← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 80

Sashe 64

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya suke babu ji, babu gani taki ta kare. Sunyi sallar azahar a hanya, haka la'asar ma, suna yi suna tsayawa suci abinci, sannan suci gaba da tafiya. Basu jigata sosai ba, kasancewar motocin lafiyayyu ne masu sanyin A.C, ga lausasan kujeru kamar akan gadonka kake. Kasancewar Huzaifa ya basu kwatance a rubuce basu sha wuya ba, suna shigowa Jalingo sai suka yi tambaya ba tare da bata lokaci ba aka samu wanda yayi musu jagora har kofar gidan su Iman. Iman da Mahaifiyarta suna zaune a daki. Falon gidan da sauran dakunan da farafajiyar gidan duk mata ne suke ta aikin abinci. Dangin Mahaifin Iman ne jingim, suka taho mota-mota daga Gombe cikinsu har da Kakarta wacce ta haifi Babanta, sauran kuma *yan uwan Mahaifiyar Iman ne da kawayenta, da makwabta suka taru ana ta soye-soye da dafe-dafe saboda masu zuwa daurin auren gobe. Wata yarinya ce karama ta shigo har dakin da Iman take ta sanar mata ta zo waje ana kiranta, tayi baki daga Kano. Tana jin kalmar Kano ko tantama babu tasan su Suhaif ne, don haka tayi zumbur ta tashi da murna ta bude labulen windo ta leka. Ta juyo ta dubi Mahaifiyarta da fara'a cikin harshen turanci ta ce "Mummy da gaske su din ne kuwa. Mahaifiyarta tayi dariya ta ce "To jeki maza ki tare su, gidan nan ba zai shigu ba ki kaisu can gidan da aka gyara na saukar baki. Ni kuma zansa a hada musu abinci a kai, sai nima in zo mu gaisa. Iman ta ja mayafinta ta fito da murna ta nufi wajen motocin su Suhaif.
Kafin ta karasa ta hango Hamma Huzaifa har ya gansu yaje wajensu suna gaisawa. Iman ta nufo inda suke, ido mai kalle-kalle, idon Suhaif ya hango masa Iman ta tunkarosu. Ya ji gabansa ya yanke ya fadi, sai yake kokarin dimaucewa. Duk wanda ke wajen zai iya gane halin da Suhaif ya shiga yanzun nan. Ba Suhaif kadai ba duk wanda ya ga amarya Iman sai ya sake kallonta, wato kyau ta kara yi kamar yau aka cirota daga leda, ta sha kunshin bakar fulawa a fararen kafafuwanta da hannayenta, ga wasu siraran kitso anyi mata yisin-yisin kai ka ce ba da hannu aka yi su ba. Da yake yau mayafi ta yafo, kuma atamfa ta saka super anyi mata dinkin riga da siket. Tana zuwa sai ta je wajen su Baba ta zube har kasa ta gaishe su. Cikin fara'a suka amsa gami da sanya mata albarka a cikin auranta. Ta wuce wurin su Goggo ta durkusa nan ma ta gaishesu. Goggo ta kamo hannunta ta ce "Taho nan Iman *yata mu gaisa sosai, gaisuwar yaushe gamo. Sai Iman ta fara hawaye Goggo ma tana nata. Iman ta karasa wajen su Naja'at ta karbi Hauwa a hannun Zubaida suma tana fara'a tayi musu sannu da zuwa. Huzaifa ya mikawa Iman makulli ya ce "Jeki ki bude musu can gidan su shiga su huta sun sha hanya. Suhaif ya ce da Huzaifa "Su Baba sunce a nuna musu Hotel baza su iya zama anan ba, mata sun yi yawa. Huzaifa ya ce "Ah! Daman matan ne kawai anan mun riga mun kama dakuna a Hotels. Bari su gaisa da Babana da Baban Iman suna falon gidanmu, mu je in kaisu. Huzaifa na gaba, Baba na Doko, Baba na Kano, Suhaif Najib da Muslim suna biye dashi a baya har falon da Mahaifin Huzaifa da Iman suke a zaune a gidan su Huzaifa.
Iman da su Goggo tuni sun shiga gidan saukar bakin, shima kusa ne a tsakanin gidan su Iman da Huzaifa yake. Shima gidan irin gidajensu ne na gwamnati. An share shi an shimfida sabon rog carpet da sababbin katifu, filillika da sababbin zannuwan gadaje. Bandakuna kuwa sababbin bokitaine da butoci. Babu abunda su Goggo suka fara yi sai sallar magaruba da isha'i, daga nan sai suka dinga shiga wanka. Bayan nan sai suka hallara a falo suka fara cin abincin da aka jera musu kala-kala. *Yan Uwan Huzaifa da *Yan Uwan Iman suna ta shigowa suna gaishe su. Da yawa daga cikinsu ko Hausa basa ji sai fulatanci. Iman tana zaune tana fassara, tana kuma gabatar da su. Suna ganin kanwarta Hajara (Rabecca) kafin ta gabatar da ita Zubaida ta ce "Amma wannan kanwarki ce ko? Don kuna kama. Haka Mahaifiyar Iman tana shigowa su Goggo suka ganeta. Ta zo ta zauna bayan sun gaisa sai ta shiga yi musu godiya, ta ce Iman ta fada mata duk abun arzikin da suka yi mata, don haka sun zama *yan uwa. Duk da ba Hausa sosai take ji ba. Su Goggo suka ce babu komai. Zuciyarsu cike da tambaya ai Mahaifiyar Iman ba Musulma ba ce a labarin da ta basu. Yaya suka ganta da hijab har kasa tana kiran Allah da Annabi?
Suhaif, Huzaifa, Najib da Muslim ne suka shigo. Goggo ta ce "Ina kuka shiga ne? Ga abinci fa jifgi ku zo ku ci ku kaiwa su Babanku suma. Huzaifa ya yi sauri ya ce, "Ai su har an kaisu masaukinsu a Hotel sun kwanta, sun ci abinci tare da su Babanmu. Su kuma su Suhaif mun ci tare, sannan suma sun je masaukinsu sunyi wanka sun ajiye kayansu. Yanzu ma zuwa muka yi su gaishe da Mummy (Maman Iman). Su Suhaif suka durkusa suka gaisheta cikin harshen turanci, tayi ta godiya da shi albarka. Mama, Goggo, Zubaida da Naja'at babu wanda bai kawo wa Iman gudunmawa ba. Suka firfito da gudunmawarsu suka jifge a gaban Iman da Mahaifiyarta sai godiya suke. Daga karshe Mahaifiyar Iman tayi musu sallama, ta ce zata aiko yara su zo su kwashe kayan, ta fita Mahaifiyar Huzaifa da kannensa ne suka shigo, suma aka gaggaisa suna godiya suma. Bayan sun tashi sun fita sai Zubaida ta taba cinyar Iman ta ce "Iman bayan kin bar Doko meya faru? Na ga Mahaifiyarki da hijab, ta Musulunta ne? Najib ya ce "Wannan Zubaidar akwai shegen surutu da tambaya. Mama ta ce "Zubaida ta baci da magana na rasa dalili, gashi ke ba bangaren jarida kika karanta ba. Naja'at ta ce "Kun manta mijinta Muslim dan jarida ne? Sai su duka suka kyalkyale da dariya. Goggo ta ce "A'a ku bar su kawaye ne fa, suyi hirarsu. Ba tare ku ka gansu ba? Gida daya, daki daya, ajinsu ma daya a Doko.
Iman ta ce "Lah ai ba laifi bane dan ta tambayeni, idan ma babu wanda ya tambayeni a cikinku sai in ce baku damu dani ba. Ranar da na bar Doko a motar *yan sanda, tashar unguwa uku suka kaini, suka saka ni a zungureriyar mota mai zuwa Jalingo. Suka bani kudin motata a hannuna, nayi musu godiya suka tafi. Ina ganin sun fita daga tashar na fito daga motar na tari tasi sai gidan Mummy Naila dan in ga Abdul-Malik kuma in mata sallama nasan idan na bar Kano na bari kenan. Da na je sai tayi matukar mamakin ganina ita da sauran ma'aikatan gidan da suka sanni da. Abdul-Malik ya warke ras har ya girma yayi wayo abinsa. Kamar zai gane ni sai kallona yake tayi ba kiftawa. Mummy Naila ta hau tambayata ina na tafi ne? Kuma meyasa na tafi? Kamar wata jahila zan hada kaya in bar gidan, in ce bana son ganin Abdul-Malik cikin wannan halin. Ina ruwan Allah, Zai iya yanke HukuncinSa akan bawansa yadda yaso. Na kasa amsa mata wadannan tambayoyi sai hawaye nake na rungume Abdul-Malik. Ta sa aka kawo min abinci na ci, sai ta ce in shiga dakina in yi wanka in shirya, taga alamar a gajiye nake. Na shiga dakina na bude dirowata, abun mamaki kayana suna nan babu wanda ya taba, an hada min su a waje daya. Bayan nayi wanka na zabi bakar doguwar riga a cikin kayana na saka. Sannna na dinga jero sallolin da ake bina. Abdul-Malik ne yake bude kofar dakin da nake yana lekowa, ya kalleni sai ya koma da gudu. Mummy Naila ta leko da kanta ta ce in fito falo idan na gama muyi kallo da hira. Na fito muka zauna a falo taci gaba da tambayata. Babu fa'idar in boye mata komai, duk da ba komai ba ne zai iya faduwa. Na gyara zama na fara neman gafararta, kuma na bata hakuri saboda zata ji labari sabanin na farko dana bata. Na zaiyano mata makasudin barina garinmu, saboda in zo in rungumi addinin Musulunci ne nabar gidanmu, kasancewar Mahaifiyata ba Musulma ba ce kuma ta rinjayi Mahaifina shima ya bita ya bar Musulunci. Na fada mata dalilin da yasa na bar gidanta kuma don kawai ina jin tausayin Abdul-Malik na matsanancin halin da yake ciki na rashin lafiya abun yake ta damuna, saboda ina son Abdul-Malik. Sai na bata labarin rayuwata a Doko, na ce na kara samo ilimi. Yanzu kuma nabar Doko zan koma garinmu Jalingo in je in sami Iyayena in yi amfani da iya ilimim dana samo in musu nasiha, in wa'azantar, in kuma tunasar dasu su rungumi addinina. Duk wannan bayanin da nayi mata babu in da na sako zancen Matsafan da suka addabeni, domin zaiyi wuya ta fahimceni. Ita ba *yar Nigeria ba ce, wata kila ma basu taba jin labarin tsafi ba, ko kuma irin wanda suka sani ba irin namu ba ne.
Chapter 64 · 0% Book details