← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 80

Sashe 25

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 6 min read

sani. Washe gari da daddare suka shirya suka sani na shirya muka tsuke da dan karamin siket din jeans da *yar riga ba dankwali da takalmi me tsini sai jaka kowacce ta rataya, muka fita. Janet ta ce da masu achaba su kaimu Hotel. Nayi mamakin yadda aka yi suka san in da zamu sami *yan iskan maza suma himili guda manyan masu kudi. Suna ganinmu suka yo kanmu kowannensu yana cewa ni yake so daga karshe dai wani mutum ne ya daukeni, bana jin dai Musulmi ne kuma a kalla ya bawa shekaru hamsin baya. Suma kawayena duk suka sami nasu costomers dakunan da muka shiga dukka ukun ajere suke. Su Janet sun fahimci a tsorace nake ko hannuna ya rike sai in fisge kafin mu shiga dakin Janet ta kirani gefe ta zazzageni tace saura kuma idan na shiga in ki yarda dashi, dole in saki jiki in faranta masa. Kafin ayi wani abu in tabbata ya bani kudina nasa a jaka. Na amsa mata jikina yana karkarwa sannan na dawo wajensa itama ta koma wajen nata kowacce da nata, mu ka shiga dakuna. Ya mayar da kofa ya datse sai gumi ya keto min na hau karkarwa. Ya zauna akan gado ya jawo hannuna na zauna a kusa dashi kamar ace kule ince cas in zura da gudu dan tsoro. Ya dubeni yayi murmushi ya ce "Wai ke wannan ya haka, ko dai sabon shiga ce? Ya miko hannu zai tabani nayi zumbur na mike tsaye na goce. Ya sake kallona cike da mamaki ya ce "Lafiya kike guduna, to nawa zan biya kwana daya? Nayi shiru can na ce dubu biyu. A ganina na ballo wasu makudan kudi masu yawa. Ya kwashe da dariya harda buga kafa. Ya ce "Haba baby ai kinfi dubu biyu ko kallon fuskarki da nayi ai na biyaki dubu biyu balle mu kwana tare, na kara miki zan baki dubu goma. Na zazzare ido don mamaki na fada a bayyane na ce "Dubu goma? Yasa hannu cikin wata *yar jakar hannunsa wato (brief case) ya zaro bandir din Naira dubu goma ya mikomin, na karbi kudin nan ina jujjuyawa don mamaki, murna ta kamani. Na ce a raina "Na sami kudin da zanje in biya Malamina su bani sakamakon Jarabawata sannan inyi kudin mota in koma gida. Nasa kudin a jakata. Ya jawo hannuna nazo na zauna a kusa dashi. Yasa hannu zai shafa wuyana sai naji maganar Hamma Huzaifa a karkashin zuciyata. "Kada kiyi zina, kiji tsoron Allah duk inda kike ko ina kika shiga kika buya Allah na ganinki. Saina zabura na mike tsaye na ce "Malam yi hakuri bude mun kofa tafiya zanyi bazan iya ba. Na bude jakata na dauko masa kudinsa na ajiye masa a gefensa. Ya bude baki yana kallona. Yace "Me yasa? Na ce "Kawai bazan iya ba, ina tsoron Ubangijina bazan iya zina ba. Ya kyalkyale da dariya ya ce "Ko ki karbi kudina ko karki karba babu yadda za'ayi in yadda ki subuce min gara ki tsaya in miki a hankali kafin inyi miki da karfi. Na rataya jakata na nufi kofar fita, daman da mukullin a jikin kofar zan murda in bude, sai naji cimak an daukeni ta baya sai naji ni a tsakiyar gado yana shirin ya afkamin. Naji raina ya fara tafasa don tsananin bacin rai, nan da nan na rasa hayyacina, muyagun dake jikina suka tashi. Na lalubo wata katuwar kwalbar lemo dake ajiye a gefen gadon na rotsa masa akai. Ko sakon daya ba'a kara ba jini yayi masa hijabi a fuska. Ya rike kai sai ihu yake zanbadawa. Na yar da jakata da takalmi na bude kofa zan fita da gudu naci karo da jama'ar da suka jiyo ihunsa suka rugo suga meke faruwa. Caraf suka damkeni. Suna lekawa cikin dakin suka ganshi cikin jini. Suna kokarin yimin duka abinka da ba yin kaina ba naji na fara zubar da kartai a kasa suka sakeni ba shiri na arce waje na fita daga hotel din da gudu. Harriet ma da nata saurayin dai-dai lokacin ya gaggalla mata mari ya kwace kudinsa ya tunkudota waje daga daki saboda ya tarad da ita da rusheshen ciki, itama ta lallabo ta fito waje. Janet itama dakyar tasha da nata yaga abunda nayi saiya korota ba tare daya bata ko kobo ba, da dabara da haure-haure ta fito daga hotel din ance sai an daketa tunda tare muke. A gida muka hadu wannan na shigowa sai kaga waccen itama ta shigo a guje a galabaice. Ranar naga tashin hankali a wajen kawayena zagi da dungure kai nasha, wai duk ni nake jawo musu masifa. Har wayau basu daddara ba washegari suka sani dole na shirya muka fita amma muka canja hotel. Aka sake kwatawa duk yawan kudin da zasu bani bana iya yarda inyi zina domin tsoron Allah ya shigeni tun ina karama, Hamma Huzaifa ya cusa mun haka a raina. Allahu akbar Allah Yayi masa albarka ya sami ladana ta wannan bangaran. Ga tsananin bukatar kudi ina yi amma tsoron Allah ya hanani in aikata sabon Allah in sami kudi. Su kuma mazan idan naki yarda da su sai su kasa hakura dani su yi kokarin zasu yimin ta karfi daga nan san hankalina ya gushe raina ya baci in fita hayyacina in farfasa musu kai. Don barnar da nake musu ta yau tafi ta jiya, ta gata tafi ta citta kullum mune a guje an biyomu na fasawa maza kai, laifina yana shafar kawayena. Da kansu suka hanani binsu suka sha zagina suka ce sai in zauna a gida na dinga dafa musu abinci tunda haka nake so. Tafi nono fari daman haka nafi so. Haka na kasance duk sanda zasu tafi su bani kudin cefane su zano mun abubuwan da suke so in suyo in dafa musu. Jikina yana rawa nake karbar kudin cefanen in hau achaba inje kasuwar Wunti ko Mudalawan da ke nan Bauchi in sissiyo in dawo. Da murhu da itace in dafa musu abinci idan da daddare suka fita to da sassafe nake dafa musu abinci kafin su karaso, idan kuma fitar yamma suka yi kafin dare na kare musu girkin dare. Duk da ba sabawa nayi da aiki ba, girkin ma ban iyaba balle hura wuta haka nake daddagulawa ina yi ina rugawa da gudu wani gida dake kusa damu ina tambayar matar gidan yadda zanyi kafin in kare girkin duk nayi wujiga-wujiga na fita hayyacina. Hawaye, majina, gumi, bakintukunya a rigata kaca-kaca. Amma duk da wahalar nan basa godewa, Janet ma saita yi fada da zage-zage kafin ta fara cin abincin. Ni dai hakuri nake basu don kar suyi fushi suce sun daina bani kudin cefane nima in fita in nemo.
Chapter 25 · 0% Book details