← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 80

Sashe 77

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Iman ta runtse ido sai hawaye ya zubo ta ce "Yanzu ina Micheal din yake? Ya ce "Yana gidan Mahaifiyarsa, nan ne ba nisa cikin G.R.A nan yake. Ya zama tamkar tababbe babu shiga gidan, yanzu sai ya farfasa maka kwalba a kai, abincinsa giya da taba. Iman tayi ajiyar zuciya ta ce "Mansir ka rakani, shi na zo nema garin. Mamaki marar misaltuwa a fuskar Mansir ya kalleta ya kalli *yan cikin motar da alama dai mai tukawar mijinta ne *yan bayan kuma Babanta da wanta. Me za su je wajen Micheal suyi? Mansir ke tambayar zuciyarsa. Ya ce "Ba matsala muje in kaiku. Ibrahim ya dora Muhammad akan cinyarsa suka matsawa Mansir ya shiga suka tafi yana nuna hanya har kofar gidan Mahaifiyar Micheal. Mansur ya ce "Ga gidan ni zan koma, shawarar da zan baku kuyi a hankali domin farfasa kai yake da kwalbar giya, ni bazan shiga ba. Iman ta ce "Mansur ba zaka tafi ba ka dai tsaya tukunna. Zan baka linkin kudin da kake samu a rana idan kayi hakuri, ina so ka taimake ni kai ka san gidan nan da halin da Micheal ya ke ciki, yanzu yaya zamu yi mu ganshi? Mansir ya ce "Ba ki nayi ba Pretty amma me yasa kike so lallai-lallai sai kin ganshi mutumin daya zama haka? Iman ta nuna masa Muhammad ta ce "Kalli yaron sosai. Mansur ya zurawa Muhammad ido ya ce "Kai! Ai kamar su daya da Micheal sak. Iman ta ce "To dan sa ne. Cikin mamaki Mansur ya ce "Tare kuka haifa? Iman ta girgiza kai ta ce "Tare da Harriet suka Haifa amma ta mutu garin haihuwarsa ni na dauke shi, shine na zo in nunawa yaron Ubansa. Mansur ya ce "Kwanaki a garin nan naga Harrit din ai. Ko ba wannan kawar taki ba? Iman ta zabura ta dafa kirji ta ce "Kaga Harriet a ina? Kai Harriet ta mutu ba dai ita ka gani ba mai kama da ita dai. Ya ce "A'a ita ce. Ba ita ce bakatsiniyar nan ba yarinyar Gabriel da nake gidansa? Iman ta ce "Okey! Fadila zaka ce min. A ina ka ganta? Ya ce "Tayi aure harda *ya*yanta, naje gidan nayi musu haka, itama ita ta fara gane ni. Iman ta ce "Allah Sarki dan Allah ka kaini in ga Fadila idan mun gama da nan. Suhaif, Ibrahim da Malam Shehu suna zaune a mota suna kallon Iman da Mansur suna sauraran abunda suke fada. Sai yanzu Suhaif yayi magana ya ce "Wai ku fada min yadda zamu shiga gidan mai fasa kai da kwalba. Iman ta ce "Yaya Suhaif ni da Mansur zamu shiga, ku jira mu anan. Suhaif ya girgiza kai ya ce "Bana so ki shiga ki barmu mu maza mu shiga. Malam Shehu ya ce "Mu shiga kawai da ayar Allah ba zai iya daga kwalbar ba balle ya rotsawa wani kai. Suka fito daga mota su duka suka dunguma cikin gidan. Mansur da Suhaif ne a gaba. Iman rike da hannun Muhammad a tsakiya. Malam Shehu da Ibrahim a baya kowa yana karanto addu'ar dake bakinsa. Suna tafe suna kalle-kalle, gida kamar babu bil'adama a ciki bayan dogayen ciyayin da suka rufe farfajiyar gidan, kofar shiga cikin gidan ma da kyar mutum zai samu ya shiga ciyayi sun yi tsawo kamar bishiyoyi. Suna shiga falon kuwa kujeru ne kowacce ta kalli kabilarta. Talabijin a kife a kasa T.B stand an rabata biyu. Yi suke suna waiwaye-waiwaye kada ya diro musu ta inda basu zata ba. Suka yi ta magana shiru, wannan ya ce Hello, wancan ya ce Hi, wannan ya ce ka fito kayi baki. Babu motsin kowa a gidan kamar ma babu mutum a gidan. Sai suka shiga bubbude kofofin dake falon suna lellekawa, dakuna ne da bandakai babu kowa a ciki sai yana da kura. Mansur ya shiga kicin ya bude kofar store din kicin babu komai sai duhu ko tafin hannunka ba zaka iya gani ba. Su Suhaif a falo sai suka ji Mansir ya kwalla kara a lokacin da yaji an cafke shi. Suhaif Ibrahim da Malam Shehu suka kutsa cikin store da gudu sai suka ga Micheal ya shake Mansir a jikin bango yana shirin kwakwale masa makogaro. Nan dai maza suka saki karfi suna jan Micheal amma gamgam sun kasa fusge hannunsa daga wuyan Mansur. Kokari yake ma ya wawuro daya daga cikinsu ya hada ya matse. Iman na falo rungume da Muhammad kam suka shige wani lungu sai sharbar kuka take. Taji shiru har yanzu ba su fito ba sai kakarin Mansir take ji kamar mai shirin tafiya lahira. Su Suhaif na cewa ja shi ta nan, rike hannun, a'a kafar za'a ja, sun kasa fisge Mansur daga hannun Micheal. Iman ta ce da Muhammad ya zauna a lungun kada ya fito, tana zuwa. Tun daga cikin store suka fito kicin ana ta dambe. Cikin rudani da tashin hankali Iman ta kuga da karfi ta ce "Micheal! Sake shi mana karka kashe shi. Micheal ya waiwayo da sauri ya dubi mai wannan muryar wacce tayi masa kama da muryar abar begensa Pretty. Sai kuwa yaga Pretty ce. Mansur da kansa ta fusge hannun Micheal daga wuyansa saboda Micheal yana ganin Iman sai jikinsa yayi sanyi. Sannan su Suhaif suka sake shi shima. Ya dade yana kallon Iman can ya ce "Pretty! Pretty!! Are you Pretty!!! Iman ta gyada kai ta ce "Yes I am. Micheal ya sulale ya zauna ya rike kai da alama tunani yake mai tsawo kansa ya daure. Mansur dai ido yayi masa jawur ya fita bakin baranda yana shan iska. Suhaif da Ibarahim suna tsaye suna kallon Ikon Allah. Malam Shehu kuwa yana jan carbi yana ta tofa addu'a kusurwa-kusurwar gidan. Iman ta durkusa a gaban Micheal cikin harshen turanci ta fara yi masa nasiha da wa'azi mai ratsa jiki. Micheal ya kwalla kara ya daki wata dorowa ya ce "Ke rabu dani, bakya ganin yadda na zama? Zaki ce min in yi hakuri rayuwar duniya sai a hankali. Na saraki, na rasa dana, na zo na rasa Mahaifiyata. Bayan dukiyata da abokaina dana rasa na rasa kafa guda daya. Dan me zan dauki duniya a hankali? Yanzu na fara kisa, yanzu na fara datsewa jama'a kafa, kowa sai ya rasa kafa a garin nan. Iman ta ce "Micheal yi hakuri duniya a sannu a hankali ake bin ta kaga da ka dauketa da karfi shi yasa ta zo maka a haka. Idan kayi hakuri za ka ga rayuwarka ta gyaru ka dawo rayuwar farin ciki fiye da tada. Ya gallawa Iman wata uwar harara ya ce "Ki gaya min yadda rayuwar da zata dawomin? Ko kin fara dawo da matatattu duniya? Ko kina iya dawo min da kafata da aka gutsire aka yar? Ko zaki iya auran mahaukaci ki zauna da shi? Don ada da nake cikakken mutum ma kin kini balle yanzu. Wani dacin kishi ya darsu a zuciyar Suhaif. Iman tayi murmushi ta ce "Duk wannan abubuwan da ka zano min amsar ita ce "A'a amma Allah Zai iya musanya maka da madadinsu gaba daya. Ya sake zabura ya fisgi kanannadadden gashin daya zama Dada saboda rashin aski ya ce "Da a ce wata ce bake ba, da yau sai na kasheta. Dan me zaki sani a gaba kina fada mun tatsuniya, dan kin daukeni mahaukaci ko? Kina so ki ce min zan iya samun wata uwar bayan uwata? Kina nufin zan sake samun wani sabon da bayan dana na wajenki daya mutu koma nace kika kashe min shi, daga baya na samu matsala likitoci sun ce bazan sake haihuwa ba. Na yi aure shekarun baya matar taga ba zata iya zama ba ta haihu ba ta gudu. Don haka karki sake kallona ki fada min wata maganar da hankali ba zai dauka ba, na san a bunda nake. Iman ta fashe da kuka. Sai Micheal ya tsaya yana kallonta can ya tambayeta "Kuka kike yi? Me yasa kike kuka? Kina tausayina ne bayan kin ki ni da? Kin guje ni bakya sona, kece kika sakani a cikin wannan halin. Domin son da nake miki, dana aureki zaki iya canja ni. Pretty me kike so yanzu? Fadi meke tafe da ke? Kinzo kiga mahaukaci ne ki tafi? Ko wadannan mazan ne suka satoki yanzu in kashe su? Duk abunda kike so zan yi, fada min. Iman ta share hawaye ta ce "Gaba daya rayuwarka ce bana so kaci gaba da irinta. Ina so ka canja, ka dawo addinina, zaka ga yadda Allah zai canja maka rayuwarka. Micheal ya tuntsire da dariya ya ce "Addininki! Ni zaki fadawa addini? Kin manta Mahaifiyata shugaba ce a wajen bauta? Iman ta ce "Addinina ba addinin Mahaifiyarka ba. Micheal ya ce "Wannene addininki? Iman ta ce "Musulunci. Ya ce "Ke Musulma ce? Iman ta ce "Ni Musulma ce shi yasa kaga bana zina, bana shan giya, bana fashi saboda tsoron Allah. Addinin Musulunci ya haramta duk wannan. Micheal yayi shiru yana tunani "Lallai gaskiya ne halin Pretty ya banbanta da namu tun a da, har muna tunanin bata da lafiya shi yasa bata zina. Yanzu ga makomar mu ita kuwa kalli yadda ta koma da alama tana cikin jin dadin rayuwarta. Iman ta ci gaba da yi masa wa'azi mai ratsa jiki yana sauraronta. Suhaif, Ibarahim, da Malam Shehu suma suka tsuguna a gaban Micheal suna taya Iman wayarwa masa da kai suna nuna masa karshen tayuwarsa bai zo ba, haka farin cikinsa a duniya bai kare ba. Ya yarda da Allah daya ne Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon ne. Can Micheal ya ce "Na yadda da Allah daya ne kuma Annabi Muhammd (S.A.W) Manzonsa ne. Sai gaba daya suka dau kabbara. Iman tana masa kalmar Shahada yana maimaitawa. Ta fashe da kukan dadi ta cewa Micheal "Ka zama Musulmi zaka ga alhairi a rayuwarka ta duniya da lahira. Daga yau ba sunanka Micheal ba zabi sunan da kake so a sunayen Musulmai. Ya ce "Sai yadda ku ka yi dani, ki zabar min kawai. Iman ta ce "Daga yau sunanka Ibrahim. Ta dubi Ibrahim marikin Muhammad ta ce "Saboda Muhammad tun a makaranta da sunanka ake kiransa ko? Su duka suka ce "Eh haka yayi. Iman ta dubi
Chapter 77 · 0% Book details