Sashe 36
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read
Me zaku ce game da Member 2 da suke son zama Admin a wannan page?
Na daya zai dinga rubuta littafin SHAFI'U DAUDA GIWA
Na biyu shi kuwa WA'AZANTARWA zai dinga yi
Ya kuka gani? Kuma me zaku ce?
________________ YARENA ADDININA.
___CI GABAN LABARI
Na fito bakin kofar dakin na tsaya ko ban fada ba kowa yasan ina cikin tashin hankali. Ina son Jaririn Harriet tamkar dan da na haifa a cikina. Ina tsoron halin da zan shiga idan aka ce min ya mutu. Fitowar likitan ya katse kukan da nake. Ya ce in shigo dakin, ya fara min bayanin abun da yake damun yaron ya ce "Yaron baya samun kulawa, ma'ana ana bashi madara ko nono ba tare da ana tallafo kansa ba, a kwance ake bashi yadda zai zuraro ta hancinsa ya kware. Haka kuma bayan ya sha ba'a dagashi akan kafada har sai yayi gatsa, sai a barshi a kwance har nonon ya gargara yabi ta wajan da yake shakar iska. Sannan ana bari yana shakar sabulu idan an zo yi masa wanka. Sune suka taru suka hana shi numfashi badan anyi saurin kawo shi asibiti ba an zuke masa, gaskiya daya rasa ransa. Na sulale na zauna kan wata kujera ina rusa kuka, ya dube ni sosai sai ya ce "Danki ne? Na gyada kai alamar eh. Ya girgiza kai ya ce "Fada min gaskiya ba ke kika haifi dan nan ba, ina Mahaifiyarsa? Dole ki fada min gaskiya don kar a sake samun irin wannan matsalar. Saboda rayuwar yaron tana cikin hatsari dole in yi magana da Mahaifiyarsa idan ma yara irinki take barwa danta to ta daina. Cikin sheshekar kuka na ce "Mahaifiyarsa ta mutu. Ya ce "To wacece take rike da shi? Nayi shiru can na ce "Ni ce cike da mamaki ya tambayeni "Ke ce? Ina Mahaifiyarki? Na ce tana gida. Ya ce "Lallai-lallai ina son in yi magana da ita ko wani babba ba ke ba. Na goge hawaye na ce "To bari inje in kirasu. Ya ce "Yauwa gara kije ki kirasu in yi magana da wani babba. Na ce "Zan iya tafiya da shi? Ya ce "Ki dauke shi ai nagama yi masa abunda zanyi masa ya samu sauki Insha Allah. Na saka masa rigarsa da wandonsa, sai tsotsar hannu yake da alama yunwa yake ji, na goya shi.
Na bude jakata zan dauko kudi in biya likita, sai naga wayam babu ashe ashirin din dana bawa mai babur din nan ita kenan. A zatona da kudi a cikin jakar sai nayi kasake ina dogon tunani, san nan na tuna ashe na kashe kudin shekaran jiya tsabar rudewa tasa na manta. Na ci gaba da binciken Jakata ina zulumin yau me zan cewa likitan nan, bani da kudin da zan biya shi wannan uban aikin da yayi min, sai na ji na lalubo sarkata ta gwal a cikin aljihun jakata na laluba kunnena na ji dankunnen sarkar a kunnena, zoben a yatsana da awarwaron gwal guda biyu a hannuna. Naga sarkar babbace sosai bazan iya bashi ba, awarwarayen ma sunyi girma sai nayi tunani in cire *yan kunnayen da zoben in bashi matsayin kudin aikinsa tunda bani da kudi. Shi dai yana tsaye yana kallona, na cire *yan kunnaye da zoben na dubeshi na dukar da kai kasa cikin ladabi da fargaba na ce "Likita na duba jakata ashe ban taho da kudi ba, ga dan kunnena da zobena na gwal ka karba a madadin kudin aikinka. Sai naji ya bushe da dariya ya ce "*Yan mata yaya sunanki? Na amsa masa cike da fargaba "Sunana Fatima. "Fatima, Fatima is a nice name, I like this name, Fatima is my Mother's name. Na ce "Na gode, ya ce "Fatima me yasa kikayi tunani bari ki bani gwal dinki a madadin kudin aikina, baki yi tunanin zan iya yi miki kyauta ba? Nayi murmushin karfin hali. Yaci gaba da cewa "Saka dan kunnanki da zobanki, karki damu nayi miki komai kyauta sai dai kamar yadda kika yi alkawarin zaki je ki kira wata babba ku zo tare ina jiranku kafin nan zuwa lokacin da zan tashi. Ina fatan zaku zo? Na amsa masa da "Eh yanzu zan je in kirata. Ya sake dubana cike da murmushi ya ce "Fatima zaki gaya min gaskiya game da jaririn nan, da inda kika samo shi? Domin kinyi kankanta ace danki ne wannan, baki yi kama da wacce ta haihu ba. Kiyi min alkawari zaki fada min komai harda sauran tarihin rayuwarki? Na amsa masa da "Eh nayi alkawari. Maganarsa ta karshe ita ce "Thank you very much my dear. Yayin daya ci gaba da kallona yana murmushi, na sunkuyar da kai kasa na fara tafiya, shi kuma ya fito bakin kofar dakin yana kallona ina tafiya.
Kamar daga sama naji an kira sunana na tsaya cak na waiga sai naga likitan ne yake kirana. Na juya na dawo inda yake a tsaye. Yayi min murmushi wanda ko bai min bayani ba nasan ma'anar murmushin. Wannan karon cikin harshen Fulatanci ba Hausa ba da Turancin da muke nagana tun dazu, ya ce "Baki tambayeni sunana ba. Nima cikin harshen na ce "To yaya sunanka? Ya ce "Dr. Hani. Nayi murmushi mai wuyar fita na ce "Dr. Hani na gode. Na juya naci gaba da tafiya bai bar wajen ba har sai da ya daina hango ni na fita daga get din asibitin. Ina fita na kalli gabas da yamma, kudu da arewa bansan ta ina zan fara ba, ina zan dosa? Meye abun yi? Ina mafita? Na farko bani da kudin achabar da zan koma gida, na biyu babu yadda za'ayi in je in kirawa Dr. Hani Mahaifiyata yayi mata bayani akan matsalar yarona, don ita kanta taki tsayawa taji gaskiyar al'amari akan yaron, haka daga ranar data gasgata bani nahaifi yaron nan ba to lallai dole in mayar da shi inda na dauko shi, ni kuma ina sonsa kamar raina. Don haka Dr. Hani zai tsufa yana jirana ba zai ganni ba. Sai babbar matsalata ta uku zancen aurena da Micheal da ya karato, ana zancan sati mai zuwa za'a zo da danginsa a zauna akan maganar auran. Sai naji zuciyata ta cushe na rasa me yake min dadi. Sai na rushe da kuka ina tafiya ina kuka. Na yanki hanyar cikin gari ba unguwar mu ba, bansan in da na nufa ba.