← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 80

Sashe 52

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da alama wannan hukunci da Baba na Doko ya yanke akan Suhaif bai yiwa kowa dadi ba musamman Mahaifiyar Suhaif, sai ta fashe da kuka tana cewa "Idan bai zauna a nan ba, bai je Doko ba ina zai je? Baba na Doko ya ce "Ina ruwana ya koma garinsu Iman. Baba na Kano ya yunkura zaije ya tsayar da Suhaif kada ya tafi Baba na Doko ya jawo shi ya ce ya koma ya zauna tunda ya rantse sai Suhaif ya tafi. Mama da Najib suka dinga rokar Baba na Doko yayi hakuri yabar Suhaif tunda yayi nadama ya ce yayi kuskure a hakura. Baba na Doko ya ce "Da gangan yayi, yayi tafiyarsa, dadi ne yayi masa yawa yana daga kwance ake ciyar da shi shiyasa bai san zafin nema ba, amma idan ya je yasha wuyar nema, gobe idan an samar masa aiki ba zai yi masa rikon sakainar kashi ba. Suhaif ya ja motarsa ya fice ba tare da yasan inda zai tafi ba. Bakin ciki goma da ashirin, yana ta yawo a gari daga wannan titi zuwa wancan, har karfe tara da rabi na dare sannan ya tuna da wani abokinsa Rabi'u wanda suka gama makaranta tare yanzu yana lecturing a B.U.K, yana zaune ne a staff qauters na B.U.K. Suhaif ya nufi gidan Rabi'u ta ci sa'a kuwa ya same shi daman bai yi aure ba, kai tsaye ya shiga gidan. Rabi'u ya yi murna da ganin Suhaif musamman da ya ce masa kwana ya zo taya shi. Sun dade suna hira sannan suka gangaro hirar dalilin daya kawo shi, Suhaif ya zaiyana masa labari kakaf. Rabi'u yayi masa fadan bai kyauta ba, dan me zai bar aikinsa ya tafi dole hankalinsa ya tashi. "Yanzu meye abun yi? Rabi'u ya tambaye shi. Suhaif ya ce "Bazan koma gidanmu ba saina sami aiki saboda haka gobe da sassafe zan bar garin nan duk inda aiki yake zanje in samu. Rabi'u ya bawa Suhaif shawara ya zo suje gidan gobe ya taya shi bawa Iyayensa hakuri tunda suna da hanya zasu iya samar masa wani aikin. Suhaif ya cewa Rabi'u ya manta da zancen bawa Iyayensa hakuri, domin ba zasu sauraresu ba, shi dai zai kara gaba neman aiki. Daga karshe Rabi'u ya bawa Suhaif shawarar yaje Lagos wajen abokin Baba wato M.D na port Authority ya duba yaga ko akwai yadda za'ayi a saka sunansa a cikin wadanda su kayi interview saboda akwai sanayya zai taimaka. Suhaif ya yarda da shawarar Rabi'u, ya yarda goben zai shirya ya tafi Lagos. Washe gari da sassafe Suhaif ya shirya, bayan sun karya kumallo sai ya yiwa Rabi'u sallama, Rabi'u yayi masa fatan alheri da fatan Allah Ya kiyaye hanya. Suhaif ya kama hanyar Lagos tafiya yake ba ji ba gani, ya isa cikin dare sai ya wuce ma'aikatar N.P.A. A cikin motarsa ya kwana, da gari ya waye ya shiga Masallacin kusa da nan yayi sallah, da ma'aikata suka fara zuwa wajen aiki sannan yayi kokari aka yi masa iso wajen Manaja. Duk da sanin da Manaja ya yiwa Suhaif sai da ya sake tambayarsa "Daga ina? Suhaif ya gyara zama ya yi masa bayani. Manaja ya bata rai ya ce "Na gane ka ai, meke tafe da kai? Ai kasan mun gama tace wadanda zamu dauka ko? Infact na kira Babanka several times cewar ya ban ganka ba, tun yana boye mun har ya fada mun gaskiya cewar an rasa inda ka tafi baka son aiki. Suhaif ya hau soshe-soshe ya ce "Ranka ya dade nasan nayi kuskure, and I realize my mistake, am sorry ran Iyayena ya baci har sun ce in bar musu gida. Sun ce in je in nemo aiki da kaina, dan Allah a taimaka min ranka ya dade. Manager ya yi sauri ya ce "Actually nayi iya kokarina in baka aiki kaine kaki, yanzu ba yadda zanyi maka kayi hakuri. Suhaif ya rike kai ya yi shiru. Manager ya ci gaba da cewa "Naga alama a gajiye kake bari in sa direbana ya kaika gidana ka huta. Suhaif ya ce "Na gode Baba kamar kasan a gajiye nake na yini na kusa kwana ina tafiya. Bayan Suhaif da direba sun tafi gida, Manager ya kira Baba na Kano yake shaida masa ga Suhaif ya zo, ya zaiyana masa duk yadda su kayi aiki dai babu sun gama dauka. Baba na Kano ya roki Manager ya taimaka ya ajiye Suhaif a gidansa tun da akwai wajen ajiye baki ko Allah zai jeho wani aikin daga wani bangaren. Manager yana ganin mutuncin Baba na Kano ba zai iya kin yi masa duk abunda ya tambayeshi ba, ya amsa da "Ba damuwa za a binciko Insha-Allah ko a wani bangaren ne. Suhaif yana zaune a gidan Manager har na tsawon wata biyu babu abinda yake yi sai kwanciya, babu aiki babu alamarsa. Sai dai Suhaif yana taimakawa Manager akan harkokinsa, yana aikensa wurare kuma yaje ya aiwatar masa da duk abunda yasa shi babu kuskure. Idan harkar kudi ne kuwa babu munafunci, ko kwabo ba zai dauka ba. Da gangan Manager yake hana Suhaif kudin kashewa kuma yasan bashi da kudi, yana son gwada hankalinsa ko zaice duk wannan wahalar da nake yi masa bai biyani ba, ko kuwa zai rinka rage kudin da yake aikensa. Sai yaga Suhaif ba haka yake ba kuma bai damu ba. Dan haka Manager ya cure Suhaif ya kudiri niyyar nemar masa aiki ko a wane waje ne. Amma a hirar da suke da Suhaif ya bugi cikinsa yaji ra'ayinsa game da aiki. Suhaif ya nuna baya son aiki kwata-kwata saboda a fadarsa yana da matsalar da ta dami zuciyarsa baya so ya fara aiki ya je ya zauna a office yana tunani ya kasa aikin yadda ya kamata. Da dai zai sami jari yayi business ko kwangila da yafi so. Duk da Manager bai gane damuwar da Suhaif yake ciki ba amma ya kudira a ransa zai yiwa Suhaif yadda yake so. Zai bashi kwangila da kuma kudin da zai yi kwangilar tunda bashi dasu. Suhaif na zaune a bangaren da aka sauke shi a gidan Manager, shi kadai yana tunanin abar kaunarsa kamar yadda ya saba wato Iman. Ya ji wayar dake ajiye a gefen gadonsa tayi ruri ya dauka da sauri. Manager ne yake magana ya ce da Suhaif ya zo office ya same shi. Suhaif bai bata lokaci mai yawa ba ya je ya sameshi a office. Manager ya mika masa takardun wata kwangila mai tsoka ya ce "Ga wannan taka ce. Suhaif ya hau dogon tunani "Ni da bani da ko sisi ya zanyi in yi kwangilar miliyoyi? Manager ya bashi amsar tunaninsa "Mu zamu ranta maka kudi kayi, sannan mu biya ka akan lokaci "Tsarki ya tabbata ga Allah (S.W.A). Suhaif ya fada yayin da ya sulale ya zauna dan murna da mamaki, lallai wannann shine arziki a dare daya. Allah mai azurta duk wanda Yake so a duk lokacin da Ya so. A cikin shekara daya Allah Ya azurta Suhaif fiye da tunanin mai karatu. Kwangilolin da yayi ta yiwa port Authority ake biyanshi akan lokaci ya sami makudan miliyoyi. A shekara ya kama hadadden gidan haya duplet a unguwar manya (victoria island) wanda kudin hayar ma kadai zai iya siyan wani gidan. Kafin ya samu a hankali ya binciko inda zai sayi fili ya gina gida irin wanda ya keso, a garin da ya keso, da unguwar da yake so. A lokacin Suhaif ya canja mota kirar zamani wacce ake tsakiyar yayinta a lokacin. Nan fa Suhaif yaga ikon Allah da abunda yafi karfin idonsa, wato cincirindon *yan mata da suke sonsa HAR DA SU WA'E . Shi kuwa basa burgeshi ko daya baya son su, soyayya bata gabansa har yau har gobe Iman ce a zuciyarsa. Ya hado tara ta arziki ya zo ya gaishe da Iyayensa, a Kano ya sauka. *yan gidan sun sha mamakin yadda Suhaif ya zama a shekara guda. Duk da bai yi kiba ba amma yayi fari, kallo daya zaka yi masa kasan yana cikin daula, ni'ima da wadata. *Yan gidan gaba daya sunyi farin ciki da zuwan Suhaif, saboda sun dade basu ganshi ba. Yana musu gizo kamar ba shi ba. Gara Baba na Kano, Baba na Doko da Najib sunje Lagos sun ganshi kwanakin baya, amma Mama, Goggo, Naja'at da Zubaida shekara guda cur kenan basu ganshi ba. Shima farin cikinsa baya musaltuwa dan haka nema ya sakarwa kannensa fuska ya daina musu muzurai. Har a kwano daya suke cin abinci shi da Naja'at da Zubaida, bayan zama akan kujera daya ana wasa da dariya har yana tsokanarsu wai ina samarinsu, bayan manya-manyan leshina daya siyo musu, mamaki ya ishi Zubaida da Naja'at ganin yadda Suhaif ya sauko wanwar. Kwanan Suhaif biyu a Kano sannan ya shirya ya ce zai je Doko ya kwana biyu. Najib ya so su je tare amma shi yanayin aikinsa na Banki ke hana shi sukuni. Wata raba har asabar da lahadi ma sai sun je banki. Suhaif cikin dandatsetsiyar motarsa ya isa kofar gidansu na Doko. Tuni kafin ya fito daga mota matukar mamaki ya rufeshi a lokacin da ya yi ido biyu da motar Zubaida a kofar gidansu. Yana fitowa direban gidansu Zubaida ya taso da sauri ya zo ya karbi jakar hannun Suhaif gami da yi masa sannu da zuwa. Cikin fara'a Suhaif ya tambaye shi "Malam Dauda yaushe ka zo, ba dazu-dazun nan na ganka a zaune a kofar gida ba a Kano? Malam Dauda ya yi dariya ya ce "Ranka ya dade ai kana fitowa mu ma muka fito muna binka a baya, sai kayi hanyar cikin gari mu kuma muka zarto nan. Isowarmu kenan Allah Yaja zamaninka. Suhaif ya ce "Kai dawa ku kazo? Malam Dauda ya ce "Ai Hajiya Zubaida na kawo, ai da niyyar makaranta zan kaita muka fito sai kawai ta ce in kawota nan ta fasa zuwa makarantar. Suhaif ya yi shiru mamaki ya rufeshi ya yi minti biyar bai motsa ba, ya kurawa kofar gidansu ido kawai yana tunani yana tambayar zuciyarsa. "Shin me Zubaida ta zo yi Doko da rana tsaka ba tare da ta fadawa kowa ba? Kada fa a ce zancena ta zo
Chapter 52 · 0% Book details