Sashe 68
Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 4 min read
Da misalin karfe goma sha daya na safe za'a daura auren Hamma Huzaifa da Iman. Misalin karfe tara Huzaifa ya shigo dakin su Suhaif cike da fara'a kai ka ce an masa albishir da Aljannah ne, hannunsa dauke da wata katuwar leda. Bayan yayi sallama ya shigo Najib ya je da fara'arsa ya mika masa hannu suka gaisa ya yi masa kirari ya ce "Ango kasha kamshi. Ango na Fatima da Zainab. Baban Fatima, kai ne Huzaifa Baban Huzaifa. Angon Fatima kuma Baban Fatima. Huzaifa ya kyalkyale da dariya ya ce "Najib a ina ka iya kirari haka kamar wani maroki? To na nadaka sarkin maroka a wajen daurin auren nan. Suka kwashe da dariya su duka dakin har da Suhaif. Huzaifa ya mikawa Muslim hannu suka gaisa, sannan ya mikawa Suhaif hannu. Gaban Suhaif sai da ya yanke ya fadi da yaga Huzaifa. Babu abinda Suhaif ya keji yau sai faduwar gaba da tashin hankali. Yasa hannu ya rike bangaren kirjinsa na hagu inda zuciya take. Shi kadai sai Ubangijinsa yasan halin da yake ciki a safiyar yau.
Hamma Huzaifa ya zazzage kayan cikin ledar akan gado. Sai ga wasu dandatsa-dandatsan shaddoji farare sol a dinke set uku iri daya. Riga da wando da babbar riga sunsha dinkin surfani da brown din zare. Hade da hular data shigo da kayan itama guda uku. Najib yana dagawa yana gwadasu yana yaba kyawun da suka yi. Hamma Huzaifa ya ce "Kaifa Suhaif sun yi maka kyau? Suhaif ya matso ya daga yayi murmushi ya ce "Kyau kai! Ai dole ma a kalle ka Ango. Amma yaya har guda uku iri daya? Huzaifa ya ce "Ni da kai da Najib na dinkowa saboda kuma abokan ango mu fito fes iri daya. Sai su duka suka ce "A'a bai kamata suyi anko dashi ba ai an fi so ango yafi kowa caba ado saboda ya bambanta, kowa ya ganshi yasan shine. Muslim ya na taya Huzaifa rokar su Suhaif akan su yadda suyi ankon babu komai shi daman haka yafi so. Daga karshe Suhaif suka yarda zasu saka. Huzaifa ya dauki nasa kayan ya saka a leda yayi musu sallama yace zai tafi gida sai sun hadu a wajen daurin auren kar suyi African time.
Najib ya lura da Suhai baya cikin hayyacinsa sosai, da alama akwai ciwon da yake damunsa asafiyar yau. Baya jin dadin jikinsa da asuba ma ya lura da kyar yayi salla yana yawan cije baki ya dafe kirjinsa. Abinci ma da aka kawo bai ko dandana shi ba. Najib ya dube shi ya ce "Suhaif ta shi ka fara wanka muyi mu shirya kar mu makara. Yayi minti biyar a zaune sannan ya yunkura zai tashi sai ya koma ya zauna ya kasa mikewa, da sauri Najib ya tare shi. Ya ce "Lafiya Suhaif, ko in kaika bandakin? Suhaif ya girgiza kai alamar a'a, ya tashi yana tafiya a hankali ya shiga ban daki hannunsa dai a dafe da kirjinsa. Yana shiga suka ji ya ce "Subhanallah" Najib ya shiga a guje yaga Suhaif daure da tawul yana tsugune yana rike da hannunsa. Najib ya tambaye shi "Lafiya? Suhaif ya ce famfon ruwan zafi ya bude ya manta ya tara hannunsa shine ya kone. Najib ya ce "Wai tunanin me kake yi haka har ka budewa kan ka ruwan zafi, ga hannunka nan ya sale? Haba Suhaif kayi hakuri mana ka barwa mai duka komai. Najib ya surka masa ruwan wanka, ya ce ya shiga yayi wankan. Najib ya fito daga ban dakin hankalinsa a tashe. Muslim wanda bai san abunda yake faruwa ba sai ya hau tambayar Najib "Wai me yake damun Suhaif ne? Najib ya ce "Baya jin dadin jikinsa ne.
Bayan Suhaif ya fito Muslim ya shiga wankan. Kayan ma Suhaif ya kasa sawa a dai-dai sai karkarwa hannunsa yake Najib ne yake gyara masa. Najib yana ta bawa Suhaif baki ya kwantar da hankalinsa kada ciwo ya kama shi. Budar bakin Suhaif sai ya ce "Dan Uwana Najib kayi min addu'a, yau za'a daurawa Iman aure nima kuma yau zaku yi taron jana'izata. Najib ya ji gabansa ya fadi ya zabura ya dafe kirji. Ya ce "Suhaif, haba Suhaif meye duniya? Daman nasan abunda yake damunka kenan. Ko kuma ka hakura da zuwa wajen daurin auren ka kwanta. Suhaif ya girgiza kai ya ce "Zanje, zan iya zuwa karka damu. Najib ya zauna kan kujera yayi shiru ya zurawa Suhaif ido ya rasa yadda zai taimake shi. Dame zan taimaka masa ya rage damuwa? Babu! Iman ce kawai maganin, babu Iman kuma.
Muslim ya fito daga wanka ya ce da Najib "Yayana shiga, na fito. Najib ya tashi dakyar yake tafiya saboda damuwa. Yana shiga shima ya kwalla kara. Muslim ya shiga da sauri sai ga Najib a tsugunne ya rike hannu, tunani yasa shima ya budewa hannunsa famfon ruwan zafi ya kona hannnu. Muslim ya ce "Yau lafiyarku kalau kuwa? Ya yi masa sannu ya fito ya jawo kofar ban daki ya rufe cike da tunani ya kasa gane kan Suhaif ga Najib shima yana kokarin rikicewa.
WAJEN DAURIN AURE ---- <3