← Book details Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 225

Sashe 75

Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Da daddare bayan sunci abincin dare, amihh ce tayi feeding hilwah harta koshi...dukkaninsu zuciyoyi babu dadih, Salwah kanta ma ke mata ciwoh tasha mgni Amma yaki sauka, Hilwah kam komi na rayuwarta ciwoh yake mata, ji takeyi tamkar zata kamu ne da ciwon zucia. Baysn sun gama, Suka nufa bedroom din salwah , sukabar Amihh a falon, tanata tunani tunani. suna shiga dakin suka kwanta Amma duk cikinsu babu mejin bacci Amihh tazo ta musu adduarh ta musu seda safe kana ta nufa nata bedroom din, zucia babu dadih se tunani takeyi a kan a wani hali AB'ILAL yake ciki, da ace lafia lafia ce tasan da dashi zasu ci abincin daren yau. Koda ta shiga bedroom dinta ba bacci ta kwantaba Alwala ta dauro ta dawo ta ci gaba da nafilfili ta riga data sawa ranta Bacci be gantaba a halin ynzu,....

Koda Amihh ta fice a dakin gaxa baccin duk sukayi, kawai suna kwance ne Amma kiwannensu da abinda ke ranshi. Ita de Salwah tausan hilwah takeyi, sbda tasan waye AB'ILAL ballan tana ma dataji kalamansa shida Amihh, se salwah taji ta kara tausayama Hilwah, kwata-kwata babu ma Alamar sauki ko sassauci a lamarinsa, ita kanta salwah kalmar karuwar da yace ma hilwah ya tsaya mata a rai. A bangaren hilwah kam abubuwan sun hadun mata ne goma da ashirin, ga dmwar tunanin halin da take ciki again ga damuwar aurenta da wannan guy din, a zahirin gaskia bata bakin ciki, a farko da batasan wayeba shi ne ta damu, amma a ynzu data ganshi kuma ta gane shin din ashe abinda gangar jikinta ke tunani ne a kullum, se taji sauki ga ranta ta rasa dalilin dayasan taji hakan. Kalma daya ce ta tsaya mata a zucia itace kalmar karuwar daya kirata dashi Amma tasan ta cancanci ya kirata da hakan ne ko fiye da hakan ma, sbda ya ganta a hotel maybe shiyasa yake kiranta da karuwa, ita abinda tunaninta ya bata kenan. Karin tashin hnklinta kuma ga kasanta nata ruwa, anbaliya kawai, shi ba ruwanshi da tana cikin damuwa ko wani hali take ciki shide kullum cikin zuba yake babu kakkautawa zallar tsiyaya kawai yaketayi, jefi jefe sha'awarta ta jini na tsungularta, nanma dauriar takeyi, ba Tablet kuma babu pad duk a takure take, duk bayan wasu awanni se tayi wanka, seta canza pant, amihh ta bata sabbin panties masu kyau dozing ashirin, hadda pad ta bata Amma ba irin pad din da take sawa ba sbda tsane ruwan ni'imar dake jikinta, wannan inta sashi ze takura mata sbda na tsane jinin al'ada ne shi kuma wancan be kai wannan girma ba kuma ya fishi soft sosai, abubuwan sunma hilwah yawa ga tunanin mahaifiyarta dake maqale da ranta a kullum, again ga kewar su kankana da,Amal dake ranta, har Alhaji sunusi ma tana kewarshi, uwa uba kuma cocaine da codeine dinta da wiwi ma duk tana kewarsu tasan da tanashansu da dmwar bata mata yawaba har haka ba. Ajiyar zucia hilwah ta sauke tanajin ruwan dake zuba a kasanta yana yawaita. ''Tashi muyi sallah tinda duk mun kasa bacci...'' Cewar Salwah. Ba musu hilwah ta tashi, kusan a tare suka tashi da salwah, hilwah ta diro daga kan gadon jiki babu laka Salwah tabita da ido Harta shige toilet din. salwah bayanta kawai take kallo, harta shige toilet din, ta daga duvet din dake gefen inda hilwah ta tashi, nan taga inda ta tashi ya jige, sau biyu kenan tana gani ta rasa meyasa take ganin hakan, ta fara tunanin kode fitsari ne hilwah takeyi. "Wani irin fitsari ne dan kadan?'' Salwah ta tambayi knta, shiru tayi hadi da yin jim tanajin kunya dase ta tambayi hilwah meyasa take zuba, kuma ba jinin period ba. Tana nan zaune tanata tunanin hilwah ta fito daga toilet din daure da alwala, salwah ta mike ta nufa toilet din itama dan dauro alwalar. Hilwah ta nufa Wardrobe dan canza kayan dake jikinta, ta sauyasu zuwa wata doguwar riga mara nauyi ta dauki hijjabi zumbulele ta saja ta tada sallarh nafilar, Salwah ta fito itama tasa hijjabi tabi sahunta ta tayar da tata sallar. Duk bayan sallarmar raka'ah biyu se hilwah ta shiga toilet ta kara dauro alwala kana ta dawo taci gaba da yin sallarh duk salwah na Ankare da ita, tin tana tunanin neman lada ne harde yau ta fara tunanin akwaide abinda ke faruwa.... Da asubahi amihh tazo dan ta tashesu suyi sallarh asubahin ta taddasu suna kn dadduma ne ma suna nafilfili, juyawa tayi ta koma dakinta zucia fal farin ciki, ada kullum seta tashi Salwah danyin sallarh asubahin amma ynzu Alhamdulillahi zuwan hilwah yasa har sallarh dare sukeyi. Seda sukayi sallarh asubahi gari ya fara haske kana suka koma suka kwanta, bacci ya daukesu ba wani me ddh ba, se mafarke mafarke sukeyi a kan abinda ke zuciyoyinsu. A bangaren Amihh ma hkn ta kasance.

A bangaren Ab'ilal ma sam be rintsaba. Hk alhasan shima be rintsaba. 1:am alhasan ya bawa AB'ILAL shawarar su tashi suyi sallar nafilah, ba musu AB'ILAL ya tashi suka dauro alwala a nan falon suka tada sallarh nafilar, sunatayi hadi da adddu'ur'i har asubahi.. suka kara Alwala suka nufa masallaci dan samun sallarh asubahin a jam'i. Da aka idar basu baro masallacinba seda alfijir ya fara bayyana kana suka dawo gidan. AB'ILAL ya zube a falo, yana dan jin sassuci a zuciarsa ba kmr jiyannan ba. Alhasan ya dubeshi yace "mushiga bedroom mna.." AB'ILAL ya masa bnza. Alhasan be kara mgna ba sbda yasan ko ya kara ba tanka masa AB'ILAL din zeyi ba. Yabar falon ya nufa bedroom danya samu ya kwanta yayi bacci, yana kwancia kuwa bacci me nauyi ya kwasheshi....A bangaren AB'ILAL kam gaza baccin yayi ga damuwa na cinsa duk silar yarinyar ne, ga yunwa na kwakular cikinsa beci ba, be sha ba har ynzu. Jiyama da Alhasan ya masa tayin cin abinci saura kadan AB'ILAL din ya zagesa dole ya barshi. A zahirin gaskia sam shi yunwarma bata damesaba kmr yadda tunani da tsanar yarinyar suka hadu suka ma zuciarsa rubdugu har Amihh ma dan beda yadda zeyi ne Amma da haushin abinda ta masa yakeji. Se 8:am ya samu bacci barawo a wahalce ya daukesa, baccin yakeyi amma bayajin dadinsa kwata-kwata.
Chapter 75 · 0% Book details