← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 80

Sashe 48

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 3 min read

Iman ta tafi tabar Suhaif da tunaninta, begenta da tsantsar kaunarta. Baya walwala, baya son shiga mutane balle yayi hira dasu daga Masallaci sai dakinsa. Abincinsa kuwa idan yayi cokali daya, biyu, baya iya yin na uku sai yaji ya kasa ci. Babu abinda yake yi sai tunaninta wani lokaci ya debo wasikunta da hotunanta yana kallo. Sai ka ga hawaye ya surnano masa saboda tsananin damuwa. Abunda yafi tsaya masa a rai, shine irin wahalhalun da tasha a rayuwaarta shima yasa yaji ya kara sonta yana kuma tausaya mata yadda rayuwarta zata ci gaba da kasancewa bayan rabuwarsu. Yana ganin abu daya zai sa hankalin Iman ya kwanta a rayuwarta shine idan Allan Ya bata miji na gari mai tsoron Allah, mai sonta tsakani da Allah. Wannan mijin kuwa ba kowa bane illa Suhaif. Ina son Iman tamkar yadda nake son rayuwata, yadda bazan iya wulakanta rayuwata ba haka bazan wulakanta rayuwar Iman ba. Allah ka bani Iman. Ina zan sake ganinki Iman? Na rasa Iman na rasa mace ta gari, mai kirki, mai addini, mai kunya da tsananin tsoron Allah. Suhaif yana fada yana kuka.
Najib bai daina yiwa Suhaif nasiha ba har lokacin da ya shirya ya koma Kano. Mahaifan Suhaif basa jin dadin yanayin damuwar da Suhaif yake ciki. Suna ta bashi baki da nasiha kala-kala. Daga karshe Mahaifin Suhaif ya bashi shawara ya shirya ya koma Kano ko hankalinsa zai fi kwanciya, har Allah Yasa aikin da ake nemar musu ya fito. Suhaif bashi da zabi yasan Kano da Doko duk daya ne tunda ba Iman zai gani ba. Bai ki yarda da shawarar Mahaifinsa ba, ya shirya kayansa kakaf ya tafi Kano. Can ma bata sauya zani ba cikin damuwa yake, amma yana samun dan sanyi a ransa tunda koda yaushe Najib yana tare da shi dakinsu daya, su kwana su tashi tare. Ko zasu yi fada Najib bazai fasa fada masa gaskiya ba, yana cewa wannan damuwar daya saka a ransa babu abinda zata kara masa illa ciwo. Iman dai ta tafi zai yi wuya ta dawo dan haka gara ya barwa Allah komai, idan Allah Yaso zai sake hadasu kamar yadda itama Iman din ta fada sai su hadu. Tamkar dalmar wuta kalaman Najib suke yiwa Suhaif a zuciya, su Suhaif da Najib suyi ta fada wai dan me zai ce ya daina damuwa Iman ta tafi kenan. Daga baya Suhaif ya fara yadda da zancen Najib gaskiya ne babu alamar dawowar Iman, gashi wata da watanni. Sai ya fara bawa zuciyarsa hakuri yana daddaurewa yana fita wasu harkokin.
Baba Usman Mahaifin Najib ya shigo da wasu motoci guda biyu iri daya kalace kawai suka banbanta, daya kalar ja, daya kuma shudiya ce, motocin sababbi dal-dal a ledarsu, irin na zamani da kowanne matashi mai ji da kudi ko Mahaifinsa mai ji da Naira yake mafarkin samunta. Aka yiwa Najib da Suhaif albishir cewa ta su ce. Wai!! Wayyo Allah Najib yaji dadi har da ihu. Suhaif ma ya ji dadi sosai, suka je wajen Baba suka yi godiya suna baiyyana farin cikinsu. Baba yafi su jin dadi ganin yayi musu gwaninta kuma wadanda yayi dominsu sun gode.

Wai meya sanya wasu suke cewa ba'a tashi inda aka tsaya ne? Wa ya fada musu ana tsallake?

Gimbiya Zarah Matawata kenan ta ce ta ji dadi da ba'a mance da ita ba a wannan dandali..... lolxxx

:::::::::::::::::::::::::::::: YARENA ADDININA
___CIGABAN LABARI
Chapter 48 · 0% Book details