Sashe 105
Yar Dangi Ce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*paid book...08136349646* 08/01/2022 脿 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 33*** Jin ta tsagaita da bugun kofar har na 20mnt yasa gogan ya Taso ya kara leqawa ta hujin jikin kofar nan ya hangota kafafuwanta a zuwa cinyoyinta a kasa hkn ya bashi tabbacin tana zaune ne ta jingina knta da murfin kofar,, tabe baki yayi daman beda burin bude mata kofar, ai bashi yace takai dare ba a side din Amihh, juyawa yayi ya nufa bedroom dinsa da system dinsa a hannunsa kashe system din yayi ya rufeta ya ajiyeta a mazauninta ya jona mata charge ya koma ya kwanta yabi lafiar gadonsa kasancewar bacci ne me nauyi a idanuwansa, ko tunanin ya bar wata halitta a waje beyi ba, kawai se juyi yakeyi a kan bed dinsa Sanyin AC na ratsasa, nan da nan bacci me ddh ya daukesa me cike da kwanciar hnkli babu wani abu me kamancecenia da dmwa a ransa, AC da AC na Aiki, suna bin jikinsa, har zuwa zuciarsa, se juyi kawai yakeyi yana baccinsa me ddh. Tinda ya kwanta baccin be ko farka ba, se wuraren 4:30am ya farka yana me ambaton sunayen ubangiji hadi da addu'ur'in tashi a bacci, yayi miqa tajin dadih ya sauke kafafuwansa kasan dakin bakinsa dauke da ayoyin ALLAH, ya mike ya kara wata miqar yana me kai dubansa ga agogon dake zaune a bedside, nan yaga abinda lokaci ke cewa, zira lallauusar slifas dinsa yayi ya nufa bakin kofar toilet ya cireshi ya saka wani me mugun kyau a bakin kofar shiga toilet din, da adduarh a bakinsa ya fada cikin toilet din, ruwa me dumi ya hada, hadi da turarukansa na wanka dade sauransu, kawai ya fad'a ruwan yayi wankansa hnkli kwance a gaggauce ya gama ya fito yayi alwala, kana ya daura bathrobe kalar milk se dan karami shima milk a hannunsa yana goge sumar knsa, ya fito dakin, a gaggauce ya karasa drower dinsa ya dauko jallabia light ash me kyau ya saka ya saka boxes dinsa guda uku kmr de yadda ya saba ya feshe jikinsa da turarensa da'iman, ya dauki counter dinsa ya zira slifas dinsa na yan hutu ya fito falon yana takun kasaita, yayi wani irin kyau kmr asa kudi a siya. Karasawa yayi ga makunnin wutar falon, ya kunna hasken duka, nan falon yayi wani fayau ya koma kmr rana, da yakke d'a hasken dake falon bame yawa bane, se ynzu ya kunna kaf glub din dake falon. kana ya nufa hanyar fita ya ya kai hannu ga key din dake jiki ya bude, ya murd'a handle din da niyar ya fice a falon, kawai yaji mutum ya fado kn lallausar kafafuwansa, ba tare daya ankare ba, binta da ido yayi jinta a kn lallausar kafafuwan nasa yasata kara gyara kwanciarta, a wulaknce yake kallonta shi fa sam Yama manta da ita wallahi makamanciyyar halittarta ma ya manta da ita a wajen, seda ya ganta a kn kafarsa ta dama ya tuna da halittarta daya bari a wajen. Tsuki yaja na tsabar takaici da bakin cikin ta fado masa kan kafafuwa, janye kafarshi yayi zucia fal matsifa da bala'i, yana janye kafarsa kanta ya fadi kasa tif a kasan tiles din sbda da karfi ya janfe kafar tasa, hkn yayi sanadiyar buguwar kunnenta har dankunnen gold dake kunnenta dayake me barima ne tsininsa ya bugi fatar bayan kunnenta har ya fashe sbda ya bula gurin ya shigeh, ai tini ta farka daga baccin da takeyi ta gigice ta d'imauce cikin fitar hayyaci ta tashi zaune tana shafa gurin sbda azabar dake ratsata, duk tabi ta dimauce se aikin zare ido takeyi kmr mahaukaciyya sabon kamu, nan ko tsabar firgici ne. "Wayyo Allah na! Momynar!'' Itace kalmar data fito daga bakinta a matukar gigice take, sbda azabar dake ratsata, abun dan kunnen ya shigata sosai, ba karamin zafi yake mata ba, Gashi daya shigan be fita ba yana nan ciki, duk tabi ta gigice dole uwarta fad'o mata rai a lokacin (kunsan in whla da dadih sukazo uwa ake kira ba?馃槀 if u know u know) Ido AB'ILAL ya zuba mata a,mgnrta yaji alamar sam hausa bata zauna a bakinta ba sosai, , tabe baki yy a zuciarshi ko alamar tausanta beji ba se binta yakeyi da kallon tsana da kiyayyah..d'ago kwayar idonta jajawur tayi ta zuba masa, tin daga kn kafafuwansa ta fara kallonsa har zuwa kn fuskarsa ganinsa kawai seda yasa mata fad'uwar gaba, saurin dauke kwayar idonta tayi a knsa tanajin zuciarta na beating da karfi, bata tabajin haushinsa da tsanarsaba a lokaci daya se yau, ji taji ta tsanesa karshen tsana. Tsanarsa ta kara yawaita a zuciarsa sbda tasan shine ya bude kofar har yajawo mata silar jin ciwon kunnenta dukda batasan cewa shi yajanye kafafuwansa ba ta fadi kasa, amma tasan wani abun ya mata ta fadi kasan, kuka takeso tayi amma ta kasa yi sbda ba hawaye, idanuwanta suka kara yin ja jawur jikinta duk ya mata nauyi tako ina ma jikin nata zafi yake mata, hadi da rad'adi. Hanyar ficewa ya nufa, hkn yasata shigowa cikin falon da rarrabi, dan ganin yana neman bi ta knta ya wuce, cikin kyama yake kallonta, harya fice ya rufe kofar falon ya kara bude kofar falon ya kalleta a wulaknce tana zaune a kasan tiles dij falon, yunkurawa takeso tayi ta tashi amma ta gaza hannunta na kn kunnenta wanda ya fara zubda jini zuwa ynzu, knta na kasa sam bata dago bama ta kalleshi. Yace "ke! Kiyi knell down kafin na dawo! Zaki gayamin ubanda yace ki bar gidannan jia ba tare da knyi aikin daya zamana mallakinki ba! Yau sena lahira ya fiki jin dadih! Zaki bambamce gidan masu mutumci da gidan karuwai yau!'' ' Yana gama fadar hakan yaja kofar ya rufe da karfi ya nufa masallaci. Dago kwayar idonta dake kasa tayi ta bishi dashi hadi da rafka uban tagumi a zuciarta tana jinjina tsantsar mugun halinsa, tasan yana sane ya batta ta kwana waje amma be isheshi na, sbda izayar da yake mata tana masa ddh yasashi kara sata knell down, abinda bata taba yiba a tsawon rayuwarta batamasan yadda akeyinsaba, rafka uban tagumi tayi hannu biyu biyu tana soshe soshen wuyanta daketa mata zafi, ga bayan kunnenta nata mata rad'ad'in azaba, bata tabbatar datazo dunia ba se yau, data d'and'ana izaya, ta kwana a wahe sanyi ya ratsata sauraye sukayi watandah da ita. ashe da a aljannarh dunia take rayuwa a gidan DANDI, bin jikinta ta shigayi da ido, tako ina yayi kuraje, ita batasanma meye yasa hknba, a dunia ma zata iya cewa batasan wata hallita ba sauro sbda bata taba cizonta ba, se yau, tunani ta shigayi ko meye sanadiyyar kurajen dasuka fito mata birjik din musamman a Hannayenta har wani kumburi sukayi, ga sanyin dare da asubahi datasha a wajen shi ya kara kmbura mata fuska duk jin jikinta takeyi ya mata danye danye ba dadih sam. Tana daga zaunen tana hawaye a hk ya turo kofar falon ya shigo byn dawowarsa daga masallacin, lokacin ana neman 6:am ne, idanuwansa ya zuba mata, yadda ya batta hk ya sameta wato ma ta rainashi bata aiwatar da abinda yasata ba, zucia tazo masa sama, hilwah na ganinsa jikinta ya hau rawa tayi kasa da knta inba hknba batasan ya zatayi ba, ita de tasan kneel down amma ta mnta yadda ma akeyinsa ynzu.... A matukar hasale AB'ILAL yace "Ba nace kiyi kneel down ba!!'' Yadda yayi mgnr seda ga gigita lissafin hilwah, hanjin cikinta suka hausina nan take bakinta ya bushe sbda firgice ta kara kasa da knta bayan ta zabura sbda firgicin mgnrsa, ido ya zuba mata dan ganin ko zata aiwatar da Abinda ya sata, Amma yaga ko motsi batayi ba zucia ta kara zuwar masa wuya, gadan gadan ya tinkarota zuciarsa na zugasa kan ya koya mata hnkli, be jira wata wataba ya daga hannun hagu ya sharara mara wani irin lafiyayyen mari a kan lallsusar fuskarta, zucia a harzuqe, wani irin zabura tayi ta firgice jin hannunsa a kn kuncinta, ta fasa ihu cikin fitar hayyaci nan da nan duk tabi ta firgice, tinda uwarta ta haifeta ba a taba kai hannu jikinta da sunan duka ba se yau, wani irin hawaye masu zafi suka shiga aikin sintiri a kn fuskarta... Daskarewa yayi a nan tsaye ya mareta a memakon yaji sanyi a ransa se kawai yaji wani iri a jikinsa sbda laushin fuskarta dayaji a hannunsa wanda ya maretan dashi, Ba karamin laushi ALLAH yyma fuskar tataba, marirrika yaso ya mata hadi da duka,ma amma abu ya gagara dole ya dakata daga marin dayan da yayi mata, ya yarfe hannunsa daya maretan dashi, ya zuba mata ido tana kuka kmr ranta ze fita, wani iri yakeji a ransa sbda sanadin kukanta dake shiga dodon kunnuwansa, ajiyar zucia ya sauke wadda besan dalilinta ba, ya bude baki ze daka mata tsawa ya kasa, kawai ya juya ya bar gurin ya nufa bedroom dinsa ba tare dayasan dalilin hknba, kawai de yasan can cikin zuciarsa bata masa ddh.... Ganin ya bar falon hilwah ta kara tsurewa ta fashe da kuka me tsuma zucia ita tunaninta ko yaje dauko abun duka ne ya daketa danta kula beda tausai, saurin yunkurawa tayi ta tashi da kyar, ta ruga da gudu tana cigaba da kukan ta nufa dakinta tana shiga ta maidashi ta rufe ta masa key luck jiki na rawa, ta karasa ta silale kasan dakin ta fashe da kuka hadda bubbuga kafafuwa a kasa tana fadin "Momy! Momy! Momy!'' Daganin yadda take kuka tana buga Kafafuwan a kasa tana kiran momy zaka fahimci akwai shagwaba a tattare da ita, kuka takeyi sosai kmr ranta ze fita, tinda uwarta ta haifeta bata tabayin kukan da takeyi ynzu ba, ta kai hannu ta shafi kumatunta taji ya kumbura saitin inda ya maretan, taji shadin yatsunsa sun kwanta radau sunyi jajawur kai kace zana yatsun nasa akayi a kn kuncinta, kuka takeyi sosai tana shushura kafafuwanta a kasa gaf jikinta ciwo yake mata ga radadin zafi yana mata, zamewa tayi ta kwanta a kasan dakin tana me kara ci gaba da kukan nata se faman shafar kuncinta takeyi inda ya maretan zuciarta na mata zafi da kuna ta rasa