Sashe 33
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read
ruwa ya cinyeni na rasa abun cewa, na tsani Micheal bana kaunar ganinsa, amma kuma ina son dansa bana son rabuwa dashi kuma na saba da shi sosai a cikin sati biyun nan. Kamar daga sama naji Micheal ya ce "Pretty me zai hana muyi aure mu rike yaron nan. Kina da labari har yanzu son da nake yi miki yana nan? Na fusata bansan sanda na fisge zanin goyon da nayi ba, na kunto yaron daga bayana na dungura masa dan gami da cewa "Idan danka ne gashi nan, ko bayan raina bana son ka matso kusa da gawata balle ni da kaina in aureka. Na fashe da kuka na juya naci gaba da tafiya. Kukan da yaron yake tsalawa ne naji tamkar mashi ake caka mun a zuciyata. Babu abinda ya fadomin a rai sai idan na barshi ya tafi da yaron nan ko shakka babu sunansa ba Musulmi ba, idan ma ba a ci sa'a ba ya tashi cikinsu *yan fashi ya koyi fashi da iskanci da shaye-shaye irin na ubansa. Sai na ji na tsaya cak, na juyo na dubesu suna nan a tsaye suna kallona. Na juyo na dawo na mikawa Micheal ya miko min dan na rungumeshi ina kuka, har cikin raina bana son rabuwa da dan nan duk rintsi. Aka rasa mai yin magana har tsawon wasu *yan mintuna. Sai Micheal ya ce in zo bakin mota in ga wani abu. Naki tafiya saida yayi ta min magiya sannan na bishi a baya, abokinsa ma na biye damu. Fargaba nake karfa su danke ni da jaririn su wurga a cikin mota, sai baya-baya na keyi. Ya bude mun but din motarsa na kalla babu abinda nake gani sai hadaddun akwatina guda biyu manya-manya. Koda ya budemun ciki sai naga tsala-tsalan rugunan Jarirai ne masu kyau da laushin gaske *yan waje masu tsada, ga pampers katan guda. Daya akwatin kuma leshina ne da atamfofi da shadda har da takalma da jakarsu da turaruka masu tsada. Cikin fushi na ce "Mungode amma ka juya da abunka bama bukata. Na yi gyaran murya na ce "Micheal ka yiwa Allah ka dubi girman iyayenka ka rabu damu ka daina zuwa gidanmu balle iyayena su ganka, ka kuma cirewa ranka zaka aureni har abada, na riga na shaidawa iyayena duk yadda aka yi Harriet ce ta haihu na taho da dan kuma ita kanta bata san wanda yayi mata cikin ba. Kana da kunya yanzu zaka dubi idona kace dan gidan Harriet danka ne? Ka manta lokacin da take sanar maka cewar har yanzu cikin da kayi mata bai zube ba? Kace mata duk ranar da ta kawo maka da ko *ya ta ce naka ne sai ka fasa dan? Ka manta ranar da zata haihu bamu da kudin zuwa asibitim nayi maka magiya ka zo ka kaita asibiti ka ce kai ba danka bane su mutu mana. Ka manta ne Micheal? Hawaye yaci gaba da kwaranyo min yayin da Micheal ya sunkuyar da kansa kasa yayi shiru. Abokinsa na cikin mota a zaune yana saurarenmu, sai gyada kai yake yana sauraron wannan abun al'ajabi. Ma sharbe hawaye na sake rungume yaron na ce "Kamar yadda kace Harriet ta mutu idan har kai zaka kaita asibiti, to baka kaita asibitin ba kuma ta mutu. Amma kafin ta mutu cemun tayi in rike danta amana bata cemun in kaishi wajen Mahaifinsa ba. Micheal ina rike yaron nan ne saboda kawata marigayiya Harriet badan kaiba. Ka cuceni ka hanani karatu amma duk nawa mai saukine tunda baka batamun rayuwa ba ka yaudareni. Wa danda ka yaudara ka rabasu da makaranta, ka yiwa Harriet ciki, Janet ka hadata da abokanka ta zama *yar fashi daga karshe kai musu sanadiyyar barinsu duniya dungurungun. Ka tafi ka bani waje bana son ganinka zan rike dan Harriet amana, kuma in Allah Yaso bazai zama mai irin halinka ba. Na juya na nufi gida ina sharbar kuka nabar Micheal anan tsaye abakin but tamkar an gina shi. Ina shiga ban tsaya ko ina ba sai na nufi dakina da sauri ina shesshekar kuka. Mahaifiyata na wuce a falo tana karatun jarida ita da Mama Tabita tana gogo-goge suka bar abunda suke yi cak suka bini da kallo. Ina shiga daki na datse, na haye kan katifa na bude sabon shafin kuka, yaron ya bude idansa yana ta tsotsar hannu alama ma yunwa yake ji. Nayi kuka ya ishe ni nayi addu'a Allah Yasa Micheal ya tafi ya rabu dani kar Allah Ya sake bashi ikon dawowa. Na tashi na tsiyayo ruwan zafi a flaks na dama masa madara ina bashi. Hirar da Tabita take yi da Mahaifiyata ita ta tsayar dani daga abunda nake, nayi tsai ina sauraronsu. Labarin dana bata na game da Micheal da Harriet take bata. Abun mamaki kafin Tabita takai aya Mahaifiyata harta rufeta da fada wai karyar banza wannan labarin bana kamawa bane. Wai karya nake dana ne. Muryar Mahaifina naji ya shigo sai kuma naji muryar maza da yawa da alama bashi kadai bane da baki yake tafe. Nayi sauri na karasa bashi madarar, na sake daukar zani na sabashi a baya na lallabo na bude mukullin dana datse kofa na bude kofar kadan na leko cikin falon. Gabana yayi mummunan faduwa a lokacin dana hango Micheal da abokinsa a zaune tare da iyayena suna gaisawa. Mahaifina ya ce "Nazo zan shigo na gansu a tsaye a jikin get da motarsu sunyi jigun-jigun, bayan mun gaisa suka ce mun wajan Fatima suka zo taki sauraronsu, ta shige gida ta barsu. Suna cemin daga Bauchi suke saina ce to su shigo. Mahaifiyata ta kalle su ta ce "Cikinku a kwai Micheal? Micheal yayi murmushi ya sunkuyar da kai kasa ya ce "Mama nine. Sai Mahaifina ya ce "Oh kai ne ka hana *yata karatu kayi mata ciki? Micheal ya yi shiru ya sunkuyar da kai kasa. Mahaifina ya rikice da fada inda ya shiga bata nan yake fita ba fada yake tun karfinsa tsakani da Allah. Har fadi yake sai dai kotu ta raba su. Mahaifiyata tana lallashinsa tana bashi baki da kyar ya fara saukowa. Micheal da abokinsa suka durkusa gwiwoyunsu a kasa suna rokon a gafarta masa yayi kuskure.