← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 225

Sashe 98

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

koda ya dawo daga masallacin be gntaba, ya nufa bedroom dinsa ya kwanta yana juyi, a ranshi yana kissima irin cin ubantan dazeyi ta yadda da knta zatace ma Amihh batason zama da shi, karshe Amihh tace ya saketa shima ya huta, wannan shawarar da zuciarsa ta basa tayi masa ddh , se kulla irin muguntar dazetayi mata kawai yakeyi a ranshi da hk bacci me nauyi ya daukesa sbda jia be rintsaba.

7:pm Amihh ta bar gidan, taso ta biya side din Ab'ilal taga Hilwah se taga yayi sassafe da yawa, hk ta fice a gidan zuciarta fal tunanin ko a wani hali hilwah take, jiya ma bata rintsaba sbda barinta datayi tana kuka, tsakar dare taji kmr taje ta dawo da ita side dinta sede ta daurewa ranta kawai, amma badan taso ba, ita knta tasan AB'ILAL ze whlr da yarinyarnan, amma bazata barshi ba hkn tama knta alqawari.

11:am salwah ta shirya zuwa scul kasancewawr tana da lecture 11:30am, fitowa tayi harabar gidan ta nufa side din AB'ILAL domin taga hilwah harga ALLAH bata iya barin gidan inhar bata ganta ba sbda kewarta bata wani rintsa ba sosai. Taba handle din falon tayi tajita a bude tinda ya dawo daga sallarh asubahihi ya mnta be rufe kofar ba, Turowa tayi ta shigo salaf salaf kmr munafuka, ta maida kofar falon ta rufe, ta shiga karewa falon kallo, bataga kowa hkn ya bata tabbacin duk suna bedroom dinsu, direct hnyar bedroom din hilwah ta nufa tana me adduarh Allah yasa kadasu hadu da yayah AB'ILAL. A hnkli take tafia kmr munafuka har ta isa bakin kofar bedroom din hilwah, da ita aka gyara komi a gidan shiyasa tasan bedroom din nata. Tura kofar tayi ta shigo bakinta dauke da sallahma, a kwance ta gnta a kasan dakin har zuwa ynzu bata ko motsa ba, ta takure ta kudindine a cikin hijjabin dake jikinta dagani salwah tasan sanyi takeji sbda yadda ta takure a cikin hijjabin jikinta, kuma ga sanyin AC karasawa tayi ta kashe AC dake dakin kana ta iso inda hilwah ke kwance, ta tsugunna ta ajiye hand bag din dake hannunta, ta kai hannu kan fuskarta dake a bude taji jikinta da zafi sosai, saurin dauke hannunta tayi daga jikin nata tana fadin . "innalillahi! Dea zazzabi kikeyi?'' Mgnr da tayi ya farkar da ita daga baccin whlar da takeyi daman bata da nauyin bacci sam, a hnkli ta bude kwayar idonta a kn fuskar salwah, nan da nan taji farin ciki ya rufeta, da tunaninta ta kwana a ranta. "I miss you salwah...'' Itace kalmar data fito daga bakinta cikin karfin hali. Nan take tausanta ya mamaye zuciar salwah tace "I miss you 2 me rabin suna ..zazzabi ne ke damunki kou?'' Salwah ta karashe mgnr hadi da kai hannu kn fuskarta ta kara tabawa taji zafi rau rau fiye da fari ma data tabatan, janye hannunta ta karayi zucia fal tausanta tace "knsha mgni?'' Hilwah ta girgiza mata kai, Salwah tace "Ai kamar ma bakiyi breakfast ba kou ?" Hilwah ta daga mata kai kawai cikin dakiya. Salwah ta zuba mata ido, se ynzu ta ankare fuskarta a kumbure take kuma tayi ja, seta dan firgita ita ga zatonta ko yah AB'ILAL ne ya mata wani abu. "Fuskarki ta kumbura why?'' Salwah ta tambayi hilwah. "Bkm..." Shine abinda ya fito daga bakin Hilwah. Salwah tace "Ba wani, ko de Yayah ab'ilal ya miki wani abu ne plx ki gayamin bazan gayawa kowa ba..." Hilwah ta girgiza mata kai, tana murmushin karfin hali. "Bakison zaman nan side din kou?'' Salwah ta kara tambayar hilwah zucia babu ddh. Shiru Hilwah tayi a wannan karan bata bata amsaba. Salwah taci gaba da mgna "Zan gayawa Amihh kawai ki dawo side dinmu Kou?'' Hilwah ta girgiza mata kai, salwah tace "Why? A nan waze rinka dafa miki abinci, kuma in baki lafia waze baki mgni?'' Hilwah ta nunawa salwah knta da hannu ba tare data ce komi ba, salwah tayi narai narai da kwayar ido, kmr zatayi kuka. Ta mike kawai ta ajiye bag dinta ta cire hijjabin dake jikinta ta fice a dakin ta nufa kiching, komi akwai a kiching din, ruwan zafi ta daura a kn gas na Lipton tasa kayan kamshi, kana ta dawo ta soya kwai guda biyu tasa kifin gwangwani, ta gama ta hado mata tea me kauri da kwan ta hada a trea ta nufa bedroom dinta, nan ta sameta inda ta batta, ajiye trea din tayi, ta karasa ta taimaka mata ta tashi tana me ganin jiri, Salwah ta kamata suka nufa toilet nan ma ta taimaka mata tayi brush , ta wanke fuskarta kna suka dawo dakin, ta tasata gaba tasha tea da kwan data soya nata kadan shima seda ta daure taci kadan, Salwah Ta bude bag dinta akwai magunguna na zazzabi hk dana ciwon ciki,, ta bawa hilwah mgnin zazzabin tasha ta koma ta kwanta a kn tamfatsetsen bed din dake dakin, salwah ta lullubeta, hilwah ta bita da ido, ta dauki trea din ta fice dashi zuwa kiching din duk abinda takeyi a hnkli takeyi inside kuma se adduarh takeyi Allah sa kada yah AB'ILAL ya fito ya gnta ita ko ganinsa tayi firgitata yakeyi. Bayan ta gama wanke kwanonin data bata ta ajiyesu a ma'ajinsu ta dawo dakin, har lokacin hilwah idonta biyu. Karasawa Salwah tayi ta taba jikinta taji zazzabin nata ma ya fara sauka. "Sannu love, zan kira Amihh in gaya mata baki lafia.. " hilwah ta girgiza mata kai alamar ah'a. Salwah ta turo baki tace "sena gaya din, maybe in ita tazo ki gaya mata daliln kumburin fuskarki inma yah AB'ILAL ne ya miki wani abun, zata masa mgna.." Hilwah tace "ah'a plx karki gaya mata..." Salwah tace "to sekin gayamin meyasa fuskarki da idanuwanki suka kumbura ko knyi kuka ne?'' Hilwah ta daga mata kai alamar Eh. Salwah tace "to meyasaki kuka? Yah AB'ILAL ne ya dakeki kou?'' Hilwah tayi saurin girgiza mata kai kana tace "kewarku ce tasani kuka..." Ta fadi da muryarta me ddh, da sarkaqiyya, 'karyayyen harshenta na nan har ynzu. Zucia cike da tausai Salwah tace "to zan gayawa Amihh ki dawo side dinmu, nima nyi missn dinki jiya bnyi bacci me ddh ba...plx dea karki fita falo, sbda karku hadu da yah AB'ILAL knji, kiyi zamanki bedroom enki plx?' Hilwah ta daga mata kai kawai zucia fall kaunar salwah. Taci gaba da mgna "Kiyi zamanki a nan bedroom plx yah AB'ILAL Matsifa gareshi, kuma bnso ya miki, inkika zauna a bedroom dinki knga baze gnki ba balle ya miki matsifa har zuwa ki dawo side din Amihh muci gaba da zamanmu Kou?'' Hilwah ta daga mata kai alamar Eh, karasawa tayi ta manna mata deep deep kiss a goshi ta mata sallahma tasa hijjabinta ta dauki hand bag dinta ta nufa kofar fita hilwah Tace mata ''thank you darling..." Salwah ta juyo ta sakar mata Murmushi tace "Kinfi hkn...bye tace care of ur safe, kiyi bacci plx..." Hilwah ta daga mata Kai Alamar to, tana gani Salwah ta fice a dakin, ta batta da kewarta ta, rintse kwayar idonta tayi tanajin zuciarta na beating da karfi da karfi tabbas tasan tana cikin jarabawar ubangijinta Alhamdulillahi! Shine abinda ya fito daga bakinta, yayinda hawaye masu zafi suka shiga bin kuncinta, nan ta shiga aikin tunanin farkon rayuwarta har zuwa ynzu, datake kwance bisa kn gadon, a fari tasan dadin dunia babu wanda bataji ba, amma sam dadin be jima ba ta fara tsintar knta a jarabawa, ta shiga hadarirrika da dama kuma ta haye tana fatan taci gaba da hayewa dunia da kiyamarta, da wannan tunani tunanin bacci me karfi ya dauketa a wannan karon bacci me ddh takeyi zucia cike da jin dadin karamcin salwah da Amihh gareta, tana jinsu a rayuwarta kmr jini da hantarta.
Chapter 98 · 0% Book details