← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 80

Sashe 38

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah Ya tsaremu daga shiga kuncin rayuwa, wadan da suke ciki Allah Ya fitar da su da girman zatinSa da ikonSa. Ameen.

Reedwan Suraj Isma'il

*************** YAREANA ADDININA
___CIGABAN LABARI

Na isa gidanmu da misalin karfe tara na dare, ina shiga na dora hannu aka na kurma kukan mutuwa a falonmu. Mama Tabita da Mahaifiyata suna kicin suka fito da gudu, Mahaifina da ya tafi nemana asibitoci kala-kala sai yanzu ya dawo a gajiye. Suka taru akaina suna tambayata lafiya? Cikin kuka na shaida musu Jaririna ya mutu an binne shi a asibiti. Daga dukkan alamu sun tausaya min su duka, suna bani baki inyi hakuri dama sun gaya min ya mutu na dauki gawa na kai asibiti. Ban daina kuka ba kamar zuga ni ma suke yi. Dole Mahaifiyata ta zaunar dani ta zuba min abinci da ruwa ta ce sai naci. Ci nake amma ban san dandanon abincin ba tamkar dusa nake cusawa ba abinci ba.
Ranar Mahaifiyata ta nutsu ta tsaya tayi min nasiha a tsanake yadda rayuwa take, ta ce kada in kuskura in sake bari rayuwa ta subuce min in shiga halin kakanikayi da nadama. Amma daga karshe ta fara cusa min addininta da aurena da Micheal. In da na dauke hankali daga sauraron abunda take cewa dan ba zai yuba. Sai a lokacin Mahaifina ya sa baki ya ce "Tunda danta ya mutu ai kuwa babu zancan auranta da Micheal, babu mai yiwa *yar sa aure tana da shekaru goma sha biyar. Sabon Adimission zai samar min in fara karatu. Ita kuwa Mahaifiyata bata yadda ba wai dole in auri Micheal sai inyi karatu a gidansa. Nan fa ta mike ta fara zuba masifa da yare kala-kala, duk hakurin Mahaifina bai cike biye mata ba idan tana fada irin wannan, amma yau ya biye mata har ma ya fita bugun kirji da jajircewa yana nan akan bakarsa babu mai yiwa *yarsa aure karatu zata yi. Kamar zasu tsagamin kunne saboda daga murya. Na tashi dakyar saboda tsananin ciwan kai da damuwar dake damuna, na shiga dakina na zube kan katifa sharaf. Tunda na kwanta ban sake farkawa ba haka ban sake jin ko kalma daya ba ta maganganun da suke don haka nake tunanin ba barci nayi ba sai dai idan suma nayi, domin yafi barci nauyi. Ban farka ba sai sanda agogon dakina ya buga karfe ukun dare daidai. Nayi karfin hali zan tashi zaune sai na koma yaraf na kwanta. A lokacin wani barci mai nauyi ya daukeni na dora da wani mafarki wanda ban taba yin irinsa ba. Mafarki nayi na ganni a wani gari, mutanen garin gaba dayansu suna sanye da hijabai a jikinsu. Sahun sallah sahu-sahu anata sallah, wasu kuma suna karatun kur'ani. Ina tsaye ina kallonsu, a mafarkin sai wata mata ta saka min hijab ta ce "Fatima shigo cikinmu muyi sallah, mu karanta littafi mai tsarki sai muyi addu'a Allah Ya yaye miki bakin cikin dake damun ki. Sai na ganni tare dasu muna salla, ban iya karatun kur'ani ba sai karatun salla kadai, amma a mafarkin na ganni ina karatun kur'ani babu gargada manyan surori nake ja. Dai-dai nan na farka daga barci, a lokacin ana kiran sallar asuba. Na bude ido na tabbatar mafarki nake, nayi farat na tashi zaune naji jikina yayi karfi. Na daina ciwan kai, zuciyata tayi fari tas. Na tsinci kaina ina farin ciki, babu abinda ya lullube min zuciya sai in tashi in tafi neman wannan gari da ake addinin Musulunci, in nemo ilimi in tsayar da Sallah da azumi.
Na yankewa kaina hukuncin gara in raba rigima tsakanin uwata da ubana in bar garin, tunda haka rayuwata ta kasance, bani da sha'awar karatu a rayuwata ba zan iya ba, ganin yadda ta kasance daga zuwana Jami'a, kawayena sun rasa rayuwarsu, nima kuma na fada hatsari da masifa kala-kala. A sanadiyyar karatu aka samu yaron da bai san komai ba ya zo ya fada maraici da rashin gata ga rashin asali. Na fada a baiyane bazan auri Micheal ba, bazan tafi jami'a ba. Ba aure, ba karatu, dole ba zaman gidanmu. Kuma idan na zauna a gidanmu bani babu addinin Musulunci. Zuciyata ta ce min "Tashi maza-maza shirya ki gudu ki bi hanya madaidaiciya. Nayi wuf na mike daga kan shimfidata na nufi bandaki da sauri na dauro alwala na rufe kofar dakina, na gyara labulayen wundo, na kashe fitilar dakin kada wani ya zo ya riske ni ina salla. Na dinga jero sallolin da banyi ba jiya na ramasu kakaf, na idar nayi addu'a sosai akan Allah Yasa karshen damuwata ce tazo barina gaban Iyayena. Na shiga bandaki nayi wanka na wanke bakina da brush, na hada sosona da brush dina a leda na daure na fito da su. Na dauko jakar zuba kayana na saka a ciki. Na zabi kaya kala uku atamfofi na zuba a jakar. Sannan na saka wani leshi pink sai dai matsalar bani da gyale babba bare hijab da zan saka in saje da Musulmai a garin Musulunci. Salla ma dakyar na harhada kananan Mayafaina nayi. Babu komai idan naje can zan samu in siya insa.
Af na manta, nan fa matsalar take da na tuna bani da kudin motar barin garin. Amma sai na tuna akwai wata tsohuwar sarkata ta gwal da ta tsinke tuntuni dan kunne daya ya fadi, Mahaifiyata ta ce in ajiye zata karba ta canzo min wata. Na lalubota cikin akwatina da warin dan kunnanta, na saka a jakar kayan tafiya. Na dauko biro da takarda guda biyu na zauna na fara rubuta wasiku, daya ta Maman daya kuma zuwa ga Babana. Na basu hakuri kuma na nemi gafarar su yafe min. Na shaidawa Mahaifiyata tayi hakuri ni Musulma ce bana bin addininta yanzu haka na tafi neman ilimin addinin Musulunci. Na bata labarin rayuwata da su Harriet da yadda aka yi na samu jaririn, amma ban fada mata jaririn bai mutu ba, nace idan Micheal ya zo su fada masa jaririnsa ya mutu. Na shaidawa Mahaifina yayi kuskure babba da ya bar addininsa na Musulunci addini gaskiya. Don haka bazan iya zama da su ba, na tafi wajen *yan uwana Musulmu. Na rokesu da kada su damu kansu su wahalar da kansu su bazama nemana, baza su iya gano inda nake ba don taka maimai nima kaina bansan garin da zan nufa ba, mai yiwuwa ma in bar kasar gaba daya. Bazan fada hannun halaka ba ko mugaye, ko karuwanci tunda Allah Yasan zuciyata da izininsa zai kareni. Na ce su kara hakuri da rashina nima ina cikin tsananin bakin ciki da takaicin rabuwa da su, da kuma kannene dole ce tasa zan tafi don ba yadda zanyi. Ina gama rubuta wasikun sai kuka ya kece min. Na jera wasikun akan katifata a bude yadda suna shigowa zasu gani. Jikina yana karkarwa na yafa dan karamin gyale na rufe jakar kayana na rataya na fito gami da tura kofar dakin na rufe kamar ina ciki na fara sanda don kar suji karar bude kofar falon, na fice na mayar da kofar falon na rufe.
Misalin karfe shida na safe ne don haka garin bai gama wayewa ba. Mai gadinmu mijin Mama Tabita bai fito wajen gadi ba yana gidansa shima. Na iske get din a datse da kwado, gashi ban san inda ake ajiye mukullin ba, amma wannan ba matsalata bace duk girman bishiya da tsawon get zan haura, saboda tun ina yarinya ni da kawayena Mumuyawa mun saba hawan bishiyoyi kala-kala. Ina jefa jakata waje, sai na nade siket dina na kama get na haura. Na dauki jakata na kara gaba. Kicibus nayi da Mahaifin Hamma Huzaifa ya dawo daga Masallaci. Nan da nan na kawar da fuskata gefe na rufe da gyale don kada ya gane ni, amma yaso ya gane ni sai kallona yake har da waiwaye cike da mamaki. Na san dalilin da yasa bai tsayar dani ba, yasan babu yadda za'ayi in ce ban tsuguna na gaisheshi ba. Na wuce shi da sauri dan kada ya tona min asiri.
Ina isa bakin titi na tsayar da achaba na haye, yana tambayata ina zan kaiki nace muje kawai. A hanya nake shaida masa wuraren zuwan nawa da yawa. Na farko ina so ya kaini duk inda yasan ana sayan gwal zan sayar, sai kuma ya wuce dani tashar da zan tafi wani gari. Yayi murmushi ya ce "Akwai wata Hajiya tana zuwa Saudia tana sana'ar gwal zai kaini yasan zata siya, sannan wanne gari zanje dan yasan tashar da zai kaini? Nayi shiru can na ce "Garin da kasan suna Addinin Musulunci. Ya tuntsire da dariya ya ce "Lallai yarinya nan baki ma san wanne gari zaki ba, ko dai guduwa zaki yi daga gidan Iyayenki, ko gidan mijinki? Nayi caraf na ce "Na yi maka kama da mai guduwa ne? Kawai tambayarka nayi don inji yadda nake zato din gaskiya ne. Shine garin da yafi kowanne gari Musulmai. Ya nisa ya ce "Wanne gari kika dauka yafi kowanne musulmi? Na ce "Kogi state. Dan acaba ya ce "Inah ai yarinya baki canka ba Kano yafi Musulmai. KANO TA DABO TUMBIN GIWA KO DAME KAZO AN FIKA. Na maimata "Kano? Ya ce "Kwarai akwai Malamai, a kwai Makaranta addini, ga masu arziki da suke taimakawa addini da dukiyoyinsu. Ke duk *yan garin Musulmai ne sai dai bakin da suke zuwa zaka samesu da wani addini. Nayi wuf na ce "Ashe nayi gaskiya nima Kanon na nufa sai na bugi cikinka na tambayeka. Ni da shi duka muka tuntsire da dariya.
Chapter 38 · 0% Book details