← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 80

Sashe 10

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 4 min read

Ana saura kwana biyar Sallar azumi Suhaif ya dira a Kano. Ko zama baiyi ba saiga Najib shima daga Kaduna yazo Sallah suka iske Mama a falo, Mama tayi dariya ta ce "Af kamar tare kuke? Amma fa kunci sa'a da suka barku ku ka taho tun yau. Suhaif ya ce "Aini ko basu barni ba na fadawa Oganmu tahowata kawai zanyi. Ta ce "Ai gara dai da ka bari suka barka baka taho ba, ai komai yana da doka. Najib ya gaishe da Mamarsa, Suhaif ma haka. Sai suka mikawa juna hannu suka tafa. Suhaif ya ce "Kalleka dan Allah har wata uwar kiba kayi daga zuwa bautar kasa. Najib yayu murmushi ya ce to kai kuwa ai Kaduna gida ce YARENMU daya ADDININMU daya. Su duka suka kyalkyale da dariya. Mama ta ce "Wannan dai tsokanar Suhaif kake dan kasan baya son kudu. Suhaif ya ce "Kyaleshi Mama yazo Ogun yaga Musulmai, hausawa, duk yadda nake tunani ashe ba haka bane. Ramar da nayi bata komai bace Azumi ne. Najib ya ce "Ai nima ina Azumin, kai duk tsiyarka na fika jin dadin garin da nake ka ji ko, komai yawan Musulman Ogun basu kai arewa ba.
Suhaif ya dubi Mama ya ce "Baba ya fita ne? Mama ta ce "Ya tafi Umara, ai ba a Nigeria zaiyi sallah ba. Ga kudin kayan Sallarku can ya bari, ya ce idan kun zo sallan a baku idan baku zo ba a suyo a dinka muku idan ya dawo zai kai muku ziyara sai ya tafi muku dasu. *Yan Doko ma tun kafin ya tafi duk an diddinka musu an kai musu. Suhaif ya ce "Allah Sarki, Allah Ya saka da alheri. Ba dan yamma tayi ba da yanzu nan zamu kasuwa mu sayo dan mu sami dinki. Najib ya ce "Sai dai gobe muje da wuri mu suyo saimu wuce wajen mai dinki ai ko ana gobe sallah Tijjani tela zai yi mana dinki.
Suhaif ya ce "Sai dai in dawo gobe muje kasuwar amma ni yau in Allah Ya so a Doko zan sha ruwa. Mama ta ce "Dan wahala? Kaje yau ka dawo gobe ba zaka bari gobe daga kasuwa ka wuce ba? Suhaif da Najib duka suka kwashe da dariya. Suhaif yadau jakarsa ya nufi dakinsu, Najib ya dauki tasa jakar suka nufi daki. Najib na cewa "Ke dai Mama yi shiru baki san me yasa yanzu Suhaif yake son Doko ba. Sallar la'asar kawai Suhaif yayi ya dauki Jakar kayansa ya fito Najib ya rako shi. Har yanzu Mama tana falo a zaune, ta kira *yan aikin gidan tana zanawa kowacce aikin da zata kama yi na hidimar kayan shan ruwa. Suhaif ya duka ya ce "Mama na fito zan tafi sai gobe in Allah Ya kaimu zan dawo, direba na nan ko ya tashi zai mika ni tasha? Mama ta ce "Kai dai ka dage saika tafinko? Danlami direba baya nan saboda Azumi da wuri nake cewa ya tafi. Ka dauko makullin motar a dakina kan fridge ka tuka ka tafi tunda gobe zaka dawo. Daman Babanku ne baya so in dinga baku mota yafi so ku gama bautar kasa, kuna samun aiki ya rarraba muku mota. Cewa yayi yanzu kawunanku samari rawa yake amma idan kun gama bautar kasa kun fara aiki kun mallaki hankalin kanku. Suhaif ya ce "Ba komai Mama zan hau achaba inje tasha har na kai gida ba'asha ruwa ba, gobe kuma tunda Motar Kano bata wuya zan dawo. Ai mun kusa gamawa har a bamu tamu ta kanmu. Najib ya ce "Wallah Baba yayi mana yawa, wai sai mun fara aiki zai bamu mota. Me kenan? Ai a lokacin zamu iya saya ma da kanmu. Yanzu ya kamata a bamu, duk mun kode a motar haya. Aini da in zauna kwam direba na tukani gara in tari achaba in hau, shi yasa ma bana shiga motocin gidan nan. Mama ta ce "Ka santa kuma. Ni dai na yi iya kokarina Babanku ya ki yarda ya saya muku yanzu.
Suhaif da Najib suka fita zuwa bakin titi. Ana kiran Sallar Magruba Suhaif yayi sallama a gidansu Doko. Gaba dayansu suna tsakar gida kowa yana kacaniyar buda baki. Sallamarsa ce ta ja hankalin kowa yana duban mai shigowa. Duk da sun so su dauki muryar. Baba yayi alwala ya dauki carbinsa zaije masallaci, Iman tana alwala a wajen rijiya, Zubaida tana tace zobo, Gwaggo ta gama suyar kosai tana rabawa, Naja'atu kuma tana zaune tana shan kunun tsamiya. Sai gaba suka hau cewa sannu da zuwa yau kaine a gari?

Na ji dadin Addu'o'in ku gareni sosai Allah Ya bar zumunci na gode.

Sai kuma wata shawara, dan Allah kada a ce wani abu, da yawa daga cikin masu rubuta sunan Allah anan page ba sa son farawa da babban baki dan Allah a gyara saboda sunan Allah ba abin wasa ba ne. Na gode

Na ku angon Iman jini da hanta..... Lolx
Reedwan Suraj Isma'il

>>>>>>>>>>> YARENA ADDININA
____CI GABAN LABARIN
Chapter 10 · 0% Book details