← Book details Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 80

Sashe 53

Yarena Addinina Part Complete Hausa Novel · about 5 min read

yi, son da take yi min bata hakura ba? Malam Dauda ya katse masa tunanin da ya ke, ya ce "Ranka ya dade a shigar da jakar nan ciki? Suhaif ya yi ajiyar zuciya ya ce "Ka kai ciki ka ce musu zan je in gaishe da Hajja Kakata zan dawo yanzu. Malam Dauda ya amsa ya nufi cikin gida. Abokan Suhaif, *yan uwa da yaran unguwa suka zo suka kewaye shi suna kwasar gaisuwa gami da taya shi murnar sayen wannan dalleliyar mota. Sun cika da mamakin ganin yadda Suhaif ya zama gagarumin mai arziki a shekara guda, tare da sha'awar dama sune Suhaif ganin yadda yayi kyau yana kyalli shi da kayan jikinsa. Suhaif baya kyamarsu, baya daga musu kai ko dan saboda yayi kudi, kamar yadda suke da, haka suke hira suna musabaha. Ko wannensu da irin nasa kokekoken da suke kawowa Suhaif. Wannan ya ce matarsa ta haihu bashi da ragon suna. wancan ya ce gidansa ya burma, katanga ta dare. Wadansu basu da na cefanu ga iyali ga yara kanana. Suhaif ya amsa musu da cewa da izinin Allah zai taimaka, amma ba yanzu ba su dawo gobe tunda yana gari har kwanaki uku. Da yawa suka shige motarsa wai zasu rakashi inda zaije. Suka dunguma suka nufi gidan Hajja. "Oh *yar Hajja ke har yanzu babu ci gaba a tattare dake balle ki waye kina nan jiya iyau. Suhaif ya fada tun kafin ya fito daga mota. Ya na fitowa daga cikin motarsa ita kuma tana kofar gida tana suyar wainar fulawa ta sayarwa. *yar Hajja ta bude baki tana kallon motar da mai motar dan bata gane shi ba har yanzu. Ta zabura ta tashi da sauri ta ce "Lah Babangida kaine? Haka ka zama? Ba'sabanba, kudi kayi? Suhaif ya tuntsire da dariya ya ce "Ni fa nasan kullum a rana sai kin ambaci kudi yafi sau dari saboda tsabar son kudinki. Ta zura cikin gida da gudu ta shaidawa Kakarta cewar ga Babangida ya zo. Suka yo waje su duka, Hajja tayi murna da ganin jikanta har da kukan dadi. Suhaif ya jawo hannun Kakarsa suka shiga gida. *yar Hajja kuwa jikinta na rawa taje ta kashe wutar wainar, tasa yara suka tayata ta shigo da kayan cikin gida. Ta fasa wainar tunda taga Babangida dole zai bata kudi, ko bai bata ba zata warta. Bayan sun gaggaisa, Hajja tayi masa fada bai kamata ba ya tafi Lagos ya shekara guda cur bai zo gida ba ganin Iyayensa da *ya uwansa, musamman ita tsohuwa wacce ake saka mata ran mutuwa yau ko gobe. Ta bashi shawara ya rage fushi da zuciya da zafin rai irin nasa, ya yi hakuri da rayuwar duniya. An bani labarin duk yadda akayi Babanka ya koreka, amma tunda Baban naka yayi nadama yaje har Lagos din ya ce ka zo gida ai sai ka zo. Anan Mahaifiyarka take zuwa ta zauna, ita kuka ni kuka tana cewa ita Lagos din zata bika idan shekara ta cika baka zo ba. Suhaif ya amsa laifinsa kuma yayi mata alkawarin zai yi amfani da shawarar da ta bashi. Albishir na farko daya fara fadawa Hajja shine ta shirya da ita da *yar Hajja da su za'ayi aikin HAJJI bana in Allah Ya so. Kuma idan *yar Hajja ta sami miji ayi masa magana ko tsinke kada wani ya saya shi zaiyi komai na aure. Sannan kafin su dawo daga Hajji zai sa a rushe wannan gidan nata na kasa a mayar da shi na siminti. *yar Hajja ta daka tsalle ta dira tana murna, Hajja kuwa sai ta rushe da kuka tana godiya. Nan dai Suhaif ya fito ya barsu sun rikice kamar zasu suma don murna. Da kyar ya samu ya lallashi dinbin jama'ar da suke jiransa a kofar gida sun kewaye motarsa, ya basu hakuri akan yanzu ya shigo garin amma su sameshi da daddare a gida. Ya shigo mota ya nufi gidansu. Ya iske babu motar Zubaida a kofar gidan, babu Malam Dauda da alamar sun tafi. Ya yi sallama ya shiga gidansu ya iske Mahaifiyarsu a tsaye a tsakar gida ta yafa gyale. Mahaifinsa kuwa a zaune akan kujera. Suhaif ya tambaya "Goggo unguwa zaki je ne? Ta harareshi ta ce "Unguwa wacce iri? Ance mun ka zo tun dazu ka aiko da jakarka ban ganka ba, na leka kofar gida aka ce mun ka sake shiga mota ka tafi, shine zan fita in tambaya ina aka ga ka nufa. Babangida meyasa kake yin haka ne? Ka shekara cur ban ganka ba, sannan ka zo garin amma ka sake tafiyarka. Suhaif ya ce "Malam Dauda bai fada muku ba? Na ce ya ce muku na tafi gaishe da Hajja. Mahaifin Suhaif ya ce "Kin gani ai, na fada miki yaran yanzu basu damu da Iyayensu ba. Iyayen ne suka fi damuwa da su. Goggo ta ce "A'a Babangida ba haka yake ba, bacin rai ne yasa shi yin hakan amma da haka kawai ne ba zai shekara bai zo gida ba. Suhaif ya karkade kujera ya zauna yana sauraronsu. Bayan Goggo ta sami waje ta zauna Suhaif ya durkusa ya gaishesu. Suma abu na farko da suka fara masa fadan shine danme ya shekara bai zo gida ba. Suhaif ya basu hakuri, yasan ya yi kuskure su yafe masa.
Chapter 53 · 0% Book details