauke su, dakinsu yana kusa da dakin Babansu. Sauran dakunan ma duk bakin su Huzaifa ne daga garuruwa daban-daban, wasu kuwa abokansa ne daga Saudiya da Bahrain har da abokin nan nasa El-Sadik shima ya zo. Najib ya taba kofar dakin Babansu yaji a kulle daga ciki, munsharinsu na tashi, shi ya tabbatar masa sun dade da yin bacci.
Su Najib sun shiga sun kwanta yayin da gajiya ta dannesu kan kace kwabo Najib da Muslim sun yi bacci amma ban da Suhaif. Idonsa biyu ya kurawa fitila ido yana tunani. Tambayar anan shine shi bai gaji bane kamar yadda sauran suka gaji? Amsar ita ce Suhaif ya gaji shima yadda sauran suka gaji, amma wani yakin yafi wani, damuwar da yake ciki tafi gajiyar damunsa. Idan ya gaji da kwanciya sai ya tashi ya zauna. Ya sauko kasa ya kwanta kan kafet. Ya gaji ya hau gado duk juyi yana ambaton La'ilaha illa anta subhanaka inni kuntum minal zalimin, da dukkan addu'ar data shigo bakinsa.
<3 ______RANAR DAURIN AURE______ <3