Sashe 12
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Au ba ki da rabo da kika sameni? Iman ta rike baki alamar mamaki ta ce "Ni na isa ince haka? Ai nafi kowa rabo dana sameka. Suhaif ya ce "Da gaske kike ko zolayata kike yi? Iman tayi dariya gami da rufe ido ta ce "Ai babu zolaya tsakaninmu. Suna tafe a hankali har suka isa makaranta Iman ta shiga ajinsu Suhaif kuma ya juyo ya dawo wajen me kosai. Iman ta iske kawayenta biyu a aji Rakiya da Laure suna shara, gaba dayansu suka hada baki suka ce "Iman yau kin makara mun rigaki zuwa. "Iman ta ce "Yau na makara gaskiya gashi nan har kunyi rabin shara. Bari inzo in tayaku. Rakiya ta ce "Gyara mana bencinnan karki shigo kurar nan yanzu ki turnike mana da tari. Iman ta hau gyara bencina kamar yadda suke a layi-layi. Muryar Malam Yahaya ce tasa dukkanninsu suka juyo suka kalli wundo da suka ji sautin maganar ya ce "Sannunku da shara, suna ganin Malaminsu sai dukkansu suka durkusa suka gaishe shi, ya amsa musu cikin lankwashasshiyar murya mai dauke da jimami. Kallo daya zaka yi masa ka san yau hankalinsa a tashe yake. "Malam yau kuwa lafiya? Iman ta tambayeshi. Malam Yahaya ya nisa yayi shiru yana tunani na wani dan lokaci. Sai gaba dayansu gabansu ya hau faduwa suka bar abinda suke suka nufo inda yake tsaye jikinsu na karkarwa. Malam Yahaya ya ce "Ku yi hakuri ku koma gida yau baza'a yi makaranta ba. Ku tari masu zuwa a hanya kuce sai nan da sati guda za'ayi makaranta. Rakiya ta dafe kirji ta ce "Lafiya? Iman kuma tuni hawaye ya fara kwaranyo mata babu abunda take sai karkarwa tana fargabar taji me zai fito daga bakinsa ya ce "Kamar yadda kuka sani dukkan mai rai saiya dandana mutuwa, Allah Ya yiwa dan uwanmu abokinmu, yayanku rasuwa a jiya da daddare yanzu muka dawo daga binneshi. Iman taji kafarta bazata iya daukarta ba saboda tashin hankali sai ta durkusa ba tare da ta iya bude baki ta yi tambayar da take so tayi ba. Waye ya rasu? Malam Yahaya ya ce "Malan Hadi ya rasu "Innalillahi wa'innailaihirraji'un suke karantawa yayin da Iman ta dora hannu aka tana jin jiri yana jujjuyawa da ita, hawaye kuwa daya na bin daya. Ya ce "Kar kuyi kuka addu'a zaku yi masa, ku tashi ku rufe ajin ku tafi gidanku. In ya so ko da yamma sai ku hadu kuje kuyi wa iyalansa ta'aziyya. Ya wuce ya tafi da sauri yana share hawayen da ya cika masa ido ganin kukan da Iman take shi yasa shi kuka. Rakiya da Laure suka goge guntun hawayen daya cika musu ido suka zo kan Iman wacce kukanta ya ribanya nasu, suna lallashinta dakyar da sudin godhi suka lallasheta ta tsagaita da kukan da take ta tashi daga tsugunan da tayi ta fito suka rufe ajin suka nufi hanyar komawa gidajensu. A hanya suka dinga cin karo da dalibai, suna ganinsu Iman suna dawowa sai suyi turus su tsaya. Sai suyi masa bayanin cewa ba makaranta saboda rasuwar Malam Hadi. Nan dai kowacce ta rafsa salati ta juya gida. Su Rakita suka yiwa Iman Sallama da suka zo lungun gidansu, suka shiga Iman kuma ta wuce ta nufi hanyar gidansu. Dai dai kan kwanar da Iman zata shiga gida ta ci karo da dandazon *yan ajinsu su biyar suna tafiya makaranta Iman ta tsaya suka gaisa. Talatu ta ce "Ah Iman mantuwa kika yi kika dawo? Iman ta girgiza kai hawaye ya zubo mata ta ce "Ba ayin makaranta yau saboda Malam Hadi ya rasu. Raiha ta ce "Wai yaya malaman makarantar nan suke ta rasuwa haka a jere a jere? Kunga ba'ayi sadakar arba'in din Malam Nayaya ba sai Malam shehu ya rasu. Ga shi ba'a fi wata biyu ba da rasuwar Malam Shehu Malam Hadi ya rasu. Allah na tuba. Mai jidda ta ce "Kuma dukakansu lafiya-lafiya ake rabuwa dasu sai dai aji sun mutu, babu ciwo. Ku kalli Malam Hadi jiya-jiyan nan fa ya zane *yan ajinmu ya farfasa mana baya. Lallai da yasan zai mutu da baici zalinmu ba. Dan ba laifin fari bare na baki ya hau dukanmu. Iman ta girgiza kai yayin da wasu hawaye masu zafi suka zubo mata ta ce. "Ya *yan uwana musulmai ku yadda da kaddara, kuma duk mai rai saiya dandana mutuwa, ko da ciwo ko babu ciwo sai an tafi. Allah Baya barin wani don wani yaji dadi. Ikon Allah Ya wuce haka ba mutuwar malamanmu a jere ba idan yaso zai iya hada garin nan koma kasar nan ko duk duniya ya kashe bazai karuba ba zai ragu ba. Shine Ya haliccemu kuma ya rayamu haka kuma zai kashemu a duk sanda Yaso fatan mu Allah Ya sa mu cika da Imani. Cikin sanyin jiki da gasgata maganar Iman ta ratsa zuciyoyin su dukkansu suka ce "Amin. Iman ta dafa kafadar Maijidda ta ce "Maijidda babu kyau fadar abu marar kyau akan mamaci domin shaidar duniya ita ake masa a lahira. Ku fadi abun alheri ko kuyi shiru. Domin Musulmi dan uwan Musulmine, kuma abunda kaso wa kanka kasowa dan uwanka. Muma za muso idan mun mutu ayi mana shaidar kirki. Dan Allah mu yafewa Malam Hadi koma me yayi mana. Allah ya yafe mana gaba dayanmu. Gaba daya suka ce "Amin mun yafe masa kuma Allah Ya jikansa. Zaka iya ganin farin cikin da Iman taji a fuskarta tayi addu'a, dukkansu suka daga hannayensu sama Iman na kwararo addu'a suna amsa mata da amin suka shafa. Sai Iman ta ce "Da yamma bayan la'asar dan Allah mu hadu a bakin ajinmu mu dunguma muje gidansa muyi musu ta'aziyya ko ba haka ba? Dukkan su suka ce "Haka yayi in Allah Yaso zamu je. Ummi ta ce "Mungode Iman kina gaya mana gaskiya, shiyasa muke son zama dake muna karuwa. Akwai ki da hankali, tunani, hakuri, ga ilimin addini, Iman sai na ganki nake tunawa da wani abun addini. Dubi yadda kike shiga kamar a Makka shi yasa nake kokarin in dinga koyi da ke. Iman ta yi murmushi ta ce "Na gode Allah Ya shige mana gaba to sai anjimanku saida yammar. Ta juya ta tafi. Maimuna bakuwa ce a garin jiya tazo gidan su Raiha *yar uwarsu ce Mamakin Iman ya hanata yin magana tun dazu cikin zumudi bata bari Iman tayi nisa ba ta ce "Wai wacece take burgeku saboda addininta? Iman ta ce muku sunanta? To karya take muku, taudararku take a nan garin dan tasan baku santa ba. Rafkatu sunanta, bama musulma ba ce arniya ce bata da addini. Har cikin shege tayi ta haihu a kashe Dan. Bata da kunya har danbe take da mahaifiyarta akan idona, kai in takaice muku tana cikin kungiyarnan ta matsafa masu shan jini wato (secretSociety). Sai karaf a kunnan Iman, Iman ta juyo a fusace ta kalli Maimuna suka hada ido, sai ta juya taci gaba da tafiya ba tare da tasan inda take jefa kafafuwanta ba saboda tsananin hankali da rudanin data shiga.