Sashe 31
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zan karasa anjima insha Allah.
Surayya
Abubakar
Masu motar basu saniba ya shigo bauchi duk acikin daren nan. Yazo gidan da nake wujiga wujiga yace inyi ta kaina. Ya dibi kudin gibrel yace yanzu zai gudu garin su lagos nima na debo mana kudin mota, taho mu gudu.
Jikina na rawa na dauko zani na daura na yafa wani zanin gadon janet. Fadila ma tasaka wata doguwar rigata. Ta fisgo hanuna muka fito daga dakin. Dan jaririn harriet sa kwalla kuka yake nace mata "ban dauko dan jaririn ba. Ta daka mun tsawa "kidauko shi ki kashi ina? Zomu tafi muyi ta kanmu. Kinsan fa ansan tare muke dasu micheal zasu zo nan nemanmu fa. Harna juya na bita, naji yaron nan sai kuka yake. Nadawo da gudu cikin dakin, fadila ta biyoni tace "me kika dawoyi? Nace dan jaririn zan dauka. Ya zanyi in yanke cibiyar in rabashi da uwar? Tace "dauko reza. Sabuwar reza nabata acikin kayan kwalliyar mu. Fadila ta yanke cibiya, sake bani shawara take tana cewa in ajiye dan jaririn nan idan nadauke shi ina zan kaishi. Nima nayi tunanin haka amma tausayi ya hanani in tafi in barshi. Nadauko zanin mahaifiyarsa na lullubeshi na rungume shi a kafadata. Najawo mayafi na lullube fuskar harriet na tofa mata addu'a Allah yajikanta. Muka sakd juyawa zamu fita wani dan karamin hoton harriet ne a jingine a wajen kayanta tana dariya a hoton tayi kyau sosai. Nakoma nadauko shi. Fadila ta kwalla da karfi tace "pretty idan bazaki tafiba zan tafi ga karar jiniyar motocin 'yan sanda can watakila nan zasu zo neman mu mu yan matan yan fashi. Muka fito daga dakin muna ta gudu muna shiga gonakin mutane. Batare damun san inda muke nufaba. Akwai wani katon dutse a bangaren da za'aje wata makaranta jibrin aminu primary school a jikin dutsen muka labe. Idan muka hango motocin yan sanda saina toshewa dan jaririn baki yanata tsala kuka. Anan a gindin dutshen muka zauna muna rusa kuka tamka ranmu zai fita. Fadila tace mu "pretty kin fadamun gaskiya, rayuwar bariki ba rayuwar kirki bace. Mubi maganar iyayen mu domin muddin kaki bin iyaye bazakaga ci gaban rayuwarka ba, dubemu kiga irin rayuwar da muka jefa kanmu. Ta debo kudi mai yawa daga kudadenta tabani, tace inyi kudin mota intafi gida itama zata shiga mota ta koma gida. Dan jariri ya gaji da kuka sai yayi barci. Bamu fito daga bayan dutse nan ba saida gari yafa washewa muka farajin karar wucewar motoci da babura suna giftawa.
Allah ne yakiyaye mu ashe duk ramukan macizai ne a inda muka fake ga kunamai sunata gif-giftawa. Mukayi sauri muka bar wajen muka fito titi muka tari achaba gudu biyu muka ce tashar yankari. 'yan achaba ma hirar 'yan fashi da aka kashe jiya suke bamu, sai cikinmu yakara durar ruwa suna cewa "abun mamaki harda mata acikin yan fashin da aka harbe jiya. "naji kuka mai radadi ya zubo min bamu iyace musu komai ba. Suka kaimu tasha muka sauka muka basu kudinsu. Dan jaririn dai kuka yake tsalawa babu riga ko wando ajikinsa ko jinin haihuwar ma ba'a wanke masa ba ga uwa uba sanyi da yake surarsa da yunwa. Fadila shawarar da take bani itace inyar da yaron nan intafi gida. Natuna amanar da uwarsa ta bani, kuma tausayinsa nakeji idan nayar dashi bansan hannun wandazai fadaba watakila yatashi ba'a musulmi ba. Naji ajikina zai zama musulmi ya amfani musulunci duk da dai bansan inda zan tinkara da dayan jariri ba a yarda arikemu. Na shaidawa fadila bazan iya yarda shiba, zan tafi dashi. Na roketa nace ta rakani kantin dake cikin tashar in saya masa madara in bashi yasha kafin afara sayar da ticket din shiga motocin yankari expressg. Akantin na tambaya ko akwai madarar jarirai akace akwai. Nasaya sai muka je wajen wata mai koko da kosai na roketa Allah annabi ta bani ruwan dimi in damawa dan jinjirina madara. Tabani kadan a kofi da cokali nida fadila muka dinga tarfa masa yana hadiyewa harya koshi, muka yiwa matar godiya muka tafi wajen da ake yankar tiket din shiga motar. Nayanki tikitin jalingo, fadila ta yanki na katsina. Muka rungume juna muna kuka mukayi sallama kowacce tashiga motar garinsu muna dagawa juna hannu muka tafi. Na shiga garin mu, atasha nadauki shatar taxi wacce xata kaini har kofar gida. Na shiga unguwarmu na tarar unguwar shiru ba kowa. Nashi mummunar fargaba da mummunar damuwa yadd zanyi da dan jaririn nan. Ina cikin taxi ina waige-waige ina fargaba jinake kamar incewa dan taxi ya juya dani nafasa zuwa gidan. Akofar gidan su hamma huzaifa na kalla sai kuwa mukayi ido hudu dashi. Ya bude baki yana mamakin ganina. Saiya washe baki yayi min wannan dariyar tasa tanuna farin cikin ganina. Yasa hannu ya tsayar dame taxi gami da cewa "wait-wait." ya tunkaro motar ta tsaya da farin cikin sa. Mummunan faduwar gaba tadasu a zuciyata. Nazaro kudi nabawa dan taxi kafin bude kofar motar in fito hamma huzaifa da kannensa sun karaso wajen motar yasa hannu yana bude mun kofar cikin harshen fulatanci yake tsokanata. Yace inye pretty 'yan makaranta, yanzu angama level 1 an zama yan level 2 ko, point nawa kika buga mana? Nasan dai kin bugo samada 3 points ko mutuniya? Yana fada yana bude mun kofar mota....
Amin afuwa plz
YARENA ADDININA....CGBN LBRN
Nasa kafata daya awaje ina kokarn fitowa dakyar don jikina yayi sanyi. Huzaifa ya sake kallona cike da mamakin ganin yadda na zama kamar baniba. Bayan rashin fara'a gashi na yafa wani burgujejen zanin gado na lulluba, baki abushe, ido a kode sanadiyar kuka. Gashin kaina biyu-biyu a cukurkude. Alamar tambaya zaka iya gani a idanuwansa. Zai bude baki yayi min tambaya meke damuna yaga nazama haka? sai kukan jaririn dake hanuna ya mayar da hankalinsa ya kalli abunda na rungume, fuskar sabon jariri ya hango. Nanda nan ya canja zaka iya ganin fargaba da tashin hanakalin da suka rufto masa, yaja da baya da sauri jikinsa yayi sanyi sai kalmar innalillahi wa'ina ilaihi raji'un yake karantowa, kaji musulmin kwarai. Muka hau kalon-kallo, ya kalleni ya kalli jaririn hanuna. Abunda ya sake fadomin arai shine nasihar da yakemun tun ina yarinya. Yace "kada kiyi zina, Allah ya hana zina, yana kallon ki zai konaki, kiji tsoron Allah. Shima kuma daga dukka alamu abunda yake tunowa a zuciyarsa kenan. Wato na manta nasihar da yayi min? Ina tsoron Allah da yake ganin alamar yashigeni? Sai naga hawaye daga idonsa guda daya ya surnano. Ya girgiza kai ya juya ya tafi ya nufi gidansu yabarni anan a tsaye. Bakina yahau kaikarwa inaso inyi magana na kasayi domin nasan babu bayanin da zan iya yi masa awannan lokacin ya yarda dani me taxi yaja motarsa ya tafi. Kannena na hango sun taho da gudu zasu tareni sainaga sunyi kicibus sun tsaya ganin dan jinjiri a rungume a hannuna sukayi gefe suna kallona, nazama abar kallo. Mahaifina da mahaifiyata nahango awajen mota da alama motar zasu bude su shiga su fita, sai suka tsaya suna hange suna so su gaskata abunda suke hange gaskiyane ko kuwa gizau idanunsu suke musu. Jariri ne a rungume a hanuna ba gezau bane gaske ne. Na tunkaro inda suke a tsaye. Mukullin motane a hannun mahaifina saiya fado kasa don razana. Haka jakar dake rataye a kafadar mahaifiyata sai data sulmiyo fadi kasa. Mahaifiyata ta sulale ta zauna akasa tsabar tashin hankali. Muka hau kallon-kallo dasu yayinda nima idanuwana suka haskomin mummunan tashin hankali a tattare dasu wanda yafi tashin hankalin da suke hangowa a tattare dani. Naji tsananin bakin cikin da nake ciki tamkar shafar mai ne akan bakin cikin daya tunkaroni a yanzu yanzun nan. Shin gizau idanuwana sukayi min ko kuma gaskiya ne. Hakika gaskiya ne ba gizau bane. Turkashi, nanda nan na nami yawun bakina da makokarona na rasa sun bushe kamas don tashin hankali sai zuciyata ta lalibo addu'ar da Huzaifa yake karantawa a lokacin dabala'i ya tunkaro shi. Naji kafata bazata iya daukar jikina ba da dan jaririn dake hannuna sai nima na sulale na zauna kamar yadda tashin hankalin ganina yasa mahaifiyata ta sulale ta zauna. Karkarwa suke suna nuna jaririn dake hanuna, nima hannuna na karkarwa idanuwana na zuba tamkar ruwa a famfo ina nuna gagarumin tashin hankalin da nake hange a tare dasu.....
Toh littafi na dayan yakare da iznin Allah
YARENA ADDININA.
___CI GABAN LABARI